← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 155

Sashe 88

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

   Ganin yanda Hajiya iya ke murna ya saka Khalipha samun waje ya zauna danta gama ta gumtsa masa. Tana kuwa ajiye wayar ta ɗaga hannu sama tana ambaton Alhmdllh.
    Katseta yayi da faɗin, “Niko Granny taƙaita addu'ar nan ki faɗamin minene?”.
     Hannu ta sauke tana masa daƙuwa. Sai kuma ta ƙara washe baki da gyara zama. “Burina ne ya cika Abdul-Mutallab ƙarami, ALLAH ya tabbatar da tarkon dana ɗana. Na kuma daɗe ina mafarki da addu'a. Bazan ɓoye makaba yau dama saboda Moddibo nasa aka bani Zinneerah. Dan nasan duk daren daɗewa zaizo ya ganta, ko yasota ko karya sota dama na tanadar masa itane. Sai kuma cikin hukuncin ALLAH ga wani sarƙi ya ɓilla a tsakani........ (tsaf ta kwashe masa labari ta bashi).
        Zuciyarsa ce ta shiga tsitstsinkewa, yay saurin yin ƙoƙarin dai-daita yanayin nasa yana haɗiye abinda ke neman toshe fitar numfashinsa. Cikin murmushi da ƴar dariyar yaƙe yace, “Kai kai kai Alhmdllh da wannan daddaɗar labari Granny. Wlhy wannan haɗi yayi kuwa, dan sun dace matuƙa, sannan hakan da baffa yayi shine maganin Aunty Farah da Mammah. Sai dai kuma abinda ya bani mamaki da al'ajabi wai little jinin Yayanmu ne. kainafa ya kulle”.
       “Nima nawan a kulle yake Khalipha, amma dai ni yanzu burina jin ta bakin Inno, tunda dai ai ba'a shan ciki a ruwa ko? Sannan kuma babu ta wata hanyar da mace zata samu ciki sai da namiji, dan haka dan ubansu zasuma faɗi yanda akayine su dukansu”.
        Ɗan jimm Khalipha yay yana wani nazari saboda maganar hajiya iya, yace, “Eh hakane Granny, amma dai yanzu akwai wasu hanyoyin da mace kan iya samun ciki koda babu alaƙar namiji a tsakaninsu”.
     Cikin sauri hajiya iya tace, “Kai Khalipha kaji tsoron ALLAH ta wace hanyace kuwa? Ni dai ban taɓa jiba gaskiya”.
     Murmushi Khalipha yayi, cike da rashin damuwa ko tunaninsa kaiwa nan ɗin da wata manufa yace, “Granny karki manta nifa Doctor ne. Doctor ɗinma dakeda alaƙa da matsaloli irin na mata. Akwai hanyoyi da dama kamar su yin dashen ciki da makamantansu”.
       “Kamarya dashen ciki?”.
Dariya yayi yana miƙewa. “Oh oh Granny wannan ai bayanine mai zaman kansa. Amma dai ki sani yanzu ana iya dasama mace ciki ta haihu wlhy”.
       Baki hajiya iya ta taɓe da faɗin, “Ah kudai da shegen ƙaƙale-ƙaƙalenku na likitoci dalilin yin karatu cikin masu jajayen kunnuwa ba. Mudai ko anayin wannan sheɗancin baije manaba kaji, danni wannan ai badan karna yanke hukunciba sai nace kamar wuce wuri ne”.
          “Tab Granny wlhy mutanenmu ma sunayi, duk da dai gaskiya turawa sukafiyi, amma yanzu kinga kamar a kudancin ƙasarmu sosai sukeyi, wasuma sana'a suka maidashi wlhy. A dasa musu cikin idan lokacin haihuwarsa yayi su haifa suba masu cikin ɗansu. ALLAH dai ya ƙyauta, dan wasu tsiraru a mutanenmu ma sun tsunduma wannan harkar sosai musamman ƴan gayun mata da basa son wahala, sai su bada a ɗaukar musu cikin idan ya isa haihuwa a haifa a basu abinsu. Wasuma a asibitin ake ajiye musu ba jikin kowaba. Idan ya isa haihuwa a ciresa a basu”.
       “Kai wannan masifa dami tai kama. A lallai wannan duniya tazo ƙarahe kuwa”.
     “Sosai ma” Khalipha ya faɗa yana ƙoƙarin ficewa dan bayaso halin da yake ciki yakai ga bayyana a fuskarsa har Hajiya iya ta fahimta.
      A falo ya wuce su Zinneerah dake kallo, yanda ya wuce ko kallonsu baiyiba yasa Jamal cewa, “Tofa, inaga Granny da Yah Khalipha anɗan dambacebe naga kamar ya wuce a fusace”.
       Dariya su Meenal sukayi. Zinneerah ko tayi kamar bata jiba dan tun ɗazun gabanta ke wani irin faduwa. zuciyarya na mata rauni kamar maijin tsoron faruwar wani abu a gareta. Sai dai ta daure bata sanarma kowaba tanata addu'a a zuciyarta. Dan kallonma yinsa kawai take ba fahimta takeba sam.

