← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 155

Sashe 45

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

..........Ƙarfe biyar da rabi motar dake ɗakko su Zinneerah makaranta ta shigo harabar gidan. Kamar yanda ta fita gidan da damuwar baƙon dasu Jamal ke kira Yayansu haka ta dawo da ita a rai. Babban damuwarta ya ganta daga ita sai guntun towel a jiki. Gashi yanda taga fuskarsa da yanda su Meenal ke labarinsa tasan ba kirki zaiyiba sam, sai kuma wani abu mai kama da almara da take hangowa, wanda ƙwaƙwalwarta sam ta kasa ɗauka.
        Kamar kazar da ƙwai ya fashema a ciki haka ta nufi sashen Hajiya iya tana mai addu'a a ranta ALLAH yasa baya nan. Koda tazo ƙofar falon sai da ta tsaya tai addu'a sannan ta shigo bakinta da sallama. Da sauri taja birki a taku huɗu, dan tun sakko ƙafarta ciki hancinta ya shaƙo mata mayataccen ƙamshin turare. Bata kawo a ranta falon yakeba idanma shine, sai da ta ƙarasa shigowa sosai idanunta sukai gamo maiban ruɗani, dan a yanzune ta sake samun damar yimasa kallo mai ƙyau.
      Zaune yake bisa kujera 1seater dake facing kofar, ƙafarsa ɗaya kan ɗaya. Hajiya Iya na zaune kujerar gefensa tana dama fura. Sai wanda bataga fuskarba saboda juya mata baya da yayi. Har cikin ranta taji daɗin samunsa bashi kaɗaiba duk da bataso ganin nasaba ma gaba ɗaya.
       Sallamarta Hajiya iya ta amsa fuska ɗauke da murmushi take faɗin, “Ƴan makaranta an dawo?”.
       Cike da ƙarfin hali Zinneerah ta sakima Hajiya Iya murmushi da faɗin, “Eh Granny barka da yamma”.
       “Barka dai Inno na, da alama yau kam an dawo da yunwa naga kinyi zuru-zuru?”.
       Murmushi tayi batare da tace komaiba. Ta ɗan saci kallon inda yake zaune idonsa a wayarsa dake hannunsa yana latsawa tamkar baisan da shigowartaba. Sai dai abinda bata saniba cikin abinda baifi sakkani ashirinba ya gama ƙarema shigar Uniform ɗin jikinta kallo. Skirt ne iyakar ƙwauri pink color. Sai farar shirt dataji guga da baby hijjab fari daya tsaya mata iya ƙirjinta shima dai a gogen yake. Sai farar safa data rufe ƙwaurin nata da farin takalmi. Bayanta goye da school bag ɗinta data saki hannunta guda. Babu mai cewa Zinneerahn danya ce data taɓa rainon ciki harta haifesa yake gudu ko ina da kafarsa a halin yanzun. Baka iya hango komai tattare da ita sai zallar ƙuruciya da jin daɗin rayuwa na canjin data samu cikin ƙanƙanin lokaci.
         “Yayanmu barka da yamma”.
Ta faɗa ciki-ciki tsabar fargaba da tsoron dake mamaye da ita. Harta fidda rai zai amsa sai taga ya ɗaga mata hannu alamar amsawar kenan.
     Gaba tai zata wuce, batare da ta gaida ɗayan wanda bata ganin fuskar tasa ba. A tunaninta ko shi baisan da shigowarta ba. Sai da taɗan gitta su taji ashe waya yake amsawa. Numfashi ta sauke da nufar ɗakin Hajiya Iya da saurinta, dan bata fatan abinda zai sake tsaidata a wajen. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali dai-dai tana saɓule school bag ɗinta da zubewa akan sofar ɗakin. Zamewa tai ta kwanta ko jininta daya ɗauke na wucin gadi zai dawo aiki jikinta yanda ya kamata.
        “Kina lafiya kuwa Zinneerah?”.
Hajiya iya data shigo ta faɗa tana kai hannunta saman goshin Zinneerah dake kwance rigingine. Buɗe idanu tai a hankali tana kallon Hajiya Iyan, ta yunƙura zata tashi Hajiya iya tace, “Kinga yi kwanciyarki abunki. Amma kina lafiya dai ko?”.
       “Lafiyata ƙalau Granny, na gajine sosai yau shiyyasa”.
     “Tofa, halan tsalle-tsallen wofin nan naku kukayi a makarantar ko?”.
    Ƙaramar dariya Zinneerah tayi tana tashi zaune saboda ganin a yanda Hajiya Iya tai magana fuska a yatsine. “Granny yanzu yaya zanyi kayana nacan ɗakin fa. Ni kuma wlhy wannan mutumun tsoro fuskarsama take bani. ALLAH yasa dai baiyi faɗan ganina a ɗakinsaba”.
       “Idan yayi tsoronsa zanjine Zinneerah? Indai Moddibo ne ma bar wahalar da kanki wajen tsoron wani faɗansa na wofi. Shi haka yake baida fara'a dason hayaniya. Harkar kowa kuma ba shiga yakeba sai idan yaso hakan dan kansa. Tashi kije ki ɗakko kayan da zaki saka, zuwa weekend idan ALLAH ya kaimu sai ki tattaro kayan da zakiyi amfani dasu harya tafi kafin ki koma”.
     Cikin waro idanu Zinneerah tace, “Granny kina nufin sake koma masa ɗaki zanyi da zama?”.
       “Oh to kajimin ja'ira bakison ɗakinne?”.
      “Nidai zan zauna dake anan. Ɗazu ɗinnan da ace babu kowa a gidannan da yazo ya sameni a ɗakinsa ai kakkaryani zaiyi yasin”.
     Yanda take maganar da iya gaskiyarta yasa Hajiya Iya yin dariya. “Idan bazaki takuraba anan ɗin nima zanfi jin daɗin ganinki kusa dani. Dama danki sake yasa nace kije ɗakinsa ki zauna a binki ai. Yanzu tashi ki watsa ruwa sai kizo kici abinci duk kinmin zuru-zuru a idanuna”.
       Miƙewa Zinneerah tai tana ƙoƙarin cire baby hijjab ɗinta. Hajiya iya kuma ta fice a ɗakin.

