← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 155

Sashe 6

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

      “Zinni!! Zinni!!. Wai dan buhun ubanki baki jina inata kware baki?”.
     A firgice ta tashi zaune jin irin kiran da Inna ke ƙwalla mata tamkar ana yaƙi. Ta amsa a kasalance tana ƙoƙari janye kayan data nausama kanta gefe dan ta samu damar mikewa.
       Fitowar tata yay dai-dai da shigowar Yaya Gajeje gidan da sallama. Inna ta sake tsuke fuska tana kallonta. sai kuma ta ɗauke kai ta maida ga Zinneerah dake fitowa tana rawar sanyi da yamutse fuska alamar bata da lafiya.
      “Oh sannu ƴar gata! Ina nan tsaye ke kina can kina jan nashari a ɗaki? To kizo ki haɗa mani wutar ɗan wake kar rana tayi..”
      Da sauri Yaya Gajeje tai saurin tare numfashin Inna, “Haba Inna, wane haɗa wutar ɗanwake kuma kike magana haka? Diba kiga yanda take rawar ɗari da alama bata da lahiya”.
       “Mtsoww!!” Inna taja tsaki. Kafin ta cigaba da magana a hasale. “To ina ruwana da ciwon nata. A yanzu ma wagga duniya waye ke da lahiyar. Gajeje ki hita idanuna, karki kaini maƙurar randa zan maki bankaɗa wallahi”.
      Murmushi Gajeje tai tana kaiwa zaune. Cikin kwantar da murya tace, “To inna idanma kin mani bankaɗa ai kin isane tunda kece kika haiheni. Ni dai kin sanni ban ganin gaskiya na riheta ai. Amma dai kiyi haƙuri ni bara na haɗa miki wutar tunda ita batajin daɗi. Harma sakin danwaken yau nice zan miki Innarmu kwantar da hankalinki”.
    Baki taɗan taɓe. sai dai batace komaiba. Hakan yasa Gajeje fahimtar taci nasara. Tai murmushi da tura hannu a zaninta ta ciro leda dake a lalitarta ta bujen ciki. Goro ne da alawa da biscuits guda biyu ƴan goma-goma. “Innarmu ga kayan suna”. Tai maganar tana miƙa mata.
      Ɗan sakin fuskarta tayi da miƙa hannu ta amsa. “Yo kuma ƙya bani duka. Su su Rabi'u fa?”.
      “Karki damu na ba Salame ta kai musu nasu suma. Wannan nakine. Nima Agali ya bani shi bayan mun hito”.
      “To, to maddala. Ni bamma sami leƙawaba yau na tashi da ƴar mashashshara ne. Sai zuwa anjima zanje nai masu an raɗa suna. Miye sunan ɗiyar ne?”.
       “Ai Hadiza aka samu, sunan Innar Bilkin aka saka”.
     “Tofa ɗigifi. Shi yanzu duk yawan gidansu ya rasa wazai saka sai sunan uwar matarsa?”.
      Ƴar dariya Gajeje tayi tana yafito Zinneerah dake tsaye rakuɓe jikin bango da hannu. “Inna kenan, ashe babu daɗi Lawal ya sakama Ummita sunanki shima”.
     Shiru tai bata tankaba. Dan an ƙure tsoguminta kenan.
    Zinneerah ta zauna tana gaida Gajeje. Cike da kulawa ta amsa mata da kai hannu a jikinta. Jin uban zafin ya sata ambaton, “Ya subahana. Zinni ai masassara ce a jikinki sosai. Kin karya dai ko?”.
      Ƙasa Zinneerah tai da kanta tana haɗiye hawayen dake neman zubo mata. Dan harga ALLAH yunwarma tanajinta mai tsananima kuwa. Saboda Inna batai mata tayin abinciba yasa ta haƙura.
     Shirunta yasa Yaya Gajeje fahimtar bataciba ɗin. Tasan za'a rina. Dan innarsu lamarinta sai du'ai. Bata sake cewa komaiba kamar yanda itama Innar bata tanka musu ba. ta dai miƙe zuwa gindin murhun inda tukunya ke aje saman duwatsun murhun. Tuwone a ciki na dawa da aka yanka aka ɗumama. Duk ma ya zama gutsatstsari alamar masu gidan sunci. Yaya Gajeje da ranta ke mata ƙuna ta ɗauka kwano ta zubama Zinneerah, tare da koriyar miyar kukar dake gefe. Har gabanta takai ta dire tana fadin, “Maza ci na samu mai sayo miki magani nan gidan Rahine idan bata fita tallar kayan koli ba”.
      Jan kwanon Zinneerah tayi gabanta, babu musu ta hau ci dan yunwa takeji sosai..
     Inna dai bata sake tankawaba har Zinneerah ta gama cin tuwon nan. Yayinda Yaya Gajeje ta koma can wajen murhu tana haɗama Inna wutar ɗanwake da ƙoƙarin saka ƙatuwar tukunyar da take amfani da shi.     

