← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 155

Sashe 25

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sati ɗaya dayin wannan magana Alhaji ya shirya zuwa Kusada ƙauyen Danya batare da sanin Zinneerah ba.
        Kasancewar a ranar yaje ya dawo kuma bata san komai akaiba tunda tasan yana fita kasuwa dama. Abinda dai kawai ta fahimta ranar Mamansu ta kwana cikin wani irin yanayi na tsantsar baƙin ciki. Dan harta kai washe gari ma sai da aka kwantar da ita asibiti. Kwananta ɗaya aka sallamota ta dawo gida. Zinneerah ta shiga damuwa da ganin yanayin na mamansu daya kaita ga kwanciya asibitin. Amma sai rashin wayo ya hanata tambaya koda suka dawo. Kallo ɗaya zakai mata itama dai ka fahimci tana cikin damuwar.
      Kusan kwanaki goma tana ganin Maman tasu a wannan bahagon yanayin, kafin kuma taga ta warware ta cigaba da harkokinta a gidan cike da ƙarfin hali.
        Abinda Zinneerah bata saniba shine mummunan labarin da Alhaji yaje ya samo a garinsune yakai ga mahaifiyarta kwantawa asibiti saboda motsawar hawan jininta. Sai dai kamar yanda Alhaji ya gargaɗeta yin gum da bakinta kar Zinneerah da abokan zamanta susan wani abu game da cikin Zinneerah ɗin yasata shanye komai a rai ta fawwalama UBANGIJI ikonsa da amsar ƙaddara. Musamman daya kasance duk wanda Alhaji ya jiyo labarin cikin Zinneerah a bakinsa saida ya yabi kyawawan halayyarta da wahalar data dinga sha ga matar ubanta. Harma takai wasu na ganin Inna ce silar komai akan cikin na Zinneerahn.
           Hakan yaɗan sake girmama danganarta ta shanye komai ko a fuska basu taɓa nuna Zinneerah sunsan komaiba daga ita har Alhaji. matan gidan kuma sun sanar musu cewar ashe mijin Zinneerah ɗinne ya mutu kawai, ruɗanin rasuwarne ya sata baro gida cikin gushewar hankali. Maman halima ta tausaya mata, Maman Sakina kuwa ko'a jikinta. saima ƙorafi data dingayi akan kenan an ƙara ma mijin nasu nauyi tunda dai nan Zinneerah zata cigaba da zama ita da abinda zata haifa.
     Babu wanda yabi takanta dan idan da sabo kowa ya rigada ya saba da halinta a gidan ai.

         Zinneerah ta cigaba da rainon cikinta aɗan tsakanin nan cikin rashin jin daɗin jiki, dan tunda ya shiga wata na tara komai ya sake mata wahala. Harma takai randa suka koma asibiti dole Doctor ɗin ya riƙeta akan zata cigaba da zama anan har saita haihu.
     Hakan baima Zinneerah daɗiba. Amma yaya zatiyi tunda ance wannan ne samun sauƙi a gareta. Yanzunma dai Maman Halima ce tare da ita, sai Mamanta dakanzo duk bayan kwana biyu ta amsheta ita kuma taje gida ta huta. Abba kam babu fashi kullum sai yazo safe da dare dubata. Ko'a fuska bai taɓa nuna ƙyamar cikin jikintaba balle bakinsa ya suɓuta wajen faɗama matansa dalilin samuwarsa.
       A randa ta cika kwana tara a sibitinne da Naziru yazo dubata yake faɗa mata kwana biyu bayajin Khalipha kwata-kwata. Yayi ƙuru ya gwada kiransa ranar kuma bata shigaba. ya tura masa saƙo babu reply har yanzun.
       Murmushi kawai Zinneerah tai na ƙarfin hali batare da tace komaiba. Hakan yasa shima bai sake cewa komaiba akan batun.

      Washe gari data cika kwana goma cif a asibitin jikinta ya ƙwaɓe ta fara zubar jini (bleeding). Hankalin likitocin ya tashi harma da su Maman Sadiq dan sun fahimci naƙudace tazo mata a bahagon yanayi. Tun suna ganin zata iya haihuwa da kanta har al'amarin yasoyin tsamari suka yanke shawarar mata cs kawai.
     Babu wani ja'inja Abba ya saka hannu matsayinsa na uba gareta. Daga haka suka shiga da ita ɗakin theatre su kuma suka koma gefe suna mata addu'ar rabuwa lafiya da abinda ke a cikin nata.