       “Granny wai keda wa naji kuna magana ɗazun ina waya?”.
    Khalipha ya faɗa dai-dai Hajiya iya data fito tana kaiwa zaune. Sai da ta zauna ta bashi amsa da, “Ƙanwarku ce mai kama da Inno. Yanzu zata fito sai ku gaisa”. Cikin rashin damuwa da sonjin daga ina yace, “Okay. Bara naje nan waje ga Sadam yana jirana zamu ɗan fita. Yayanmu baka buƙatar komai?”.
         Har yanzu idanunsa nakan wayarsa tun yanda Zinneerah ta barshi. Ya ɗan ɗago kansa ya duba Khalipha ɗin ya maida. “No jeka abunka. Nima zuwa 6:30 Mahmud zai shigo muɗanyi magana”.
     “Okay bye, insha ALLAH zan dawo nima kafin ya tafi. Dan nasan yau tare zakuci abincin dare. Granny bye”.
       “A dawo lafiya”. Ta faɗa dai-dai yana ɗaga mata hannu zai fice.

     Koda Zinneerah tai wankan ƙin yarda ta fito ɗaukar kayan tayi, duk da tanajin yunwa ta gwammaci ɗaukar sauran biscuit ɗinta dake cikin jakka taci, a ranta addu'a take ALLAH ya kawo wani acikin su Jamal ya taimaketa ya ɗakko mata kayan. Sai dai addu'arta bataciba. Dan muryar Hajiya Iya ta tsinkayo tana ƙwala mata kira. Hijjab ta ɗauka ta fito badan tasoba. Hajiya iya dake kallonta tunda ta fito tace, “Wai nikam bazakizo kici abinciba kika maƙale a ɗaki kamar wata sabuwar amarya?”.
        “A'a Granny dama yanzu zan fito”. Ta faɗa tana satar kallonsa ta gefen ido. Yanzu kam waya yake a kishingiɗe saɓanin ɗazun. Saurin nufar kitchen tayi ɗebo abincin a bazata ta tsinkayi nutsatstsiyar muryarsa mai kama data rowa cikin kunnenta a karon farko. “Ki kwashe tarkacen da kika barmin a toilet”. 
      Duk da ba ita yake kalloba ta tabbatar da ita yake. Tuna abinda ta bari ɗinne ya saka kunya mai tsanani lulluɓeta. da sauri tabar wajen.
     Gaba ɗaya turarensa mai ƙarfi ya danne nata daya fara zama a ɗakin cikin wuni ɗaya. Toilet ta wuce sum-sum tamkar yana a cikin ɗaki. Ganin alamar yayi amfani da toilet ya ƙara saka zuciyarya shiga cikin wani irin matsananciyar kunya. Ta kwaso kayan tana rintse ido kamar ta fasa ihu. shikenan ya gama gane mata sirrinta wayyo ita Zinne. Koda ta fito sum-sum ta wuce bata yarda ko sashen da suke ta kallaba.