            Kasancewar Yaya Gajeje a gidan yau sai ta samu ƴar salama. Dan har Baba daya shigo shima ya ɗan samu sakewar bata kulawa, harda siya mata awara.
     Washe gari kam Inna bata saurareta ba. Duk da ta fahimci har yanzun bata da lafiya, dan ba'a ƙulla awa biyu Zinneerah bata raɓe gefe tana riƙe cika ba alamar dai cikin na mata ciwo.
      Sai dai tsabar rashin tausayi ko'a fuska Inna bata nuna ta fahimtaba, daga ƙarshema tallar riɗi da gyaɗa ta sakata ɗauka. Da Sa'a tayi magana kuwa ta hayayyaƙo mata da masifa kamar zata daketa. Dole tai shiru tana maijin babu daɗi da halin mahaifiyar tasu.

★★★

            Yau satin Zinneerah ɗaya kenan da dawowa da ga Katsina. Tun Inna na zuba idon ganin Hajji Lanti ta biyo bayan Zinneerah harta fara sarewa. Dan har ranta ta ɗauki alwashin sai Zinneerah ta koma, bazata taɓa yarda kuɗin data ƙwallafa ran samu su wuceta a banza ba.
       A ɓangaren Zinneerah kam a kwanakin nan daka kalleta kasan bata da lafiya. Musamman yanda ta wani rame sosai. Gashi sam bata da kuzari a jikinta. Yanda ta saba aiki ada da kazar-kazar yanzu sam bata iya hakan. Komai zakaga tana yinsane da sanyin jiki kamar mara ƙashi. Inna tayi masifar harta gaji ta barta, sai dai zagi da tsina ne tana shansa, dan ranar har marinta tayi.
       Yau ma kamar kullum tana gama ɗibar ruwa da dukkan aikinta na gidan tai shirin ɗaukar tallar riɗi da gyaɗa. Tinene kaɗai ta samu a tsakar gida tana suyar wainar fulawa. Inna kuwa ta fice barka wai.
      Ɗakin Inna ta shiga ta ɗakko ƙaton farin botikin da aka cika da gyaɗa da riɗi, ta sake fitowa tsakar gidan. Cike da sanyin murya tace, “Tinene idan Inna ta dawo ki hiɗi mata na wuce”.
      Kallon banza Tinene tai mata ta ɗauke kanta. Cike da rashin mutunci tace, “Inma wannan allagiran kike mawa kima cire rai yarinya, dan aradu baki cin ko ranyo anan”.
     Murmushi Zinneerah tayi kawai ta fice, dan tasan inhar ta biyema Tinene zama su iya faɗa, itako bata da wannan ƙarfin yanzu kam.
         Dai-dai fitowarta ƙofar gidan nasu gabanta ya faɗi. Tai ƙasa da kanta saboda cin karo da fiska mafi daraja a zuciyarta bayan ta iyayenta. Ba kowa bane face saurayinta Babawo wanda a yanzu ya maida akalar neman auren nasa kan yayarta Karima da yaya Sa'a ke bimawa. Babawo ya sota tun bata san kantaba. Da farko matsin rayuwar data tsinci kanta a hannun Inna dalilin rashin mahaifiyarta a gidansu Babawo yake tausaya mata. Shine silar cigaba da karatunta bayan gama firamare , shine ya tsaya tsayin daka harta shiga makarantar gaba da firamare (Secondary), tana aji ɗaya wani kawunsa ya zo ya tafi da shi kaduna. Bai dawo ba sai da ya shekara. Kamar yanda ta ɗokantu da zuwansa haka shima ya ɗokantu da ganinta. Yazo mata da tarin tsaraba, tare da burin iyaye su shiga akan maganar aurensu, a cewarsa data kammala aji uku na sakandire zasuyi aure. zai wuce da ita can kaduna sai ta cigaba a gidansa