← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 155

Sashe 31

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

      Bayan Gwaggo Maryama tayi wanka da salla sukai zaman cin abincin zuminci da ƴar uwarta. Yayinda little kenan tare dasu a falo nata wasansa konace ɓarna. Zinneerah kam tuni ta shige ɗaki dan zazzaɓi nema ke neman rufe mata jiki.
      Gwaggo Maryama ƙanwa ce ga Maman Sadiq. Uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Sukaɗai mahaifiyarsu ta haifa a duniya ALLAH yay mata rasuwa, dan haka akwai shaƙuwa mai ƙarfi da ƙaunar juna tsakaninta da ƴar uwartata wadda ƙaddarar aure takai can Minna jihar Niger. A yanzu haka itama ta zuba iyalai acan Alhmdllh.
         Kaf labarin Zinneerah da dalilin zuwanta nan wajensu da samuwar Little Maman Sadiq sai da ta zayyanema ƴar uwarta dakeshan kukan tausayin Zinneerah har cikin ranta. Tare da ɗaukar dukan laifi ta ɗora akansu suda sukai wasarere da lamarin Zinneerah ɗin bayan sunsan rashin imani irin na Asabe. Tunda har ta iya rabo Maman Sadiq da mijinta itama Zinneerah ɗin ba barinta zataiba.
        Murmushi mama tayi, cikin son kwantarma da ƴar uwarta hankali ta shiga nuna mata komai ƙaddara ne. Tunda UBANGIJI ya hukunta sai Zinneerah tai irin wannan rayuwar babu wani daya isa hana hakan a cikinsu ai. Sai dai su cigaba da mata fatan alkairi kuma a rayiwarta ta gaba. Wannan kam ta rigada ta faru kuma.
         “Hakane Yaya Hauwa. Amma wannan tabon bazai taɓa goguwa a zuciyar yarinyarnanba dangane da watsi da mukai da ita bayan duk munsan a inda take”.
      “To yadai wuce yanzu dan ALLAH. Muci abinci koma kimtsa kafin Yaya ya shigo gidan muji yanda za'ai tafiya inda Inno take. Dan da san samune mu tafi yau duk da naga garinma dai yana haɗe fuska alamar hadari”.
        Da wannan maganar ta Maman Sadiq bakin Gwaggo Maryama yayi shiru. Suka ƙarasa cin abincin da saida ta matsa mata. Daga haka suka zauna zaman hirar zuminci da jiran dawowar Abba gidan.

     Kamar yanda su Maman Sadiq ke jiran dawowar Abba iyalan Maman Sakina ma zaman jiran dawowar tasa gidan suke cike da alwashin sai Zinneerah tabar gidan yau ɗin nan. Duk da sun shige ɗaki basubar zage-zage ba da aibanta Maman Sadiq da Maman Halima. Dan ko abincin rana yau sunƙi zuwa su ɗakko na ɗakinsu har yamma tayi yara suka dawo daga makarantar islamiyya.
         Tunda su Abdull sukaga Gwaggo Maryama suka rikice da murna sosai. Itama taji daɗin ganinsu. Ta haɗasu a jikinta ta rungume harda Little daketa walwalar ganinsu.

        Bayan an idar da Sallar Magriba Sadiq yazo yana sanarma Mama Auntynsu bata da lafiya. Kafin tace wani abu sallamar Abba ta shigo kunnuwansu alamar ya dawo gidan kenan.
       Duk da suna a cikin ɗaki ba kuma nan ya shigoba kai tsaye sai da suka amsa. Su Sadiq duk suka fice yima Abban sannu da zuwa kamar yanda suka saba idan ya shigo suna gida.
     Wuff Maman Sakina ta fito daga ɗakinta tunda taji sallamar mijin nasu. Kusan a tare suka shiga falonsa da ita da yaran. Sama-sama ta gaidashi, zata fara kumfar baki ya ɗaga mata hannu dan dama tun a yanayin data shigo yasan gidan babu lafiya. Ga kuma Aliyu na faɗa masa Auntynsu bata da lafiya tana ɗaki kwance.
      “Salla zanyi, sannan kinsan dokata a gidan nan bana buƙatar yin maganar da duk bata shafi alkairiba a gaban yarana. Dan haka ki koma sai anjima idan na nutsu kizo miyi magana ba yanzu ba”.
     Wani irin baƙin cikine ya turnuƙe zuciyar Maman Sakina. Ta fito fuuu kamar zata tashi sama. Da kallo kawai ya iya binta yana mai girgiza kansa.

     A ɗaki kuma Gwaggo Maryama ce da kanta ta miƙe zuwa wajen Zinneerah da Sadiq yace bata da lafiya. Ƙudundune ta sameta cikin bargo tana rawar sanyi. Saurin ƙarasawa tai gareta tana faɗin “Subahanalillahi Zinneerah dama baki da lafiya amma kikayi shiru?”.
    Kafin Zinneerah ta bata amsa Maman Sadiq ta shigo ɗakin itama. Duban inda take kwancan tayi tana bama Gwaggo Maryama amsar zancenta. “Tunda ta iya cin dambe ba dole tai zazzaɓi ba. Ki tashi kiyi wanka da ruwan zafi kici abinci kisha magani, dan wannan dai zazzaɓin bai wuce sanadin hayaniyar nan ba”.
    Cike da takaici Gwaggo Maryama tai tsaki. “Shi dai yaya ya auroma kansa masifa wlhy. Ayi mace bata son zaman lafiya kamar dangin yahudawa”.
      “Humm ai kaɗanma kenan Maryama, dan wannan fitinar ba mutuwa taiba rufa tai, na tabbata jiran dawowar maigidan take, bara kuma kiji zakice nina faɗa miki”.
      “Fitinanniyar banza. Gashi nan duk tabi ta koyama ƴaƴa hali mara amfani, aini Zinneerah ta birgeni sosai data nuna musu ƙyalesu dama kawai take ba tsoro bane. Shi kuma yayan tunda yasan halinta dama ai kinga sai yay musu iyaka yanzun”.
      “To ALLAH yasa. Dan da kike ganinta a haka son matarsa yakeyi”.
       Kiran sallar magriba da aka kirane ya katse hirar tasu. Zinneerah kam dama harta shige bayi tuni.

