← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 155

Sashe 140

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

............Cikin dakiya Baffah yace, “Wannan hukunci naka yayi dai-dai kuma na gamsu dashi nima wlhy, dan haka nima ga nawa hukuncin akan ƴaƴana da Hindatu. Duk da ni bazan rabaki dasu ba amma tabbas zan nesanta rayuwarsu da taki. Daga yau Abdul-Mutallab zai dawo rayuwa a Nigeria, idan har kikaga ƙafarsa a london sai dai harkar kasuwarsa amma bada rayuwaba. Hukunci na biyu anan gurin nakeson a ɗaura auren Huzaifa da Adilah itama ta baro can har abada sai dai taje domin gaisheki ita da mijinta. Hukunci na ƙarshe karna sake ganin ƙafar Hindatu a gidana har abada, idan kuma ta sake shigowa nima zanyi ƙararta........” Katsesa Abba yayi (mijin mmn sadiq) “A'a dan ALLAH ayi haƙuri Alhaji Kabeer, ai ko babu komai ALLAH ya haɗa tunda gashi har an fara ajiye jikoki bama ƴaƴa ba. Hukuncin dawowar yara dai yayi amma ita kar ace bazata zo nan ba dan ba'asan mi rayuwa zatai nan gaba ba”. Wambai yace, “Maganarka gaskiyane Alhaji Abubakar, a daiyi haƙuri Alhaji kabeer a tsaya kan yaran kawai domin ALLAH. Babu yanda za'ai tunda zuminci ya sarƙa a tsakani, koba komai darajar shi Abdul-Mutallab ɗin da biyayyarsa a ɗagama Hindatu ƙafa. Mai afkuwa ta afku, kamar yanda kuma Malam Sulaiman yay bayani ALLAH ya bama kowa sakamakonsa tun a duniya tunda mainakon nasara duk faɗuwa sukai batare da sun ci nasarar burinsu ba. Koba komai ita wannan yarinya MAKAUNIYAR ƘADDARA ta zame mata BUƊAƊƊEN HASKE, ta mallaki ɗa, ta mallaki uban ɗa, sarƙin dake tsakanin iyayenta ya buɗe, sai muyita mata fatan gamawa da rayuwa mai albarka har ƙarshen numfashinta. Su kuma nema gafararta dan alhakinta bazai barsu cigaba da rayuwa cikin salamaba. Suma kuma waɗanda suka sakema ta'asar a nemesu aji ta bakinsu, idan kuma da amincewarsu ne shikenan ai. Sai a tattara a barma UBANGIJI ikonsa. Koda hukuncin mai martaba aka barsu ya ishi rayuwarsu izina. Masu shirin aikata wanan taɓargazar ko ma suka aikata suma sufa sani sakamakonsu naga ALLAH, dan shine kaɗai yasan hukuncin daya dace ga mutane irinsu. Ina amfanin abinda yahudu da nasara suka ƙirƙira da har zai birgeku wajen aikatawa bayan kuna al'ummar musulmai? Koba komai ka nuna rauninka kenan ga jarabawar da UBANGIJI yay maka domin gwada imaninka. Sannan zata iya yuwa shi wannan ɗan ya girma ma ya gallabi rayuwarka, ƙilama yay sanadin hallakaka ko shigarka wuta. Dan ƴaƴa da yawa sune zasu kai iyayensu wuta. Dan haka ya kamata mu kiyaye, dan kana neman haihuwa bai kamata kabi ta kowacce hanya domin samu ba. Hakan son zuciyace da rashin godiyar ALLAH. Domin idan zaka nutsu ga ni'imominsa ya maka ta hanyoyi da dama ba sai ta haihuwa ba, ko musulinci da yayika aciki da soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W) daya dasa maka a zuciya kawai aka barka ya maka babban ɗaukaka da rahama. Balle wanima zakaga bayan wannan akwai wasu tanade-tanade da UBANGIJIN yayma rayuwarsa waɗanda shi kansa baima san yawan adadinsu ba. Amma saboda kawai ya jarabcesa da rashin samun ƴaƴa sai ya ruɗe ya fita hayyacinsa. Kaiconmu da wannan shiriritar, nasan rashi ƴaƴa nada zafi a rai da damuwa. Amma duk abinda ka ɗaukesa mai sauƙi sai UBANGIJI ya sake sauƙaƙa makashi kai ma a zuciyarka da ayyukanka. Idan