      Fitar da yay da daddaren saboda zuwan abokinsa Dr Mahmud ta bama yaran gidan damar shan sharafin hirarsu yanda suka saba. Sai dai anayi ana leƙen waje wai karya shigo. Sai ma ALLAH ya taimakesu har suka tashi bai shigo ɗinba.
     Washe gari da safe ma har suka gama breakfast kowa ya fice yana ɗaki bai fitoba. Kasancewar juma'a ce da wuri su Zinneerah suka dawo gidan.
              A bedroom ta iske hajiya iya zaune tana karatun AL-QUR'ANI. Bata zaunaba ta ajiye school bag ɗinta da cire hijjab ɗinta ta fice zuwa kitchen dan yunwa takeji, yau bata wani zauna tayi karin kirkiba suka fita makaranta. Gaba ɗaya ta shafa'a da kasancewar sa a gidan. dan haka ta fito kanta tsaye ko ɗan kwali babu akan nata. Sai gashinta data wanke dan zuwa kitso dake ɗaure a tsakkiya. Tanada gashi duk da bamai wani uban tsaho bane, dan yakanzo mata dai har kafaɗa musamman idan ta wankosa a saloon.
        A yanda take tafiyar yasa sam bataga mutum dake tahowa a gabantaba. Gab sukai karo da juna. Ta ɗago a firgice tana murza goshinta zatai magana, amma sai maganar tata ta maƙale a maƙoshi ta tsaya kawai tana kallomsa. Shima ɗin dai kallo yake mata irin na sani, sai dai ya kasa tunano a inda yasan fuskar.
        Baki ta buɗe da nufin ambaton sunansa ya katseta yana murmushi. “Sorry Beauty. Ko kece Sister ɗin tamune?”.
        Saurin haɗiye maganar tata tai itama mamaki na neman kasheta a tsaye. Kenan bai ganetaba komi? Kokuwa basarwace irinta masu hannu da manda. Aiko inhar hakane itama ta iya ai, musamman a yanzu da take ƙara samun wayewar rayuwa da zamantakewa wajen malamta su Jamal.
       Kanta ta kaɗa masa tana ƙaƙaro murmushi. Tace, “Eh nice Yayanmu, kunzo kafiya?”.
        “Alhmdllh, amma kinma sanni kenan?”.
      “Eh mana. Na sanka a bakinsu Bahijja”.
      “Kai-kai a bakin magulmatan gidannan kenan. to ALLAH yasa dai basu koyama ƙanwar tawa gulma ba?”.
         Ƙayataccen murmushi ta saki har haƙoranta na bayyana fili. Hakan yayi dai-dai da isowarsa wajen. Ta buɗe baki da nufin bama Khalipha amsa idanunta suka faɗa cikin nashi. Wani irin yarrr tsigar jikinta ta tashi, tai azamar maida kanta ta duƙar ƙirjinta na bugawa saboda abinda zuciyarta ta hasko mata a yanzunma kamar jiya data fara ganinsa, koma wanda yafi na jiyan, idanunsu iri daya hatta da kwayoyin ciki.
      Juyawa Khalipha yayi domin son ganin abinda ya hanata maganar, yay murmushi a dai-dai sanda yayan nasu ke ƙoƙarin gittasu tamkar baima gansuba. Da sauri Khalipha yace, “Barka Yayanmu”.
     Hannu ya ɗaga masa kawai yawuce abinsa. Hakan yasa Khalipha ƙara matsawa gaban Zinneerah da kanta ke a ƙasa. Cikin raɗa-raɗan magana yace, Beauty bara muje massallaci, idan na dawo zakizo ki tayani hira”. Daga haka yabi bayan Yayan nasu ɗakin Hajiya Iya daya shiga.
        Nannauyan numfashi Zinneerah ta sauke tare da lumshe idanu ta dafe kirjinta. Zuciyarta na gargaɗinta akan abinda ƙwaƙwalwata ke hasko mata maiban tsoro da ruɗani. jiki a saɓule ta wuce kitchen dan neman abinda zata sakama cikinta ko taji dama.
Chapter 45 · 0% Book details