← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 155

Sashe 20

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

          A asibiti kam shiru-shiru Khalipha bai dawoba har lokacin yin barcin ranar Zinneerah yayi tasha magani ta kwanta. Bata tashiq farkawaba sai bayan sallar la'asar. Ganin lokaci yaja ya sata miƙewa aɗan harzance ta shiga toilet ɗin dake a ɗakin. Alwala tayo ta fito, bayan idar da sallar ne Salima ta shigo dan bata abinci kamar yanda Khalipha ya rataya mata alhakin yin hakan ga Zinneerah. Itako bala'in son da takema Khalipha yasa bata iya ƙetare buƙatarsa a rayuwarta, shiyyasa take bama Zinneerah kulawa sosai dan duk zatonta yanada alaƙa da zinneerah ɗinne musamman dataga an kawo zinneerah ɗin ɗaki na musamman ita kaɗai an ajiye.
        Zinneerah na tsaka dacin abincinne Salima na mata hira tana ɗan murmushi sukaji sallamar Khalipha bayan yayi ɗan knocking. Saurin jan hijjab Zinneerah tai ta saka, Salima ma ta gyara zamanta dana ƙaramin hijjab ɗinta tana amsawa.
       Shine ya fara shigowa ɗakin tamkar ɗazun, sai Naziru biye da shi, wani da suke tsananin kama da Nazirun na bayansu, sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci ya girmi Nasiru ɗin dan ba yaro bane.
       Sai matan ɗazun biye da su a baya, amma banda matar Naziru. Matar ɗazun da taji suna kira da Maman Sadiq ta ƙaraso gaban gadon sosai batare da tama saniba. Hannu takai bisa kumatun Zinneerah jikinta na wata irin tsuma da karkarwa. Ko shekara dubu tai bataga wannan halittarba tayi imani da ALLAH randa suka haɗu saita gane abarta. Tunda tabar ƙauyen Danya cikin gushewar hankali dana tunani har zuwa yau ɗinnan bata daina kwana da mafarkintaba da tashi da tunaninta kuma. Ta kai ƙasa durƙushe hawaye na silalo mata a kumatu. Tabar ƴarta da ƙarancin shekaru hannun kishiya mai ƙarancin imani dana tausayi badan ranta yasoba, sai dan anfi ƙarfinta kawai. Yau kuma sai gata a inda bata taɓa zatoba ko tsammani a shekarun girma....
       “Zinneerah!”.
Ta ambata da wani irin rawar murya dana harshe.
     Ganin Zinneerah ta kasa magana sai kallonta kawai da takeyine kamar ɗazun ya saka Naziru faɗin, “Maman Sadiq ki kwantar da hankalinki, insha ALLAHU itace ma”.
         Idanunta da hawaye ke kwarara ta ɗago ta kallesa, taɗan saki murmushin ƙafin hali tana miƙewa tsaye sosai. “Nasiru indai har yanzu ba ƙwaƙwalwata ce bata gama dai-daitaba to wannan kam Zinneerah ce, dan naji hakan a jikina duk da kuwa bata amsa sunan dana kirata da shi ba”.
        Maman Halima da sukazo tare yanzunma ta matso gaban gadon itama ta zauna kusa da Zinneerah da alamu suka nuna tamkar bata a cikin hayyacinta. Sai da ta riƙe mata hannune tai firgigit alamun ta dawo cikin hayyacinta. Ƙasa tai da kanta saboda wani irin bugu da ƙirjinta ke mata ainun, Maman Halima ta katse shirun ɗakin da faɗin, “Ƴammata minene sunanki?”.
     Babu wanda yay tsammanin zata amsa. Sai ji sukai a bazata tace, “Zinneerah”.
      Wata irin nannauyar ajiyar zuciya maman Sadiq ta sauke, yayinda ɗunbin mamaki ya kashe Khalipha da  Naziru, musamman da suka tuna randa sukaita ƙwaƙwar jin sunan nata amma tai musu shiru..
     “Masha ALLAH Zinneerah daga ina kike? Ina nufin a wane anguwa iyayenki suke?”.
     Shiru kamar bazata amsa ba yanzu. Sai kuma zuwa can tace, “Ba'anan nake ba”.
        Cike da zumuɗi maman Sadiq tace, “Daga wane gari kike?”.
      Ɗagowa tai tana kallonta na tsawon kusan mintuna biyu, sai kuma ta maida kanta ƙasa tana sauke ajiyar zuciya. Cikin suɓutar bakin da bata shiryaba tace, “Danya”.
      Gani kawai sukai maman sadiq ta zube kan kujerar roban dake a gaban gadon ta fashe da kuka tana faɗin, “Wlhy itace, Zinneerah tace”.
     A yanda tai maganarne ya sakasu jin wani irin tausayinta ya ɗarsu a rayukansu, cike da son jin ƙarin bayani Naziru yace, “Zinneerah kekam miya kawoki hanyar jigawa keda ke a jihar katsina?”.
       Hawayen dake sakko mata ta share tana girgiza kanta. “Nima ban saniba, na samu kaina ne kawai a haka”.
         Sai yanzu ne Alhaji yay magana. “Lallai da alama kamar bata cikin hayyacintane ta baro gida fa kenan”.
      “Tabbas hakane Alhaji, kenan har yanzu Asabe bata canjaba ko kuma Zinneerah ma tayi gamo da abokiyar zama irin Asabe a gidan aure.” Maman Halima ta faɗa saboda ganin ciki a jikin Zinneerah duk da kuwa ta saka hijjab.
      A karon farko shima Khalipha da tun ɗazun baice komaiba sai kallonsu ya sauke numfashi. Gyara tsaiwarsa yayi a jikin bangon daya jingina yana kallon Zinneerah da keta satar kallon maman Sadiq da suke tsananin kamanni. janye idanunsa yay ya maida ga Naziru yana faɗin, “Inaga tunda har an fahimci bakin zaren ayi haƙuri haka har zuwa lokacin da za'a sallameta daga nan ɗin insha ALLAH. Sai dai ya kamata ku sanar mata wacece ita a gareta dan na kula ba fahimtarku takeba kamar”.
     Sosai duk suka gamsu da bayaninsa, suka zazzauna aka shiga gaisuwa da tambayar jikin Zinneerah ɗin, wanda Khalipha ya ƙara musu bayani game da matsalar dake tare da ita akan buƙatar hutu bisa ga lalurar cikin jikinta. Sun shiga mata addu'ar fatan sauka lafiya.
      Maman Halima dai ce da har yanzu ke zaune a kusa da ita tana riƙe da hannunta ta nuna mata wadda aka kira maman Sadiq. “Zinneerah wannan ɗin mahaifiyarki ce, duk da nasan baki santaba kamanin dake a tsakaninku da duk bayan da mukeyi a wajennan zai tabbatar miki hakan, kai namasan zakiji a jikinki koda ba'a faɗaba dan mahaifiya tafi gaban wasa ai.”
         Kafeta da kallo kawai Zinneerah tayi tamkar wadda ta suma a zaune. Sai da Maman Halima ɗin taɗan taɓatane ta kawo numfashi, sai kuma ga hawaye sharr. Batare datace komaiba tai ƙasa da kanta, daga haka bata sake ɗagowa ta kalli kowa a cikinsuba.
     Sosai hakan da Zinneerah tayi ya taba zuciyar Maman Sadiq. Dan ta fahimci kamar Zinneerah ɗin fushi take da itane kokuma kalar nata murnar kenan oho. Kowa ma dake wajen da irin fahimtar da yayma shirun na Zinneerah. Murmushi Alhaji yayi, cike da sanin yakamata da hangen nesa irin na manya yace, “Kubata lokaci kamar yanda likitan nata ya faɗa ko”. Sai kuma ya juya ga Khalipha batare da ya jira amsarsuba. “Likita yaushene zaku sallameta?”.
       Murmushi Khalipha yayi yanaɗan sosa gefen goshinsa. “Alhaji banine likitanba dai, amma insha ALLAH zuwa nan da kwana biyar haka akoda yaushe za'a iya bata sallama tunda jikin nata yana ƙyau, dama matsalar kamar daga cikin jikintane yasa aka riƙeta”.
      “To masha ALLAH, ALLAH ya kaimu, ya kuma bata lafiya”.
    A tare suka amsa da amin. Daga haka sukai musu sallama domin tafiya badan Maman Sadiq tasoba. Sai dai taji daɗin abinda Maman Halima ta faɗa akan cewar itace zata dawo ta cigaba da jinyar Zinneerah ɗin har a sallameta. Kowama yaji daɗin hakan har Khalipha.     