       Duk wannn abu dake faruwa Farah na ɗakinta cike da damuwa. Dan tunda taji AK ya tafi Nigeria zuciyarya bata samu nutsuwaba. Wannan dalilin ya sata kiran Aunty Zakiyya ta sanar mata, ta kuma turama Mammah text message. Aunty Zakiyya ce ta kira Mammah suka tattauna, duk da ba'a kano takeba Mammah ta bata damar sakawa a mata binciken zancen yaron.
      Daga haka ta kira baffa a gadarance tana tabbatar masa bai isa rabata da AK ba. Idan ma wani abu yake ƙullawa sunyi ta banza, dan ko aure suka saka AK yayi har aka samu wannan yaron ya tabbatar sai AK ya saki koma ƴar uban wacece. taji zafin maganganun da Baffah ya yaɓa mata, dan haka ta yanke shawarar Aunty Zakiyya na gama mata bincike zata tafi Nigeria ɗin da kanta, shiyyasa ta kira Farah ta kwantar mata da hankali da mata nasiha akan karta sake shiga harkar kowa a gidan harsu gama bincikensu.
     To wannan nasiha ta Mammah tasa Aunty Farah nutsuwa waje guda ita a dole ta kama kanta.😹. Suma dai su Hajiya iya daba sanin miya faru sukaiba babu wanda ya shiga harkar tata. Dan yanda bata nema ganin kowaba tun bayan tafiyar mijinta, suma sai basu nemetaba. Dan a matsayinta na matar gida ita keda haƙƙin bin yanda suka tashi ko sukaci suka sha a gidan. Amma bata taba yiba tayaya suma zasu takura kansu ne akan damuwa da al'amarinta. Gara su rike mutuncinsu ko za'a zauna lafiya.

      Su Zinneerah kam koda suka fahimci ɗunbin farin cikin da hajiya iya ke a ciki suka tambayeta catai babu komai. dan sunyi magana da Baffah akan zasubar zancen kar Zinneerah ta sani har sai sun dawo Nigeria saboda sheɗancin su Mammah. Baffah yace yana tsoron su sani subi ta wata hanyar su cutar da yarinyar mutane a ƙasar da batasan kantaba. Amma tunda nan da sati biyu zasu koma ayi haƙurin hakan kawai dan za'a haɗe bikinne da nasu Ni'ima. Hajiya iya kuwa ta gamsu da wannan shwarar ɗari bisa ɗari. Dan haka bayan Khalipha tai gum da bakinta...........✍

*_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.

*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu😭🙏🏻_*

*_TYPING📲_*

*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*

___________________

*Page 43*

...........A Nigeria kuwa yau cikin farin ciki AK yay barci rungume da Little, haka kawai wata nutsuwa da farin ciki suka mamayesa. Dukan wani ƙunci da damuwa da tunani akan samuwarsa suka kwaranye, farin ciki da nutsuwa suka maye gurbinsa, jiyake tamkar ya haɗiye abinsa ya ƙara haifosa tsabar yanda yakejin abun kamar almara. wai shine da ɗa da rana tsaka, ɗan da baisan ta yanda ya samar da shi ba, ɗan da baisan a ina ya samar dashi ba. Shi tsabar ma nazari akan waɗanan tambayoyi. har ji yake ƙwalwar kansa na kuɗa, shiyyasa ya tattare komai ya ajiye gefe ya rungumi ɗansa tare da sumbatar goshinsa yana murmushi.
      Ya jima barci bai ɗaukesaba yanata kallon little ɗin, sai can kusan ɗaya na dare barci yay awan gaba da shi. ALLAH ya soshi yaron baida fitina. Dan bai farkaba sai gabannin asuba ya tashi yana kiran “Mama ruwa, mama ruwa”.
    A hankali AK ya buɗe idanunsa, ya miƙa hannu ta bayansa ya kunna fitila dake a bedside drawer dan da alama basu da wuta. Zaune ya tashi da ƙyau yana riƙo little dake neman yin kuka yana kiran ruwa. “Oh oh sweetheart i'm sorry ina zuwa”. Ya faɗa da ɗagashi gaba ɗayansa ya maida jikinsa. Kafin ya ɗakko ruwan daya ajiye gefensu dan shima yakan tashi shan ruwan dare shiyyasa baya kwanciya babu shi a kusa. Sosai little yasha ruwan. Yana gamawa ya lafe a jikinsa ya koma barci. Shiru yay yana kallon fuskar yaron mai tsananin kama da tashi, wani lallausan murmushi da ajiyar zuciya suka kufce masa a lokaci ɗaya. Kwantar dashi yay a hankali yaja bargo ya rufa masa shi kuma ya sauka dan yasan bazai iya sake komawa barcinba kuma.
Chapter 88 · 0% Book details