kuma ka dage sai ka samu to lallai San zuciya kuwa ai ɓacintane ga duk mai sha'awa ko buri. Duk wanda basu haihu ba ya ALLAH ka azurtasu da zuri'a masu albarka a garesu, idan ba alkairi bane ALLAH ka sakanka musu da abinda yafi alkairi, ka yalwatasu da tarin haƙuri da juriya a zukatansu”. Da amin duk suka shiga amsawa, kuma kowa ya gansu da bayanin waziri, saurama suka shiga tofa albarkacin bakinsu. Sai da duk mazan suka gama kace nace Mahma da tun ɗazun al'ajabin su Zakiyya ya hanata tofa komai ta duba su Zakiyyan. “Wannan shine abinda naketa nusar daku amma kuka kasa fahimta, bansan miyasa a mafi yawan lokuta gatan rayuwa da tagomashin arziƙi dake zuwa cikin hannayenmu ke dulmiyar da zukatajen jin muna sama da kowa ba. Zamu iya zartar da hukunci ga kowa, zamu iya taka kowa dan ko anje an dawo babu yanda zaiyi damu. Duk da dai anata maimaita magana ɗaya amma dolene a faɗa. Kun zalunci yarinya saboda kuna mata kallon mai ƙarancin gata, sai gashi UBANGIJI ya biyo muku ta inda bakuyi zatoba ya ruftaku a ramin da kuka tanadi sakata ku kuka afka. Shi kansa Abdul-Mutallab kun cutar dashi ai, gara ace fitowa kukai kuka shaida masa ƙudurinku, idan ya amince fine, idan bai aminceba sai ku bi duk hanyar data dace wajen ganin kun lallaɓasa ya yardan koku haƙura har ALLAH ya kawo mata iyakar da zata samu. To yanzu dai dukma abinda zai faru ya faru. kun aikata a ɓoye ALLAH ya buɗa kowa ya gani, kunyi danku tsare mutuncinku gashi ya zube a idanun kowa. Kunyi don samun haihuwa, gashi an haihu ɗan yafi ƙarfinku dan nima ina bada goyon bayan hukuncin Abdul-Hakim (Mai martaba), kunyi dan gudun kishiya, ga kishiyar nan mai daraja ma kuwa da inhar Abdul-Mutallab ya wulaƙantata koda na second guda bazamu yafe masaba, dan ta cancanci a kula da ita a riritata. Kunyi dan kar Abdul-Mutallab ya suɓuce muku, gashi ya suɓuce mukun ya dawo inda baƙwaso ya rayu dagashi har ƴar uwarsa. Da wannan kawai aka barku ya isheku, dan nidai banga ribar da kukaciba anan sai asarar kuɗaɗenku dana lokacinku da kukayi a banza a wofi, idan kuma wannan baiwa da waɗan can ma basu yafe mukuba to yanzu aka fara wasan. Koda sun yafe muku sai kuma ku jira hukuncin UBANGIJI a gareku dan shi ne yafimu sanin abinda ya cancanta da mutane masu hali irin naku. Hindatu kinfi kowa ganganci matsayinki na uwa, duk da kuwa Zakiyya ce tai amfani da abinda ke damuwarki ta sarrafaki cikin sauƙi kika afka, amma ba komai ya jawo hakanba sai gurɓataccen tunaninki da son zuciyarki. Wanda inada tabbacin son Kabeer ne ɗawainiya dake ba komaiba, girman kai ya hanaki nutsuwa ki nema sulhu da shi sai kike huce komai akan yaronsa da baijiba bai gani ba. Gashi nan ai kin rasa Kabeer ɗin da Abdul-Mutallab ɗin duka harma da Adilah. ALLAH UBANGIJI ya rabamu da son zuciyoyinmu, ya yalwatamu da haƙurin ibadarka. Daga ƙarshe dan ALLAH ina roƙama ƴan uwana gafara a gareku iyayen Zinneerah, ku yafe musu, karkuyi dubi da halayensu da cutar da sukaima ƴarku. Dan tunkan aje ko ina ALLAH ya saka mata. Dan ALLAH ku gafarcesu ko zasu sami sassauci daga raɗaɗin da za'a bar rayuwarsu da shi. Keko Zinneerah bazance ki yafe musu ba, idan zaki iya yafe musu Alhmdllh, idan kinga bazaki iyaba ki barsu da ALLAH zai cigaba da saka miki ta hanyoyi daban-daban kamar yanda ya fara tun yanzu anan duniya. Kabeer