★★★

       Tun daga wannan ranar jiyyar Zinneerah ya dawo hannun Maman Halima, Khalipha ma bai janye daga mata hidimaba, hakama Naziru, ga Alhaji ma ya ƙaru. Sai ga Zinneerah ta sake zama ƴar gata, sai dai abinda kebama kowa mamaki har yanzu taƙi barin damar da zasu fahimceta game da komanta. Hatta haɗuwarta da mahaifiyarta sun kasa gane mike a ranta. Dan taƙi cewa komai, ta kumaƙi nuna murnarta a fili ko damuwarta. A duk yanda Maman Halima ke janta a jiki dan son jin wani abu gameda rayuwarta da Inna taƙi sakin jiki da ita, duk da kuwa ta fahimci babu wata mummunar manufa ga Maman Halima ɗin. Sanin yakamatane kawai irin na matar.
      Tun daga ranar Maman Sadiq bata sake zuwa asibitinba, sai dai ranta fal yake da damuwar yanayin Zinneerah a kanta. Tadai danne ne kamar yanda mijin nasu ya bata shawara akan ai haƙuri da komai har Zinneerah ɗin ta dawo gida.

        Itakam Zinneerah bawai farin cikine batai da ganin Mahaifiyartaba. Har ranta ita kaɗai tasan daɗi da take a ciki, sai dai wani ɓangare na zuciyarta ya sakata jin ciwo da zargin mahaifiyar tata ta watsar da itane akan sani kenan. Dan duk wanda zai kalli Maman Sadiq ɗin yasan tana a cikin kwanciyar hankali a gidan aurenta na yanzu.
       A ganinta idan ba tana saneba yaya za'ai ta watsar da ita tsahon shekaru batare data taɓa waiwayar inda take ba, hakama danginta. Wannan dalilinne ya saka yin kamar batai farin cikiba. Sai dai a randa abin ya faru tasha kuka a ɓoye, still rashin ganin kuma Maman Sadiq bata sake zuwa asibitinba ma ya ƙara taɓa mata zuciya.
Chapter 20 · 0% Book details