← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 155

Sashe 127

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

gaɓa tata ta gamsu kafin tai wanka ta fito ɗaure da towel ɗinsa daya tsaya mata iya cinya. Batai tunanin samunsa a ɗakinba tunda tasan yana tare da baƙi, sai dai kuma tana fitowa tai turus saboda cin karo datai dashi zaune a bakin gado yana waya. Da baya-baya ta dinga jan ƙafarta zata koma AK ya miƙe yana binta da wani shu'umin kallo daya nema harmutsa hanjin cikinta dan tsoro, dan ita dai harga ALLAH wani irin tsoronsane ya sake tasiri a ranta bayan matsananciyar kunyarsa da bata taɓa ji ga wani ba. Ganin ya taso ɗin ya sata kara sauri, sai dai babu nasara dan taku baifi huɗu yayba ya cafkota. Gaba ɗayanta ya jawo jikinsa yana faɗin, “Okay Baffah sai nazo gidan zuwa anjima ɗin”. Daga haka ya ajiye wayar a ƴar drawer ɗin wajen da suke gab da ita. “Anya wannan jikan na Granny zatai jarumta?”. Ya faɗa cikin wani irin kasalalliyar murya dai-dai yana sa kansa a wuyanta. Duk da wanka tayo hakan bai hana tasirin fitar kamshin mayun khurah ɗinta ba. Ya ƙara tura hancinsa cikin wuyan duk da laimar ruwan dake naso a jikinta. Tare da zagayo duka hannayensa akan cikinta. Cikin rawar murya kamar mai shirin fasa kuka tace, “Yayanmu su Granny”. “Su Granny mi? Ba suna falo ba muko muna nan abunmu a ɗakin sirrinmu”. “Amma zasu ce.....” Ta kasa ƙarawa saboda nauyin maganar. Yana cigaba da shin-shinar wuyan nata dake tada mata tsigar jiki yace, “Zasuce ina lalube amaryana?. To ai suma sunsan tunda suka bani komaima zanyi baby girl”. Zinneerah da kunya ke neman kasheta da mamakinsa, tai saurin cewa “Nifa ba hakaba Yayanmu”. “To yaya ne?”. Ya faɗa yana ɗagowa da birkitota suna fuskantar juna. Kafafu ta shiga matsewa saboda kunyar cinyoyinta dake waje. Yanda take ɗinne ya sashi kallon cinyoyin, idanu ya ɗan lumshe da sake buɗesu a kansu, kafin ya cije lip ɗinsa muryarsa na canja amo yace, “Karfa kisa nai miki wani sabon aika-aikan ALLAH. Muje ki shirya ga abinci har 2 tana neman yi. Kinyi salla ko?”. Kanta a ƙasa ta daga masa kawai. “Magana da baki”. Dole ta buɗe baki tace, “Eh nayi tunma dana tashi naga lokaci yayi”. “Good. kije ki shirya to, ko na shiryaki ne?”. Babu shiri ta waro masa idanunta da har yau ke a ɗan kumbure. Shima waro mata nasa yayi sosai. Hakan sai ya sata jin kunya tai saurin saka tafukan hannaunta ta rufe fuska murmushi na suɓuce mata. Wannan salon nata na nuna yawan jin kunya na kayatar dashi, dan haka ya rungumeta gaba ɗaya a jikinsa yana faɗin, “Ina son wannan salon naki baby. Da gaske fa kina neman shigama Farah hanci, idan kuma ta tashi fyatoki zakiji jiki”. Gaban Zinneerah ne ya faɗi dan itakam sai an amfaci sunan aunty Farah take tunawa da ita, tare da tuna cewa Yay Abdull-Mutallab bafa nata bane ita kaɗai, akwai wadda ta fita tsananin sonsa da kishinsa, komai kuma zata iya aikatawa akansa. lallai tana cikin lukutin yanayi duk randa aunty Farah tazo Nigeria (dan itafa batasan suna nan ba har Mammah). Ganin yanda ta koma saboda ambaton Farah da yayi sai ya ɗauketa cak domin gusar mata da tunanin, saman gadon ya ɗorata yana ƙoƙarin kwance towel ɗin jikin nata ta riƙe gam idanunta na firfitowa waje da jera masa roƙon haƙuri jikinta har rawa yake. Duk yanda yaso ya danne sai ya kasa sai da ya dara. Ya ɗan dungure mata kai da faɗin, “Matsoraciya kawai. Tashi ki shirya kici abinci inason fita”. Yana gama faɗa ya nufi hanyar fita dan ya bata damar da zata kimtsa tunda ya fahimci a takure take matuƙa.
Chapter 127 · 0% Book details