← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 155

Sashe 43

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"الحَمْدُ لله الذِي أَحْيَانَا بَعْدَ مَا أَمَاتَنَا وَإِلَيْهِ النُّشُور"
Alhamdu lillahil-lazee ahyana ba'ada ma amatana wa-ilayhin-nushoor.
       Sai da ta bada ratar kusan mintuna uku bata motsaba dan idanunta su ƙara saki sosai sannan ta tashi zaune tare da zuro ƙafarta ta sauka a gadon. Tayi mamakin ganin an kashe mata wuta da lulluɓa mata bargo, sai dai tasan bazai wuce ɗaya daga cikin su Aunty Safiyya ba. Wanka ta farayi da ɗauro alwala ta fito. Bayan ta gabatar da nafila raka'a biyu ta ɗakko AL-QUR'ANI ta fara duba inda akai mata ƙari jiya a islamiyyasu data koma zuwa ta anguwar su mmn sadiq.
    Tana zaune a wajen har akai salla. Bayan an idar tai Azkar kamar yanda Hajiya Iya ke maimaita mata muhimmancin yinta a kowacce safiya da maraicen duniya. Sai da ta kammala gari yay haske ta miƙe ta gyara ɗakin tsaf kamar yanda ta saba, ta saka kayan ƙamshi ta fice zuwa taya su baba Rahi aiki. Amma sai da ta fara shiga ta gaida Hajiya Iya da mura sannan.
        Sai da suka kammala komai tsaf suka shirya tebir sannan ta koma ɗakin domin yin wanka.
       Sanin ba kowa ke shigowa ɗakinba sai Hajiya iya yasata fitowa kanta tsaye da towel. Sai ƙarami da take ƙoƙarin naɗe kanta data wanke a ciki. Wani irin mugun tsargawa zuciyarta tayi dai-dai lokacin da take fitowa daga ɗan lungun da toilet ɗin yake. Tsabar ruɗani da firgici batama san ta saki towel ɗin da take ƙoƙarin ɗaurawa kantaba a ƙasa....
     Ƙyaƙyƙyawan matashin dake zaune hakimce a bakin gadon ƙafa ɗaya kan ɗaya waya manne da kunnensa ya ɗago dara-daran idanunsa masu cikar gashi da haske yana kallonta da alamun tsantsar mamaki a cikinsu. Hannunsa yakai bisa kwantaccen sajen fuskarsa da babu yawan fara'a a kanta ya shafa ɗan guntun sakewar dake kanta na ƙoƙarin gushewa gaba ɗaya. Sauke hannun daya shafa fuskar yay yana gyara ɗayan dake riƙe da wayar da yakeyi har yanzun yana janye idanun nasa daga kanta yana furzar da wani irin huci daya saka Zinneerah dawowa hayyacinta ta ƙwalla ƙara dan duk zatonta aljanine kawai ya shigo mata, shiyyasa tai sumar wicin gadi.
      Gaba ɗaya ya saki wayar a ƙasa, yay saurin saka tattausan hannunsa ya toshe kunnuwansa yana runtse idanunsa da ƙarfi.

     Kusan rige-rigen shigowa ɗakin akai tsakanin Hajiya Iya da Baba Rahi.  Su duka kan Zinneerah sukayi dan babu wanda ma hankalinsa ya kai kansa. Hajiya Iya ta kamo Zinneerah da alamu suka nuna bata cikin hayyacinta jikinta. “Ya ALLAHU, Zinneerah! Zinneerah kinga buɗe idonki gani tare dake. Miya faru? Ko wani abune ya tsorataki?. Rahi kawo ruwa a bata dan ALLAH da sauri”.
       Fita Baba Rahi tayi da sauri sai gata da ruwa ta dawo. Amsa Hajiya iya tai ta bama Zinneerah daketa faman ɓoye fuskarta a jikin Hajiya Iya nata jikin na rawa dan ta tsora sosai musamman data sake kallon fuskarsa yanzu hankalinta ya sake tashi. Kaɗan ta sha dan bata tare da nutsuwar shansa. Hannunta na karkarwa ta sake ƙanƙame Hajiya Iya  ta nuna inda yake zaune kunnensa toshe, hakama idanunsa a rufe har yanzu.
       “Aljani, wlhy Aljanine Granny”. Tana maganar hawaye na ziraro mata kamar an buɗe fanfo.
       Daga Hajiya iya har Baba Rahi turus sukayi suna kallonsa suma fuskokinsu ɗauke da mamaki musamman Baba Rahi da sam bataga shigowarsaba duk da tana kitchen tana wanke-wanke. Sai dai tabbas taji baƙon ƙamshin turare datai tunanin ko cikin samarin gidanne suka fara shigowa yin breakfast.
         Fuska hajiya iya ta haɗe da kamo hannun Zinneerah dake nunashi har yanzun ta riƙe, ta sake kwantar da ita a jikinta tana shafa mata baya da sauke ajiyar zuciya. “Kinga Zinneerah kwantar da hankalinki ba aljani bane mutumne”.
     “Wlhy ba mutum bane Granny, aljanine, dan aljanine kawai zai iya buɗe ɗakin dana rufe kuma na cire key ɗin kingansa acan na ajiye......”
       “Shiii, ya isa kiyi shiru, Yayankune ba aljaniba, yanada key a hannunsa shiyyasa ya shigo”.
       Kafin Zinneerah ta samu damar cewa wani abu Baffah ya shigo ɗakin saboda jiyo muryar Zinneerah ɗin dake magana tana kuka, sai kuma ya jiyo hajiya Iya itama.
      “Lafiya kuw....” ya kasa ƙarasawa saboda sauka da idanunsa sukayi akansa shima. A take fara'ar fuskar Baffah ta ɓace ɓat. Saurin duƙawa Baba Rahi tai tana gaishesa. Bai iya amsa mataba sai hannu kawai ya ɗaga mata. hakanne ya sakata tashi da ta fice a ɗakin.
           Hijjabin Zinneerah na salla hajiya iya ta jawo ta saka mata, batare da tace komaiba ta kama hannunta suka fice daga ɗakin. Bayansu Baffah yabi shima batare da yace uffanba.
        Kansa dake a duƙe tun haɗa ido da sukai da baffa ya ɗago a hankali yabisu da kallo har suka fice gaba ɗaya. Sake lumahe idanun yay da furzar da huci mai ƙarfi tare da kai hannunsa ya dafe kansa.

