← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 155

Sashe 149

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Daga ranar Zinneerah bata sake masa zancen Farah ba har ALLAH yasa sukai arba'in. A randa tai arba'in ɗin kuma su Mammah ke shirin tafiya katsina duba su Farah daga can su wuce london.
         Gaba ɗaya Zinneerah sai ta shiga damuwa. Dan zamansu a gidan ba ƙaramar shaƙuwace ta shiga tsakaninsu ba. Ganin shine zai kaisu katsinar ta sake daurewar masa zancen dawowar Farah sai ya balbaleta da faɗa, duk da tasan bayason wargi bata taɓa ganin fushinsa irin yau ba. Ita kuma yanda yake mata ihu akai yasata fara kuka.
      Suna haka Mammah ta shigo falon. Saurin share hawaye Zinneerah tayi tana ƙaƙaro murmushi da yima Mammah ɗin dake binsu da kallo sannu. Daga haka ta zame ta gudu ta barsu, dan tasan tunda Mammah din ta shigo nan da kanta magana zatayi da shi.
      Da kallo tabi Zinneerah harta fice kafin ta maida ga AK dake ta wani bata fuska. “Abdul-Mutallab mi kaima yarinyarnan?”.
       Guntun tsaki yaja yana murza goshinsa. “Mizan mata kuwa Mammah, itace da neman fitina kawai”.
     Shiru Mammah tai tana kallonsa cike da nazari, sai kuma taɗan girgiza kanta da cewa, “Fitina kamar ya? Ai kowa Yasan Zinneerah bata da kwaramniya, dan nidai a zamanmu gidan nan banga wani abun ashsha daga garetaba sai dai ajizanci irin na ɗan adama kawai. Amma yarinya mai kawaici da kunya ga haƙuri. Sai dai idan kai ne da laifin tunda sarai na san halinka bawai baƙona bane. Miya haɗaku?”..
         “Nifa Mammah babu abinda nai mata. Kawai ta isheni da zancen Farah ne”.
      Kallonsa kawai Mammah keyi dan maganar yanayintane da faɗa sosai. Ta sauke numfashi da gyara zamanta. “Abdul-Mutallab nasan Farah mai laifine tabbas, amma karka manta harda gudunmawarmu, kuma maganarta da yarinyarnan take maka tasan kantane. Dan wannan haline irin na mutanen ƙwarai da sake tabbatar maka ita mai tarbiyyace da hangen nesa. Ni bazance dole ka dawo da Farah gidankaba, amma zan baka shawarar ka daina ƙuntata yarinyarnan akan abinda ba laifinta bane saima alkairi da takeson ɗoraka akai. Ita rayuwa komai ɗan haƙuri ne ai. idan akai haƙurin sai komai ya zama labari wataran”.
       Shi dai kansa na ƙasa baice mata komaiba harta gama zancen Farah da Zinneerah ta ɗakko abinda ya shafesu sannan ya tsoma baki.

    Duk da Zinneerah tasan su Mahma basu rasa komai na rayuwaba sai da ta shirya musu tsaraba domin girmamawa. Musamman turarurrukan khumrah dana wuta da a koda yaushe suke yaba kamshin a jikinta da gidanta. Hakan yasa tasa Hajiya Falmata ta haɗa musu na musamman akai musu packaging nashi.
    Sai gata harda ƙwalla da zasu wuce. Bama ita ba hatta su Yaya Gajeje sunji babu daɗi. Inna ma da take ɗan magana yanzu kuma takan ɗan motsa jikinta tafiyace dai batayi sai da ta nuna alhinin tafiyar tasu, dan kullum sai sun shiga sun gaidata sau uku a rana babu fashi.
       Duk yanda Zinneerah ke share hawaye AK na kallonta ta mirror. Yay ɗan murmushi yana cizar lip ɗinsa dan yau kam yasan ango yake tunda Mahma ta ɗaure mata ƙugu sai da tai arba'in duk da ba haihuwa tayi da kanta ba.
      Baisan Mahma ta masa wayo bane tanata gyare masa Zinneerah ɗin a ɓoye. Ga gyaran Hajiya Falmata datake ɗorata a layi, hakama Hajiya Iya kullum cikin faɗa mata dabaru takeyi. Ita kanta tasan idan taje hannun boss din nata sai ta yabama aya zaƙinta. Shiyyasa yau duk take a tsure.