        Awa kusan uku Doctor Mansura ta fito fuskarta da murmushi. Duk miƙewa sukai suna mai sauke ajiyar zuciya ganinta a yanayi mai daɗi. Ta sake faɗaɗa murmushin da faɗin, “Alhmdllhi, an ciro baby boy ƙyaƙyƙyawan gaske, mai kuma lafiya insha ALLAH”.
        Basu gaza wajen ambaton Alhmdllh ɗinba suma, dan sunyi imani akan duk abinda kaga UBANGIJI ya jarabceka da samu ta hanyar da kai baka buƙatarsa ya fika sanin dalilin yin hakan. Basu isa canja ƙaddarar Zinneerah ba komai son hakan da zasuyi, sai dai su tayata da addu'ar ALLAH yasa haka shine mafi alkairi. Duk da har cikin ransu suna tsananin tausayin uwar da ɗan.
       Abbane yace, “Yaya jikin ita Zinneerah ɗin kuma?”
       “A Alhmdllh Alhaji. Itama dai insha ALLAH komai zai dai-daita zuwa nan gaba kaɗan. Kuyi haƙuri sai zuwa anjima zaku samu ganinsu koma da safe”.
       Godiya sukai mata. Ta wuce su kuma suka koma suka zauna kowa da abinda yake saƙawa a ransa.

    ★★★

     Kamar yanda likita Mansura ta faɗa basu sami ganin Zinneerah ba a ranar dai kam, sai dai zuwa yamma an fiddo musu da jariri ƙaton gaske kuma ƙyaƙyƙyawa kamar yanda Dr Mansura ta faɗa ɗazun.
     Abba ne ya fara amsarsa yana mai yin godiya ga ALLAH tare da jin tausayin yaron da baisan wanene shiba. Bayan ya masa addu'a ya miƙama Maman Halima daketa faman washe baki. Tace, “Masha ALLAHU mijin nawa kam dai-dai ni. ALLAH ya rayaka ya albarkaci rayuwarka. Ya jiƙan mahaifinka kaji”.
        Da amin suka amsa. Kafin ta miƙama Maman Sadiq dake kukan zuci. Bata musaba ta amsa itama ranta fal tausayin yaron dabaijiba bai ganiba. Ta ƙura masa idanu na tsahon lokaci zuciyarta na suya akan samuwarsa ta hanyar da ba ita sukai fataba. Sai dai a gefen zuciyarta na gargaɗinta da ambaton Alhmdllh. Dan babu maima UBANGIJI dole akan abinda yaso. Babu kuma mai sakashi saɓanin hakan.
     Itama dai addu'ar tai masa tamkar kowa ta sake miƙama Maman Halima dake kusa da ita. Ita kuma ta miƙama Matar Naziru. Bayan sun gama ganinsa da masa addu'a Nurse Salima tazo ta amshesa tana faɗin, “To waye zai zauna a wajenta? Dan an kaita ɗakin hutu yanzu haka. Sai dai likita tace wadda zata zauna da ita kawai za'a kai sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zaku ganta”.
        Dukansu sun gamsu da hakan, kafinma kowa yay magana Maman Halima tace ai bama sai anja zanceba itace zata cigaba da zama da ɗiyarta.
    Wannan karamcin na Maman Halima kesa Maman Sadiq jin daɗi sosai da sake ganin girmanta da kimarta a koda yaushe, dan mace ce data cancanci girmamawa kodan ƙyawawan halayenta.
         Sallama tai musu tabi bayan Nurse Salima. Su kuma suka fito domin komawa gida.

