← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 155

Sashe 150

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

     Shiko harya ɗan shaƙa dan ya zata abinda ya faru tsakaninsu ɗazun da safe ne ya sata fushi. Sai da ya shigo sashensa ya shaki wani mayataccen ƙamshi daya nema karar masa da man kai lokaci ɗaya sannan ya sauke ajiyar zuciya. Taku yake tamkar mara laka a jiki yana bin falon data sakama hasken wuta kaɗan da kallo. Bukatar fara wanka ta sashi nufar bedroom ɗinsa ransa fal waswasin ina ta shiga.
      A bedroom ɗinma ƙamshin da yafi na falo ɗaga masa hankali ya shaƙa. Kasancewar wutar ɗakin a kashe dindim ta sashi fara lalauben makunnar fitilar. Ɗan zabura baya yayi lokacin da haske ya gauraye ko ina a ɗakin. Kyawawan idanunsa kuma sukai masa gani na musamman daya sakashi hangame baki. Zinneerah ce zaune a tsakkiyar gadon lulluɓe tamkar sabuwar amaryar da aka kawo ɗakin miji yau. gefe da gefenta Amaan da Anam ne cikin showals suna barcinsu hankali kwance suma cikin gayu.
      Jiyay gaba ɗaya yana neman daburcewa da salon nata. Ya shiga takawa a hankali zuwa gaban gadon jininsa na tsinkewa tamkar manjan da yaji zafin wuta.
          الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .
*_Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat._*
      _Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda saboda ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika._
اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ.
*_Alhamdu lillahi ala kulli halin_*
     _Godiya ta tabbata ga ALLAH a cikin kowane hali._
       Ya faɗa lokacin da yake kaiwa zaune bakin gadon. “Dan ALLAH ki zauna a haka karki motsa harna fito a wanka, dan wannan sirrin ya wuce na gani da ido kawai ko fatar baki”.
     Zinneerah da duk take jinsa tai murmushi batare datayi ko tari ba balle ta motsa. Bai damuba shima dan mikewa kawai yay ya nufi toilet.
      A yanda ya barta ɗin kuwa haka yazo ya sameta. Tsane jikinsa yake amma ya kasa daina kallonta ita da yaran daga inda yake. Turarurruka ya cuɗe jikinsa da shi da ɗaukar wando fari ƙal iya cinya ya saka da ƙaramar riga armless ya haura gadon
    Zama yay a gabanta ya tanƙwashe kafafunsa suna fuskantar juna. Yasa hannayensa biyu ya kamo bakin mayafinta ya ɗaga sama ƙyaƙyƙyawan fuskarta na bayyana garesa tana neman zautashi da wani sassanyan murmushi.
     Da ƙyar ya iya fisgar numfashin dake neman ƙwace masa yana wani mar-mar da idanunsa dake neman zubowa jikinta. Luuu ta ɗanyi da idanun tasa tafukan hannunta ta rufe fuskarta. Hakan da tai ya bashi damar yin tozali da ƙyaƙyƙyawan ƙunshinta.
        “My Neerat zaki halakani wlhy”. Ya faɗa a wani irin sassanyan sauti da ita kanta sai da tsigar jikinta ta tashi. Hannayensa duka ya ɗaura akan nata yana janyewa daga fuskarta. Cikin idanunta ya zuba birkitattun nasa yana faɗin, “Ina ƙaunarki da yawan yawa My Neerat, zaki zautan ɗan Shira da salonki”.
         Zinneerah dake amsar saƙwanninsa ta cikin idanunsa itama da wata irin muryar da batasan tanada shi bace, “أَحَبَّكَ الَّذِي أَحْبَبْتَنِي لَهُ.
   *_Ahabbakal lazi ahbabtani lahu._*
_Wanda ka so ni saboda Shi, kai ma Ya so ka Yayanmu. Kuma nima ina ƙaunarka”_.
        Gaba dayanta ya cacumo jikinsa ya rungumeta tamkar zai cusata a fata da ɓargon jikin nasa gaba ɗaya. Cikin fisgar numfashi ya shiga laluben bakinta ya manne a cikin nashi jikinsa na wani irin tsuma na zalamar son kasancewa da ita. Bata iya ta hanashi ba. Sai ma haɗin kai data shiga bashi.
    Sai da labarin ya nema yin nisa kuma tsoro ya kamata, dan gasu Anam a gadon karsu taushesu. cikin taimakon da ALLAH yay mata sai Amaan ya farka da kuka. Da ƙyar AK ya iya sakinta yana cizar lip. Itama ta mike da ƙyar daga jikinsa dan tunaninta kar hayesa sukai. Ganin babu abinda ya samesa ya sakata sauke ajiyar zuciya da hararsa. “Ɗan ɗagwai na zatama hayeka akai”.
       Idanu Ak ya buɗe da ƙyar yana duban inda Amaan ɗin yake. Kafin ya yunƙura da ƙyar ya matsa garesa yana dungure masa kai. “Haka kawai ka ɓatamin wasa. Shiyyasama bana Baffan da kai yaro”.
    Murmushi Zinneerah dake kallonsu tayi, ta sauka ƙasa gaba ɗaya tana kai hannu ta ɗaukesa dan tasan yunwa yakeji. Komawa AK yayi ya kwanta dan cikinsa ya ƙulle tamau. Har Zinneerah ta gama shayar da Amaan ta maidashi ta kwantar sannan ta dubesa.
     “Yayanmu ga abinci fa a falo kar dare ya ƙara zurfi”.
    Lumsassun idanunsa ya buɗe a kanta. Akan laɓɓansa da ƙyar ya furta, “Ke kaɗai kin wadatar dani”.
    Dariya zancen nasa ya bata dan tasan dai shi da abinci sai ta ALLAH. Ta miƙe tana fadin, “Nidai daka daure kaci bara na kai su Anam ai musu shirin barci. Uffan bai iya ce mataba harta fice a ɗakin. Bai kuma iya motsawa ba yana a inda ta barsa har kusan mintuna talatin sai gata ta shigo ɗauke da tea. Ajiye masa tai tana faɗin, “Ga tea nanto Yayanmu bara na ɗakkosu.”
    Bai motsaba bai kumayi magana ba harta sake ficewa yanzu ma. Bata jimaba yanzu ta dawo ɗauke da ɗan gadon su Amaan. Ta ajiye ta koma falonsa inda Mama A'i ta rakota da yaran ta amso su sannan tai mata sai da safe dan tama su Yaya Karima sallama.