       Bayan idar da sallar magriba Gwaggo Maryama ta tsare Zinneerah taci abinci tasha magani sannan ta kwanta. Maman Halima ma ta kawoma Gwaggo Maryama nata abincin yaɗan zauna sukai hira bayan ta shiga ta duba Zinneerah data sanu barci. Kiran sallar isha'i yasata komawa nata sashen.
        Alhaji da yara kam basu shigo gidanba sai da aka idar da sallar isha'i. Harda Little da yay barci. Gwaggo Maryama ta amshesa ta goya tana maijin tausayin yaron a ranta.
        Sai da Maman Sadiq ta tabbatar Alhaji yaci abinci ya huta sannan suka fita ta raka ƴar uwarta danta gaidashi. Sai da sukai sallama ya amsa shi da Maman Halima dake tare da shi  sannan suka shiga. Sosai fara'ar fuskarsa ta daɗu yanama Gwaggo Maryama lale da zuwa dan dama yara sun sanar masa zuwanta.
       Suna kaiwa zaune sai ga Maman Sakina tamkar an jehota falon dan ko sallama basa tunanin tayi. Kallonta Alhaji yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya maida hankalinsa ga Gwaggo Maryama. Hakan da yayine ya saka Maman Halima da Maman Sadiq suma yin kamar basusan da shigowar tataba.
       “An haɗa kai an shigo dan a ƙulla mana sheri ni da ƴaƴana. To ta ALLAH bata mutumba”.
     Babu wanda ya tanka mata. Sai da Alhaji ya gama gaisuwarsa ta zuminci da Gwaggo Maryama sannan ya dubeta fuska a tsuke. “Saude yaushe ne zakisan inda ke miki ciwo ne wai kekam?”.
        “Taya kuwa zansan ciwon kaina agola ta haɗani da ƴayana ta doka saboda an gina mata jiki da tuwon gero dana dawa Abban Luba”.
      Kallonta kawai yake batare daya tankaba. sanin baya son jan rai a magana ya sata fara zayyane masa abinda ya faru, sai dai tanayi tana haɗowa da ƙarya da sheri. Tsam Gwaggo Maryam ta miƙe zata fice ya dakatar da ita. “Maryam kina gidan duk akai wannan?”.
      “A'a gaskiya Yaya kafin nazone. Nadai iske kawai suna rikicin faɗa nashiga na taya Maman Halima rabawa”.
      Komai baiceba sai kallonsa daya maida ga Maman Sadiq. “Ina Zinneerah ɗin take?”.
     “Tana can kwance babu lafiya”.
“A dalilin shi wannan rikicin kenan?”. Ya tambaya yana cigaba da dubanta.
    Kafin ta amsa masa Maman Sakina ta karɓe da faɗin, “Andai shirya munafunci kawai za'ace, yo inba munafun........”
     “Saude!”.
Ya katseta a tsawace. Badan tasoba dole tai shiru. Yaja tsaki da faɗin, “Da safe inason ganinku dukanku har yaran”. Ya faɗa yana miƙewa ya fice.
    Ganin haka ya saka su Maman Sadiq miƙewa suma duk suka fito. Sai dai a mamakinsu sai hangarsa sukai ya nufi sashenta da alama duba Zinneerah zaijeyi.
     Hakan yama Gwaggo Maryama daɗi sosai, duk da dama tasan halin ɗan uwan nasu baya wasa sam da lamarin gidansa. Amma batai tunanin Zinneerah ta samu matsayi na musamman haka a garesaba.
      Bayan ya shiga ya dubata tana barci dan haka ya fito falo. Batare da dubansuba ya nufi hanyar fita yana faɗin, “A tada ita muje ko nan kyamis ɗin Umar ne tunda dare yayi”.
     Halinsa da Maman Sadiq ta sani yasa bataja zancenba taje ta tado Zinneerah suka tafi kyamis ɗin. Itako Saude nacan tana tijara a sashenta kamar zata haɗiye haƙoranta, musamman ma dataga Alhajin ya fita tare da Zinneerah da Sadiq.

WASHE GARI

        Washe gari da safe Zinneerah ta tashi Alhmdllh babu zazzaɓin dan tasha allura jiya. Bayan idar da salla suka zauna zaman hira ita da Gwaggo Maryama dake janta a jiki cikin hikima. Sai da gari yay ɗan haske suna shirin fita gaida Alhaji sai gashima ya shigo duba Zinneerah ɗin. Kanta a ƙasa ta gaidashi. Ya amsa mata da kulawa kamar yanda ya saba da tambayarta kuma jikinta.
     “Alhmdllh Abba naji sauki”..
“Haka akeso ai, ALLAH ya ƙara lafiya”.
    “Amin” suka amsa gaba ɗaya.
Chapter 31 · 0% Book details