   Kasancewar da little ya tafi suna wucewa mai ƙunshin da zatai mata tana isowa. Ƙunshi akai mata na gani na faɗa na jan lalle da baƙi, Yaya Karima ta yarfa mata kitso kananu da ya fiddo mata ƙyawunta sosai musamman yanzu data yi wani bulɓul da ita tamkar ba itace tasha fama da rama lokacin cikin ƴan biyu ba.
        Kasancewar basu zauna wasaba kamar wasa kafin la'asar suka kammala komai tai fes da ita. Dama tunda ta fara zaman jegon nan take dilke jikinta da kayan gyaran fata na musamman da Hajiya Falmata ta haɗa mata ga kuma na Mahma. A gurguje ta shiga gyaran sashe. AK duk da bawani ƙura yayi ba. Sai da ta tsaftace komai yay mata yanda takeso ta baje kalolin ƙamshinta masu rikitashi. Sanda ta dawo sashenta ma su Mama A'i sun gyare ko ina sai ƙamshi yake.
       Waya tai zamanyi da AK ɗin taji kosun taho. amma yace mata yana dai shirin tahowar. Taji daɗin haka dan ta samu damar shiga kitchen kenan ta haɗa abinci da kanta. Dan tunda ta fara zaman jegon nan kullum cikin ƙorafi yake akan abinci, idan kaji baiyi maganaba Mahma ce tai girki da kanta saboda shi.
     Lafiyayyen abinci ta shirya masa da tasan zai gamsar dashi. Tare da haɗaɗen shayin barnawa daga Hajiya Falmata da kalolin kayan sha na zoɓo da kunun aya. Suna kammalawa dan da taimakon Mama A'i tayi ta bar mata idawa bayan ta ɗiba na AK takai sashensa.
      Wanka takeson shiga Amaan ya wani saka kuka shi a dole yunwa yakeji. Ɗaukarsa tai tana dungurinsa da kiransa acici like Daddynsa. Tana gama bashi a tsaitsaye itama Anam ta saka tata rigimar. Kanta ta dafe da amsarta Yaya Gajeje na dariya. “Wai yaran nan mi kuke son maidani ne halan? Ku gama naku shima yazo ya isheni da tasa rigimar”.
        “Ai daidai kenan”. Cewar Yaya Gajeje tana dariya. Murmushin jin kunya Zinneerah tayi da ajiye Anam din ta shige cikin dan watsa ruwa...........✍

*_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.

*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*

*_TYPING📲_*

*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*

_______________________

*Page 68*

..........Sai da Zinneerah ta fara gabatar da sallar magrib bayan fitowarta wanka sannan ta zauna ta tsara kwalliya ƴar gaske, tare da baje lungu da saƙo na jikinta da ƙamshin mayun turarurrukan ta sabbin haɗi daga Hajiya Falmata. Ta ɗakko less da yaji ɗinki mai ƙyau da tsari ta saka tare da kashe kan ɗauri. Awarwaraye da sarƙa ta zuba kai kace wani biki zata. Ta sake ɗorawa da wasu turarurrukan sannan tai zaman sallar isha'i. ALLAH ya sota ƴan biyu suna goye a bayan Yaya Gajeje da Mama A'i.
       Sauri-sauri ta kammala ganin har isha'i su AK basu shigoba. Koda ta fito su Yaya Gajeje wani ihun dariya suka ɗauka da yaba wannan wanka nata. Kunya tasata jan mayafi ya rufe fuskarta.
      Mama A'i da yake itama a ce, babu yawan magana sai lalata tace, “A'a wannan gayun bai kamata ki kaisa turaka ke kaɗai ba. Bara na ɗakkoma su Alhaji ƙarami kaya a canja musu suma dasu za'a”.
       “Wannan zance nakan hanaya Mma A'i”. Yaya Karima ta faɗa tana dariya. Zinneerah ta tura baki kaɗan tana faɗin, “Gaskiya nai dai a'a, salon su batamin gayu”.
      “Iyee, lallai Zinni binni ta buɗe miki ido da baki, a gabana babu kunya”. Cewar Yaya gajeje tana riƙe haɓa.
     Dariya Zinneerah ta shiga kwasa. Ta faɗa ɗaki tanayi da faɗin, “Yi haƙuri Yaya gajeje na tuba”.
   Suma dai dariyar suke tayata harta ɗakko kayan da za'a canjama ƴan biyu. Su Mama A'i suka shiryasu tsaf sannan Zinneerah ta kwashesu. Dan Yaya Gajeje korata tai wai ta tafi can yazo ya sameta zaifi jin dadi. Su Yaya Gajeje tsoffin masoyane da sukasan takan maza da muhimmancin irin wannan ranar. Aiko shawararsu Zinneerah ta bi. Dan dama itama akwai nata shirin a ƙasa.

          AK bai shigo gidan ba sai wajen tara da rabi na dare. A gajiye yake matuƙa. Dan haka kai tsaye ya nufi sashem Zinneerah ɗauke da little dayay barci. A falon farko ya samesu dan sunfi zama nan, kai shi baima taɓa samunsu a falon ciki ba dan daga shi sai Zinneerah ɗin ke shigarsa da bedroom dinta na ciki, saiko little.
     Mama A'i ta mike tana amsar little ɗin da masa sannu da zuwa. Suma su Yaya Gajeje sannun suke masa. Cike da mutuntawa yake amsa su yana baza idon ganin ta inda Zinneerah zata ɓullo da twins nashi. Ganin dai babu alamarta ya sashi leƙa Inna sannan ya fice.
    Gulmarsa su Yaya Karima suka shigayi suna dariya. Dan yanda yaketa kalle-kalle sunsan matarsa yake son gani, gashi su kuma sun yi gum bama su nuna sun fahimcesaba.
Chapter 149 · 0% Book details