← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 155

Sashe 93

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

      A ɗakin hajiya iya kuwa koda AK ya shiga tararwa yay su Baffah na magana. Baffah na zayyanema Hajiya iyan yanda sukai da Mammah. Gaishesu yayi, duk suka amsa masa da kulawa. ya yunƙura da nufin fitowa ya basu waje Hajiya iya ta dakatar dashi ranta a ɓace dajin abinda Mammah tazo tayi.
     Komawa yayi ya zauna kansa a ƙasa dan yaƙi yarda ya kalli kowansu,  bayason suga damuwar dake kwance a cikin idanunsa.
         Cikin kaushin murya Hajiya iya tace, “Ina maka murna da samun yarinyar ƙwarai kamar Zinneerah moddibo, itama kuma ina tayata murna da samunka matsayin miji. duk da har yanzu zuciyata ta gaza hasaso ko tunanin ta yanda kuka samar da Abdul-Mutallab. Amma a dalilin wani bayani da Khalipha yaymin yasani shiga wasuwasi, zuciyata kuma ta ƙara shiga ruɗani da bayanin mahaifinka akan abinda ya faru randa aka sanar maka yaron jininka ne. Sai dai hakan dakai ba shike nuna zan yarda dakai ɗari bisa ɗari ba Moddibo har saina san gaskiyar al'amarin nan. Amma zan cigaba da roƙon ALLAH ya bayyanamin gaskiyar kafin nabar duniya. Ada nayi tunanin barin tarewar Zinneerah harta kammala karatunta na sakandire. Yanzu kuma na canja shawara saboda dalilai masu yawa. Ciki kuwa harda gadaran da mahaifiyarka keson nuna mana akanka da ƴar uwarka, tunda dai ita na fahimci batasan kawaiciba. Kaje daga yau ka fara gyaran gidanka, ka kuma shirya haɗama Inno lefe dan nan da kwanaki goma zata tare”.
     Ba AK kawai ba hatta Baffah da Mommy sai da suka ɗago suka kalli Hajiya iya. Cinkin ɗan rawar baki Baffah yace, “Amma Inna karatunta fa?”.
      “Tayi a gidansa”.
Ta bama Baffah amsa kai tsaye babu alamar wasa ko sassauci a saman fuskarta. Ɗan ajiyar zuciya Baffah ya sauke duk da shima bawai yana nufin wani dogon zango Zinneerah zata kaiba. Dama dai tunaninsa bai wuce ta gama zana jarabawarta ta ssce da zasu fara kwanan nanba. Amma kuma tunda hajiya iya ta yanke hukunci shi hakan ya masa kodan ya sake tabbatarma Hindatu shine boss.
      Mommy ce tai ɗan murmushi tana kallon hajiya iyan, cikin kwantar da murya tace, “Innarmu baƙya ganin anyi gaggawa. Mu bashi damar shiryawa a tsanake sai a haɗa danasu Ni'ima tunda wata biyu ne kawai ya rage”.
        “Na riga na gama yanke hukunci Bilkisu, ba kuma zan canjaba saboda shine dai-dai. Anjima kaɗan za'a kaini gidan Hauwa'u itama”.
       Dole Baffah da Mommy suka amsa da to, AK kuwa uffan baice mataba. Dan shi yanzuma hankalinsa ba'a kansu yakeba. Tunanin wace magana? Khalipha ya sanarma Hajiya iyan yakeyi.
        Ganin yanda yayi ɗinne yasa hajiya iya kallonsa a ƙufule. “Saboda an manna maka abinda ka ɓata yasa kaimin shiru Abdul-Mutallab?”.
      Yanda ta faɗi real name nashi ya tabbatar masa da har zuciyarta ne. Dan haka ya ɗago ya kalleta, wani ɗan murmushi ya sakar mata yana miƙewa, “Indai nine kamar ki ɓata ranki, duk yanda kikeso haka za'ayi”.
    Daga haka ya nufi ƙofar fita abinsa.
Su duka da kallo suka bisa. Hajiya iya dake masa kallon harara tace, “Munafuki kama fito ka faɗa kowa ya sani”.
       Babu shiri dariya ta suɓucema Baffah da Mommy, dan yanda Granny tai maganar dolene ta baka dariya. Itako tai kicin-kicin da fuska kamar ba ita ta faɗa ba.