★★

        Koda suka shigo gidan Maman Sakina batako leƙoba balle ta tambayesu yaya jikin Zinneerah ɗin tunda batabisu asibitinba. Duk da kuwa sanda Matar Nasiru tazo ta sanar musu ruɗewar jikin Zinneerah ɗin itama tana zaune a tsakar gidan. Amma taƙi bin Maman Sadiq. Bayan tafiyarta kuma bata kira waya taji halin da ake cikiba. Gashi yanzu sun dawo bataleƙo tajinba kuma.
      Hakan bai dami Maman Sadiq ba. Dan halin da take ciki ya wuce na matsalar Saude a yanzun. Tana shiga ɗaki fashewa tai da kuka, kamar Alhaji yasan za'ai haka ya biyo bayanta kuwa. Ganinta tsaye gaban mirror kanta a ƙasa tana shashshekar kuka ya sashi ƙarasowa cikin ɗakin sosai.
       “Haba Hauwa'u, minene kuma abin kuka anan dan ALLAH? Kenan bazaki iya karɓar ƙaddaraba? Ki tuna UBANGIJI ya fimu sanin abinda ke a ɓoye. Sannan yarinyar-nan mutane da yawa sun shaideta akan ba yarinyar banza bace. Kowa na ƙyautata mata zaton cewar tsautsayine kawai da ƙaddara da babu wanda ya isa kankaresu a rayuwarta. A ganina yanzu kamata yayi mu sake nutsuwa da janta a jiki wajen samun gaskiyar zance game da samuwar cikin, dan a yanda na fahimci zantukan jama'a a inda taje kwana da kwanaki ba'a saniba acan koma minene ya faru. Ina son ki kwantar da hankalinki ki karɓi komai a mashayin ƙaddara da jarabawa. Karki bari yarinyarnan ko wani a gidan nan yasan gaskiyar zance gameda yaron nan saboda gudun matsala, kokuma ita mu sakata  a wani halin da har zata iya tunanin sake sulalewa ta gudu daga nan kamar yanda ta baro can”.
     Cike da gamsuwa da bayanin mijin nata ta share hawayenta. “Nagode Yaya, nagode sosai da rufa asirina dana yarinyarnan. Lallai kaiɗin masoyine na gaskiya abin alfaharin kowacce mace. Insha ALLAH zanyi kamar yanda kace, sai dai ka tayani addu'ar jurewa wannan al'amari”.
       “Insha ALLAHU zan tayaki Hauwa'u. kema kuma kisa a ranki zaki iya ɗaukar komai kamar yanda kika ɗauki na baya da suka shuɗe. Kuma in ALLAH ya yarda inhar yarinyar nan bata da hakki duk inda uban yaron nan yake sai ya bayyana kansa watarana. ALLAH kuma zai wanketa ga idon kowa da izininsa”.
      “ALLAH ya tabbatar da hakan Yaya”.
      “Amin” ya amsa yana juyawa ya fita. Itama saita sake share hawayen da ke sake zubo mata. Zuwa tai ta leƙa yaranta taga harsun kwanta. Dama tasan Sadiq akwai ƙoƙarin kulawa kamar yanda ta horesa. Ɗan gyara musu abinda baiyiba tayi ta fito. Bayan tayi wanka itam ta kimtsa zuwa ɗakin maigidan dan girkintane.
     Sosai ya sake mata nasiha da tausarta akan komai, ya kuma sakata sukai salla da mikama UBANGIJI kukansu da bukatunsu. Sai gashi Alhmdllh ta wayi gari zuciyarta sakayau. Harma da jin zumuɗin komawa a sibitin taga halin da ƴarta ke ciki da baƙon duniya da baisan wanene shi ba.

       A asibiti kam da daddare ansha rikici, dan ɗan jinjiri dai kuka ya dinga tsula musu na yunwa gabannin asuba. Haka dai Maman Halima taita ƙoƙarin bashi ruwan zam-zam da aka haɗa da zuma a ciki. Zinneerah kam tanata faman barci batare da tasan wace wainar ake toyawaba.
       Koda suka tashi aɗan barcin daya figesu bayan lafawa da kukan jaririn sai maman Halima ta samu sun makara. Lallaɓawa tayi domin gabatar da alwala. Tana kabbara salla tamkar jira yake ya fara raira kukansa da muryarsa dake cauy-cauy masha ALLAH.
      Sosai maman halima ta rikice, tana a raka'ar ƙarshe taji shigowar mutum cikin ɗakin, ba'ayi maganaba dai, sai wani irin ƙamshin turare mai shegen daɗi daya gauraye ko ina na ɗakin. Tana ƙoƙarin sallamewa taji an fice da jaririn da har yanzu kukan yakeyi. Saurin sallamewa tai ta miƙe zaram ta biyo bayansu. Wayam babu kowa a wajen, sannan babu kukan yaron kuma. Hankalintane yay masifar tashi sanin duniyarnan fa babu gaskiya a cikinta. A cikin matuƙar ruɗani ta shiga leƙe-leƙe na neman inda aka nufa da yaron..............✍

       *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.
Chapter 25 · 0% Book details