har sai taga ƙarshen biro. Hakan yama Zinneerah daɗi a zuciya da ruhi, sai dai kuma a kwana biyu da zuwan Babawo labarin ya canja alƙibla. Dan kuwa bai komaba sai da tsuntsun soyayyarsa ya tashi daga kanta ya koma kan yayarta Karima yar wajen Inna ta uku. Ƙiri-ƙiri ta gaza gane kan Babawon ta, ya canja mata gaba ɗaya. Kosan ganinta bayayi. Taci kuka sosai, ta kuma shiga ruɗani, dan har ciwo tayi. Mutane sunta kace nace akan wannan al'amari, wasu na faɗin asiri Inna taima Babawo ɗin, wasu suce kuma shine dai yake ganin Karima ta fiye masa tunda ita babbar budurwace wadda akema surutu akan rashin samun miji. Dan Karima shekararta sha takwas da wasu watanni, a ƙauyen kuma sa'annin su Zinneerah sune dai-dai aure ƴan sha biyu. Amma sai dai ita ƴaƴan Inna dama sukanyi jinkirin samun miji a ƙauyen saboda mugun halinta, shiyyasa ma har yau babu wacce ta taɓa aure a nan cikin Danya. Gajeje na kauyen Sanni, Atine na can Rimaye. Sai yanzu ga Karima da Sa'a waɗanda duk sun zama manyan ƴammata. Karima nada sha takwas Sa'a na sha shida. Sai Tinene sa'ar Zinneerah itace auta.
         Bayan wucewar ruɗanin canjawar Babawo da shekara ɗaya da wasu wattani, dan har manya sun shiga maganarsa da Karima sai kuma Inna ta haɗata da hajji Lanti da tai sanadin kaita birnin Katsina da niyyar aikatau, inda ita kuma ta gudo ta dawo gida........
         “K! Wai baƙyaji ana miki magana”.
   Tsawar da Babawo ya daka matace ta dawo da ita daga dogon tunanin da ta tafi batare data farga ba. Saurin haɗiye hawayen da suke neman zubo mata tayi tana girgiza masa kanta.
         Ta ɗan risina kaɗan tana faɗin, “Kayi haƙuri Ya Babawo banji bane wlhy”.
      Tsaki yaja yana taɓe baki da jifanta da wani irin mummunan kallo na tsana, wanda a da idan wani yay kuskuren yimata irin wannan kallon sai inda ƙarfinsa ya ƙare. A gadarance yace, “Kiramin Karima nace”.
        Idonta ƙasa-ƙasa tana mai satar kallon yanda ya ƙara ƙyau da cikar zati tace, “Yaya Kareema bata nan, tana Rimaye wajen Yaya Atine, nima ban dawo na sameta ba”.
       Tsaki yaja yay gaba batare da ya sake tanka mataba. Ta bisa da kallo cike da tsananin so da ƙaunar da take masa har yanzun. yayinda ƙamshinsa daya bar mata take jinsa mafi daraja da tsada a cikin iskar da take shaƙa. Duk da ƙarancin shekarunta zuwa yanzu tasan minene soyayya, dan shine ya rene ta akan bigirenta, tun bata fahimta harta fara ganewa da banbancewa, sai gashi rana tsaka rabuwa tazo musu bisa tafarkin MAKAUNIYAR ƘADDARAR da batasan sila ko mafarinta ba, tunda har yanzu bazata iya faɗin dalilin rabuwar tasuba balle dalilin komawar Babawonta kan yayarta.
     Hannu tasa ta sharce hawayenta tana gyara riƙon botikin gyaɗa da riɗinta ta cigaba da tafiya ranta na mata zafi da ƙuna.............✍

*_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.

*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Chapter 6 · 0% Book details