        Tsaye cirko-cirko suka iske yaran gidan da suka fara shigowa sashen. Dan har sunji labarin zuwan Yayan nasu gidan a bakin Yaya Khalipha da sukazo tare.
      Wucesu Hajiya Iya tayi riƙe da hannun Zinneerah dake sharar hawaye ɗakinta. Baffah kuma ya nifi dining shima fuska a ɗaure.
     Baffa mutum ne mai barkwanci ga yaransa, amma idan ransa ya ɓaci dolene kowa ya shiga hankalinsa. Da sauri Safiyya ta taso inda yake ta fara ƙoƙarin haɗa masa abincin gabansa. Hakan yasa suma sauran yaran nufo dining ɗin duk suka zauna. Hajiya Iya ce ta fito daga ɗakinta tana ƙwalama Jamal kira. Dai-dai yana ƙoƙarin zama danshi shigowarsa ma kenan sashen baisan mike faruwa ba.
      “Na'am Granny ”.
Ya amsa yana maida kujerar daya jawo tare da juyawa gareta.
     “Ka shiga ɗakin can ka ɗakkoma Zinneerah Uniform ɗinta da jikkarta”.
      Cikin rashin damuwa da abinda tace ɗin, yace, “Okay maa”.
     Yanda ya nufi ɗakin kansa tsayene ya saka sauran ƴan uwansa binsa da kallo. Bahijja ta saka hannun ta rufe bakinta jin dariya na neman kufce mata. Meenal kam ƙasa tai ƙarƙashin tebir tamkar zata gyara wani abu tayi tata.

       “Oh ni Jamal ni za'a saka na ɗakkoma ƙanwata abu. yau yarinyarnan zatasha ƙwanƙwashe a kai kuwa a class na rantse”. Yay maganar yana tura ƙofar ɗakin da shiga kansa tsaye.
     Wani wawan birki yaja yana waro idanu waje ganin wanda baiyi zatoba tsaye yana ƙoƙarin zame rigar saman suit ɗinsa. Cikin rawar baki yace, “Bar... Ba.. Barka da zuwa Yayanmu. Kazo lafiya? An barosu lafiya? Ya hanya?”.
     Yanda ya jero gaisuwar kawai zaka fahimci a kiɗime yake. Shiko da ake gaidawar kallo ɗaya yay masa ya janye idanunsa batare daya amsa ko ɗayaba a ciki, dan gaba ɗaya ransa a dagule yake. Yasan shiɗin mai laifine ga mahaifinsa da kakarsa. Amma yayi zaton Baffa ya yafe masa kamar yanda ya roƙesa tun a waya kafin ya taho....
     Da sauri Jamal ya juya zai fice a ɗakin....
          “Mi kake buƙata?”.
   Nutsatstsiyar muryarsa mai kama data rowa ta bayyana cikin kunnuwan Jamal. Tamkar zai fasa kuka ya juyo garesa. “Yayanmu Granny tace nazo na ɗaukama Zinneerah Uniform ɗinta zamu wuce school”.
      Uffan baice da shi ba, sai ma towel daya ɗauka a akwatin da yazo dashi ya nufi toilet abinsa. Jamal na ganin ya shige ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, tare da nufar Uniform ɗin Zinneerah dake ajiye a bakin gado ya ɗauka sauri-sauri tare da schoolbag ɗinta da takalma ya fita da gudu.
        Shikam koda ya shiga toilet ɗin kallon tsaf ya shiga masa, dan a rayuwa ya tsani ƙazanta. Jin ƙamshin toilet ɗin gaba ɗaya ya canja daga nashi ya sakashi cije baki a ransa yana raya hukunci da zaima yarinyar nan da har idonta yay tsaurin shigo masa ɗaki tai wanka. Gamsuwa da tsaftar bayin ya sakashi ƙoƙarin ajiye towel ɗin hannunsa a bazata idonsa ya sauka akan B&P ɗin Zinneerah data shanya. Kauda ido yay yana wani cizar baki da rinmtse idanu da ƙarfi, a fusace ya rataye towel ɗin ya fito yana ƙwala kiran sunan Jamal.
       Wayam babu Jamal a ɗakin alamar ya gudu, ya riƙe ƙugunsa da hannaye duka biyu idanunsa na canja launi saboda haushi. Ƙofa ya nufa kamar zai fita sai kuma ya fasa ya dawo da baya yanayin ƙwafa. Haka ya haƙura ya gudanar da dukan uzirinsa, sai dai sau goma idonsa yakai ga kayan sai sun sami tsarabar harara talatin da tsaki. Sai wani faman yamutsa fuska yake tamkar yau ya fara ganin irinsu.
Chapter 43 · 0% Book details