       Koda AK ya fita baiko kalli kowa a falonba ya fice, garden ya nufa kai tsaye, yana shiga ya ciro wayarsa a aljihu ya dannama Khalipha kira. Cikin sa'a kuwa ta shiga. Ring ɗaya ana biyu Khalipha ya ɗaga dan yaga sanda Yayan nasu ya fita daga falon kamar a fusace.
     “Ka sameni a garden”. Ya faɗa kawai yana yankewa.
     Miƙewa Khalipha yayi da sauri ya fice shima sauran yaran na binsa da kallo. Tun kafin ya ƙaraso cikin garden ɗin ya hango AK daketa safa da narwa hannayensa duka biyu goye a bayansa. Sai da ya iso daf da shi sannan yay sallama. Juyowa AK yayi ya zuba masa birkitattun idanunsa da suka gama tsorata Khaliphan a take. Duk yanda yaso daurewa sai ya kasa dole ya risinar da kansa ƙasa. Cikin harɗewar harshe yace, “Yayanmu gani”.
       “Na ganka ai”.
AK ya faɗa yana nufar kujera ya zauna. Fahimtar da Khalipha yayi yau a yaya yake ba besty ba sai ya nufesa shima ya zauna kusa da shi cikin rauni.
      “Yayanmu wani abu ya faru ne?”.
“Zai dai faru Khalipha”.
    Ƙara daurewa Khalipha yayi, dan shi duk tunaninsa ko Yayansu bayason auren Zinneerah ne, duk da yanajin zafin rasata bazai so Yayansu rabuwa da itaba dan sun dace. Duk da kuma yanada mata ya fisu buƙatar Zinneerah a yanzu.
         Cikin nuna damuwarsa a bayyane yace, “Yayanmu dan ALLAH miya faru? Wlhy tsoratani kake sakeyi”.
       Kamar AK bazai tankaba sai kuma ya gyara zamansa yana duban Khalipha ɗin da ƙyau. Zazzafar iska ya furzar idanunsa na sake rinewa. Kai tsaye yace, “Wace magana kukai da Granny?”.
      “Granny kuma? Ni?”.
Khalipha ya faɗa cikin jinjinawa da son tunanowa.
      Shiru AK yayi baice komaiba. Hakan ya bama Khalipha damar shiga kundin tunani na tsahon mintuna huɗu. Sai kuma ya duba AK yana ɗan jinjina kansa. “A sanina dai gaskiya babu wata magana da nayi da ita. In badai akan maganar IV......”.
     Sai kuma ya kasa ƙarasawa.
Da idanu AK yay masa alamar cigaba. Dole Khalipha ya ɗan haɗiye yawu yana maida kansa kasa. Maganar da suka tattauna da Hajiya iya akan hanyoyin iya samuwar ciki ya sanar masa. Har yakai aya AK baice komaiba, dan tun a fara bayanin ya raba hankalinsa biyu, ɗaya ga Khalipha ɗaya ga nazari da fashin baƙin dukkan kalma ɗaya dake fita a zancen Khalipha ɗin.
       “Amma kai miyasa kayi wannan hasashen?”. AK yay tambayar yana duban Khalipha cikin ido.
      “Ba hasashe nayiba Yayanmu, kawai dai yanda ita Granny tai maganar hanyoyin iya samuwar cikine sai ta dalili ɗaya yasa nai mata fashin baƙi akai cewar yanzu akwai wasu hanyoyi da suka ɓullo a likitance. Ni wlhy bamma ɗauka zata riƙi maganar serious ba sam”.
     Karan farko AK ya saki wani lallausan murmushi da ɗaura hannunsa akan kafaɗar Khalipha ya dan bubbuga tare da miƙewa. Daga haka baice komaiba ya nufi barin garden ɗin yabar Khalipha binsa da kallo.
     Sai da ya ɓacema ganinsa sannan ya sauke numfashi shima da ɗaura hannunsa akan kumatu yayi tagumi. A fili ya furta, ‘Anya kuwa nima ban cancanci yin nazari akan wannan batunba. Gashi dai na faɗama Granny ne kawai bada wani daliliba. Amma yanda Yayanmu yay serious a maganar da yanda ya dage akan shi bai aikata komai akan samuwar Abdul-Mutallab ba kamar akwai ruɗani’.
      ‘Tabbas akwai ruɗani’. Khalipha ya sake faɗa yana miƙewa zaram tamkar wanda aka tsikara. Domin shikam dai akwai abinda dama ya tsaya masa a rai game da cikin da akace aunty Farah na dashi ranar, shi likitane, likitan ma dayake karatu akan matsalolin mata. Amma sam baiga wani alamomin mai ciki tattare da Aunty Farah ɗinba. Anya kuwa Yayanmu da Aunty Farah babu wani abu da suke ayanzu yake ƙoƙarin bayyana kansa da kansa?...........✍

_Sannu-sannu bata hana zuwa, sai dai a daɗe ba'ajeba. Naga wasu sun ƙagara susan yanda aka samu little da zuwan Zinneerah aikatau, karku damu zaku sani, dan kowane al'amari da muhallinsa yake tafiya, idan kuma gaggawa ta shigo sai ya koma ba'akan tsarin dazai birgeba, wata ranama labarin zamu gama baki ɗaya insha ALLAH. Kudaiyi tattalin man kanku karya tsiyaye, al'amarin mai saukine😂. Ina gaisuwa irin trillions ɗin nan.☺️🤝🏻._

*_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.

*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

*_TYPING📲_*

*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*

_______________________

*Page 46*
Chapter 93 · 0% Book details