← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 155

Sashe 82

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

       Bayan wasu taƙaitattun awoyi aka samu nasarar farkawar AK da tun ɗazun ya farfaɗo daga sumar da yayi. A hankali ya buɗe rinannun idanunsa ya saukesu akan Baffah dake zaune riƙe da hannunsa. Sai Abba dake ta wajen ƙafafunsa shima a zaune. Mmn sadiq kam ta wuce gida tuni tare da little dan taje ta huta itama gudun kar taje ƙasa. Dan kallo ɗaya zakai mata ga gano tsananin tashin hankali da ruɗaninta.
       Kallonsu yayi ya maida idanun ya lumshe a hankali yana wani irin murmushi da baida maraba da kukan ƙunar zuciya. Idanunsa a lumshe yace, “Baffah nasan ba lallai ku yarda daniba akan bansan yaya akai na samar da Abdul-Mutallab ba. Domin ni kaina na kasa yarda da kaina balle ku da zan faɗamawa. Sai dai ku sani lallai ina cikin *_MAKAUNIYAR ƘADDARA_* babu wani haske da zai haska min idanun ganinta kuma sai UBANGIJINA da haƙurin fahimtata da zakuyi na ɗan wanu lokaci dazanyi ƙoƙarin ganin bakin zaren, b.........”
     Saurin katsesa Abba yay ta hanyar faɗin, “Ya isa Adnan. A yanzu halin da kake ciki baya buƙatar duk waɗanan maganganun. Dan Mahmud ya tabbatar mana da jininka yayi ƙololuwar hawa sama. idan kuma ka matsa da yawa za'a iya samun matsala. Mu dukanmu nan musulmai ne, muna kuma iya fahimtar yaran ƙaddara ko jarabawa, suk da dai ita wannan tazo mana a makance. Dan kai da Zinneerah ne ya kamata muji amsar tambayoyinmu a gareku, sai kuma gashi kuma neman amsoshin kukeyi a karan kanku. A ganina mafita ɗaya ce da shawara ta rage mana Alhaji”. Ya faɗa yana duban Baffah.
     Kai tsaye Baffah yace, “Karka damu Alhaji Abubakar, kai maganarka kai tsaye dan kaima ubane mai cikakken iko akan su Adnan da wannan matsalar tasu da ni ta sakani a babban ɗakin duhu bama na makanta kawai ba”.
    Murmushi Abba yayi, cikin son tausasa fushin Baffah da yake hangowa yace, “Nagode Alhaji Kabeer, abinda nakeson faɗa kai tsaye shine, mu koma ainahin ƙauyen Danya ko zamu samo bakin zaran inda matsalar take, dan a binciken da nayi wancan karan bazai gamsar damu ba saboda rashin samun mahaifin Zinneerah da nayi, sannan ƴan uwansa duk sunƙi bani haɗin kai akan wani dalilinsu da ban saniba. To amma sai nake dangantashi da fushi, sai dai ina fata da tsamanin insha ALLAHU zuwa yanzun sun huce. Maybe mu samu wani bakin zare da zaisa shima Adnan ya fahimci daga inda matsalar take ko zai tunano wani abu tunda dai babu wata hanyar samuwar ɗa sai da nasaba mai ƙarfi. Amma yaya kuka gani, dan yanzu ni wannan hasashena ne kawai”.
       “Maganarka nakan hanya Alhaji Abubakar, kumani wlhy na gamsu da ita ɗari bisa ɗari”. Baffah ya faɗa yana miƙewa tsaye.
       Zaune AK ya tashi da ƙyar, cikin son danne damuwarsa yace, “Uncle wannan shawaran naka yayi dai-dai, nima na gamsu da ita. Sai dai dan ALLAH ku gafarceni idan na ɓata ranku”.
      Da sauri Abba ya girgiza kansa. “Ka kwantar da hankalinka Adnan kaji, ALLAH zai warware mana komai cikin sauƙi”.
    Kai kawai AK ya ɗaga masa, dan yasan Baffah a ƙullace yake da shi. Duk yanda Dr Mahmud yaso riƙesa a asibitin yaƙi yarda, dole ya barsa suka tafi gida shi da Baffah Abba ma ya nufi nasa gidan. Bin bayansu Dr Mahmud yayi da drip da magunguna dan yasan AK na buƙatar hutawa na wasu awoyi ko hankalinsa zai dawo jikinsa.
         Tunda suka taho ko sau ɗaya Baffah bai yarda sunyi maganaba. Shima bai iya cewa dashi komaiba saboda ciwon kai dake damunsa har yanzun.
      Da suka shigo gidanma baffah cayay AK yaje shi yana buƙatar hutu. Ganin Dr Mahmud biye dasu yasa baiyi musu ba ya nufi sashen Hajiya iya shima. Acan Dr Mahmud ya samesa. duk yanda yaso ƙin yarda ya saka masa drip ɗin haka Dr Mahmud ya dage sai da ya saka masa tare da allurar barci mai ƙarfi. Aiko cikin amincin ALLAH sai gashi a ƙanƙanin lokaci barcin yay awan gaba dashi.............✍

*_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.

