← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 155

Sashe 33

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

       Sun iso *_SHIRA HOSPITAL_*. Alhaji ya kira Buba ya fito ya shiga dasu har ɗakin da aka kwantar da Inno ɗin. Wajene na musamman a cikin asibitin da iyalan family ɗin Shira ne kawai keda hurumin shigarsa koyin jiyya a wajen idan hakan ta kama. Wajen tsitt yake sosai babu wata hayaniyar komai. Gashi a gare tsaf duk da kuwa sun tadda mutane kusan shidda tare da Inno ɗin.
     Ɗakin da take ɗakine babba da komai na kulawar marasa lafiya wanda ko ƙasar ka bari iya abinda zaka iya zuwa ka tarar kenan acan ɗinma.
       Inno ta tsufa sosai, sai dai ba irin tsufan nan da za'ace ta fita hayyacintaba. Dan tana gani ras tana kuma magana. Matsalarta kawai ciwon ƙafa dake damunta kasancewar ta mace mai jiki a da can. A yanzu hakanma bawai ramammiya baceba.
        Tunda sukai sallama a ɗakin kusan duk waɗanda ke a ciki suka zubo musu idanu suna mai amsa musu sallamar tasu. Tsohuwa mai ɗan yanayin kamanni da Inno, sai dai bata kaita tsufaba, sannan alamar jin daɗi fiye dana Inno ɗin ya bayyana a gareta ta tsaresu da idanu tamkar maison gano wani abu.
    Ganin duk sun tsargu da kallon da take musunne ya sata sakin murmushi da faɗin, “Wannan dai kamar Maryama idan idanun nawa na gani da ƙyau?”.
     Murmushi Gwaggo Maryama tayi a karo na farko, dan sai yanzune ta gane Hajiya Iya. Cike da girmamawa tace, “Nice Gwaggo. Tare da Yaya Hauwa da mijinta”.
           “Eh to naganki dai ke da na sani, sai kuma mijin nata zan masa na baƙunta, amma ita kam idona bai gantaba tunda itama nasan bason ganin nawa takeba kamar yanda bana tunanin tama sanni. Mutuniyar da aka sanarmin an bata adireshin inda nake a garin nan kusan shekara huɗu kenan amma bata nemeniba sai yau dalilin zuwan Inno, ai nikam banace nama santaba tunda dama canɗin ba sanin nata nayiba”.
        Sanin halin Hajiya Iya ya saka sauran mutanen ɗakin kowa yin murmushi harda Alhaji da Gwaggo Maryama. Maman Sadiq ma kanta a ƙasa take murmushin. Inda Hajiya Iya ke zaune kusa da Inno ta ƙara ta durƙusa akan gwiwoyinta tana faɗin, “A gafarceni Gwaggo. Nasan ni mai laifice amma dan ALLAH ina mai neman afuwarki”.
       “To zanɗan haƙura kaɗan idan mijinki ya sanarmin bashi da laifi wajen hanaki neman inda nake. Shi zuminci ai daɗine dashi koda na zaman anguwane balle ace na ɗan uwanka na jini. Uwa ɗaya uba ɗaya fa mahaifiyata suke da Inno, hasalima itace ta riƙe mahaifiyar tawa harta aurar da ita, dan itace ƴar zaman ɗakinta. Da hannunta ta raini mahaifiyarku har tsahon shekara huɗu kafin a aurar da ita. Amma ace yau ƴaƴan Hafsat na gudunmu saboda mahaifinku ya nisantamu daku a dalilin Hafsat bata raye a duniya”.
    Yanda ta ƙare maganar tana sharar hawaye ya saka ɗakin yin tsitt, itama Maman Sadiq sai hawayen suka shiga silalo mata saboda tinawa da mahifiyarsu da ALLAH yayma rasuwa tun suna yara.
      “Kiyi haƙuri Gwaggo munyi kuskure. amma insha ALLAH zamu gyara, na tabbatar miki zamu gyara”. Alhaji ya faɗa cike da girmamawa.
     Gyalenta tasa ta sake share hawayen nata, sai kuma ta kalli Alhajin tana murmushi. “Shike nan ɗana ALLAH ya tabbatar da hakan. Tunda harkun gane kunyi kuskure na haƙura. Amma dan ALLAH ku gyara dan shi zuminci babban abune mai girma da ta silarsama za'a iya zuwa aljanna. Mu daina biyema sharrin sheɗan dana zamani zukatanmu nayin nisa da juna. Ina daɗi ace ƴaƴan Hafsat basusan inda nakeba saboda iyayenmu basa raye. Wajen gwaggo kawai kuke zuwa”.
        “Tabbas ba'a ƙyautaba Gwaggo. Amma dan ALLAH ayi haƙuri. Kamar yanda ya faɗa insha ALLAH zamu gyara. Wlhy zuwanma da kikaga banyiba nima rasa takardar da aka rubutamin adireshin da lambar wayar nayi. ALLAH kuma bai ƙaddara duk sanda na shigo bauchi na sake amsar wani adireshin ba a wajen Buba”.
        Hannu Hajiya Iya tasa ta kamo na Mman sadiq mai maganar, sai kuma ta kamo na Gwaggo Maryama duk ta haɗa cikin nata tana murmushi. “Ya wuce insha ALLAH, nima namuku hakane danku ƙara sanin muhimmancin zuminci, mu kuma sake dunƙulewa tsintsiya naɗaurinki ɗaya. ALLAH yayi muku albarka kuda zuri'arku damu baki ɗaya”.
     Cikin jin daɗi su mmn Sadiq suka amsa mata. Daga haka aka koma gaishe-gaishe kamar ba yanzu Hajiya Iya ta gama sharar ƙwalla ba.
     Sai da aka gama gaishe-gaishe da tambayar jikin Inno daketa kallonsu kawai dan ko magana bata iyayi amma tana jinsu. Hajiya Iya ta koma nuna musu sauran jama'ar ɗakin.
       “To ga ƴan uwanku nan nasan duk baku sansuba. Waɗan nan biyun matan yayanku ne. Waɗan nan kuma ƴaƴanku ne dukansu gasu nan. Badai zaku gane lissafinba anan sai munje gida”.
       Su mmn Sadiq dai murmushi sukeyi cike dajin ƙaunar ƴar tsohuwar, suka sake gaisawa da waɗanda ta nuna musun. Yanda suma babu alamun wulaƙanci a garesu yasaka jin farin ciki a zukatansu Mmn sadiq ɗin.
    Hajiya Iya ta nuna su mmn sadiq kuma garesu suma tana faɗin, “Ku kuma waɗannan ƙannenku za'ace kenan ko. Dan ƴaƴan Yaya Hafsat ne da ALLAH yayma rasuwa babbar ƴar Gwaggo da aure ya kai can Katsina, nasan dai bazaku gaza jin sunantaba a hirata ma. mahaifinsu ne bai barsu sakewa a cikinmuba tun suna kananu shiyyasa baku sansuba basu sankuba kuma. Amma insha ALLAH daga yau kowama zai sansu ɗin”.
     Duk suma amsa mata sukai da girmamawa dan babu mai jayayya da ita a kaf family ɗin harsu matan ƴaƴan nata. Sallama Alhaji yay musu ya tafi saboda ganin lokaci zai ƙure masa na kasuwa. ya wuce akan zai dawo anjima ya ɗaukesu idan ya taso.
Chapter 33 · 0% Book details