da Hajiya Mama (Hajiya iya) kuma dan ALLAH ku yafe musu badan halinsu ba, kodan darajar Abdul-Mutallab dake a tsakani, dan ya can-can-cin yabo yaron nan ta fannoni daban-daban. Duk da kun sakashi a tsakiya game da wannan al'amari a koda yaushe burinsa yaga ya saka farin ciki a zukatan kowannenku koda kuwa shi zai ƙuntata tashi zuciyar. Dan ALLAH muyi haƙuri mu yafi juna kodan shima yay farin cikin da yaketa fata akan kwanciyar hankalinmu”. Baba ne ya fara jinjina kansa bayan kammalawar Mahma. Yace, “Kinyi bayani mai ƙyau hajiya, kuma nidai ta ɓangarena na yafe musu wlhy, dan koba komai abinda suka aikata ɗin ya zama tsanin nasara ga gudan jinina. Shiyyasa akace idan kaga UBANGIJI ya jarabceka da wani al'amari ka nutsu wajen kwatanta haƙuri dan zata iya yuwuwa wani tsanin zuwa ga nasara ne. Na yafe musu. ALLAH ya yafe mana baki ɗaya”. A take aka shiga amsawa da amin duk cikin farin ciki. Maman sadiq da batace komaiba tun zamanta a wajen, tace, “Tabbas abubuwa da yawa sun faru an maimaita wasu anan amma wasu bazasu maimaituba. Ni shaidace daga wahalhalun cikin nan da yarinyarnan tasha wanda da da ƙarar kwana ranar haihuwarsa da ta bar duniya. Amma Alhmdllh, nagodama UBANGIJIN daya rayata, ya kuma kaimu ga ganin wannan ranar tunda gata a ɗakin mijinta cikin mutinci, kuma gaskiya ta buɗe a garemu ALLAH ya wanketa tun anan dunuya. Da yaso sai ya barmu muyita kallonta da laifin har ranar tashin alƙiyama. Nima na yafe muku domin ALLAH da wasu dalilai da Gwaggo ce silarsu (Hajiya iya) ALLAH ya yafe mana baki ɗaya ya kuma kiyaye na gaba”. Itama godiya suka shiga mata da amsawa da amin. Kafin Hajiya iya ta fara magana. “Tabbas dolene nima nace a yafemin ɗin bisa wani dalili, dan ƙila daban matsama Moddibo da ƙara aure ba da tunaninsu bai karkata ga hakan ba. Ni kuma ba komaine ya sani damuwarba sai ganin yanda matarsa bata ɗaukemi da darajaba. Hakama Hindatu. dan duk da Kabeer ya fita ƙarfin faɗa aji akan yarannan tana nuna masa iko a kansu, ko zancen auren yarinyarnan bamusan komai ba saida yazo gab. Koda yake duk ta wani tone-tone ya wuce, Moddibo ka yafemin kai da matarka dan zan iya saka kaina matsayin silar faruwar komai”. “Bake bace sila Granny, dan koda kikace na ƙara aure baki tursasaniba, sannan tsarin da sukazo muku dashi ya sakaki wannan tunanin kema. Dan haka nikam kima daina neman gafarata bakimin komaiba why”. AK ne ya faɗa cikin dauriyar abinda yakeji game da jikinsa. Mammah ta karɓe da faɗin, “Tabbar Inna ba laifinki bane, nice da wannan laifin, dan daban zurfafa da yawaba akan yaran nan da Zakiyya bataci galaba a kainaba har nakai ga bata goyon bayaba, dan ALLAH Adnan ka yafe min kaji, ajizancine na ɗan adam da son zuciya da tsoron rasaku tamkar yanda gangancina ya kaini ga rasa kabeer. Kishi ba hauka bane, kuma halas ne. Amma irin namu yayi muni da yawa dan muna zafafawa, da nayi haƙuri da hukuncinsa a wancan lokacin da duk haka bata faruba na tabbata. Dan ALLAH ku gafarceni baki ɗaya. Ɗiyata Zinneerah kema dan ALLAH ki yafemin kinji, wlhy bazan ɓoye mukuba tun randa na diro ƙasarnan naga yaron nan da kika haifa ƙaunarki data yaron ta kamani, duk abinda kukaga inayi borin kunyane kawai, amma har cikin raina son ɗanki dake kanki ya shigeni, koda nake cewa kar Adnan ya taɓaki ya
Chapter 140 · 0% Book details