*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*

*_TYPING📲_*

*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*

________________________

*Page 40*

...........Da farko Baffah yaso kira ya sanarma Hajiya iya komai, sai dai a bisa wani tunaninsa kuma sai yace bara ya bari har zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu da yake da burin yanke hukuncin daya dace ya kuma san Hajiya iya zataji daɗi sosai. Bai sanarma kowa mike faruwaba a cikin matan nasa, ya dai nema ƙanwarsa Bilkisu a waya sunyi magana, anan nema take sanar masa itama gobe idan ALLAH ya kaimu takeson sake zuwa london ɗin domin duba jikin hajiya iya, tanata neman wayar AK ma bata samuba ashe ya shigo 9ja ne. Tace amma tunda wannan ta taso bara ta dakata harsu dawo daga danya, dan dama tanason su tattauna akan ɓoyema Ahmad rashin lafiyar Hajiya iyan da sukayi.
      Cike da so da ƙaunar ƴar uwarsa Baffah yace, “Babu damuwa Bilkisu, kiyi haƙuri na kashe wannan ƙurar duk da nasan tawuce kasuwar gobe, dan yanda Adnan ya dage cewar bai aikata wani abu akan samuwar yaron nanba hankalina na tashi, inaji a raina kuma kamar akwai wani abu ɓoyayye da bamu saniba”.
     “Gaskiya kam Yaya al'amarin yana buƙatar bincike, baka shaidar ɗan yau amma koni dai inaji a raina Adnan bazai aikataba, to amma jin cewar gwajin DNA ya tabbatar da ɗan nasane yasaka jikina duk yayi sanyi gaskiya. Amma inaga zan shigo zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu nan ɗin kawai”.
      “To ALLAH ya kaimu da rai, kizo ɗin kozanji sanyi a raina na samu abokin shawara nima”.
   Daga haka sukai sallama. Idan barci ya figi baffa a wannan dare sai dai ɓarawo. Hakama mmn Sadiq acan barci ya gagareta. Danma Abba nata mata nasiha da lallashi harya samu taɗan saki jikinta saboda kar matan gidan su fahimci akwai matsala.

*WASHE GARI*.

      Washe gari Alhmdllh AK ya tashi garau a zahiri. a cikin zuciyarsa kuwa shi kaɗai yasan mi yakeji gameda son tunano ko ya taɓa aikata wani abu makamancin wanda yake tuhumar kansa akan samuwar little. Sam bai iya tuna komaiba balle ya gano, dan haka ya ajiye komai a ransa yay shiri kamar yanda baffa yace.
      Yayi ƙyau matuƙa cikin ɗanyar shadda fara tas da taji ɗinki mai ƙyatarwa da ɗaukar hankalin mai kallo, ya murza hula a kansa wadda ta sake ƙawata tsarin adon nasa da bayyanarsa cikakken bahaushe. Turare ya saka ya fito yana baza ƙamshinsa mai sanyi da daɗin shaƙa. Yayi mamakin cin karo da matasan ƙannensa suma cikin shiri, sai dai baice komaiba ya shiga amsa gaisuwar da suke masa cikin girmamawa.
      Baffa ne ƙarshen fitowa sanye shima cikin tashi ɗanyar shaddar, fuskarsa a sake tamkar babu damuwar komai tattare da shi, har hakanma ya bama AK mamaki da tsoro, dan tun yana yaronsa ya gama karantar irin wannan yanayin na Baffa. Idan kai masa laifi ya nuna kamar bai damuba to lallai akwai abinda yake shirya maka kuwa.
     Motoci suka shiga, Baffa shi kaɗai sai drivern sa, dan acewarsa zasu ɗauki Alhaji Mansur babban amininsa a gidansa. Sai yazam su Moos'ab sun taru a mota ɗaya su huɗu. AK na shirin shiga wata motar shi kaɗai sai ga Dr Mahmud ya iso. Hakan yasa ya shiga motar Dr Mahmud ɗin kawai da shima dai da alamar shirin tafiyar yazo gidan dama.
        Duk da AK cike yake da mamakin wannan gayya sai baice komaiba. Sun dai gaisa da Dr Mahmud ya tambayi yaya ƙarfin jikinsa daga haka sukai shiru, Dr Mahmud nata juya abinda yakeso su tattauna a ransa ya kasa furtawa, dan duk da AK abokinsane yana girmamashi akan wasu dalilai masu yawan gaske.
      Sai da suna gab da fita cikin garin kano zasu kama hanyar katsina AK ya sake fahimtar bayan motocinsu uku akwai wasuma biye dasu kusan guda uku. Cikin kasa jurewa yace, “Wai nikam wannan gayyar ta minene Baffah yayi?”.
      Ɗan dubansa Dr Mahmud yayi, cikin rashin fahimtar inda zancen nasa ya nufa yace, “Gayya kuma ranka ya daɗe?”.
     “Uhm, ko bakaga motocin dake biye damuba?”.
    Ta mirror Dr Mahmud ya duba bayansu, a nazarce yace, “To inaga dai ba tafiyarmu ɗayaba gaskiya”.
     Shiru AK yayi duk da bai gamsu da hakanba, sai ma ya jawo wayarsa kawai ya shiga daddanawa.
Chapter 82 · 0% Book details