       Jin ta dawo tana kwantar dasu ya sashi miƙewa da ƙyar zaune. Kofin tea ɗin ya ɗauka ya hau sha dan da gaske yanajin yunwar ma. Sai dai duk inda tai yana binta da kallo harta gama hidimar yaran tai musu addu'a. Dan ma sanye take da zumbulelen hijjabi a saman kayan barcinta.
    Sai da ya kammala yaje yay brush itama taje tayo dan ta kimtso kanta daga can, alwala kawai tayo da brush ɗin ta fito. Tsugunne gaban gadon su Anam ta samesa yana musu addu'a fuskarsa ɗauke da murmushi yana faman shafa kawunan yaran. Ta zare hijjab ɗin nata tana nufar falo ɗakko ruwa duk da ta tabbatar sai yaci abincin nan ko zuwa anjima ne.
    Da kallo ya bita harta fice. Ya sauke ajiyar zuciya yana mikewa daga wajen su Amaan ɗin.
    Tsaye ta samesa gaban mirror yana saka turare. Tana ajiye ruwan ta juyo da nufin masa magana taji anyi cak da ita sai gado. A tare ya faɗa da su yana magana cikin kuneneta. “Wai sokike dai sai na miki kuka yarinyarnan. Sai wani ƙwalele kikemin ni da kayana”.
    Siririyar dariyar data nema zautashi ta saki tana cusa kanta a wuyansa da shaƙar ƙamshinsa itama. Babu shiri ya lalubo bakinta dake ƙamshin strawberry freshener ya manna nasa a ciki. A zalame yake, dan haka cikin zalamar ya shiga sarrafata shima, itama kuma tana amsarsa da zalamar dan koba komai tayi kewa.
     Sai da tafiya tai nisa sosai ta gama shagala a hannunsa da salonsa sai ga idon madam ya raina fata ta koma raki daga karshe. Inama AK ke wani jinta shi a wannan yanayin. Sai da ya more duk ƙwalelen kwanakin da akai masa shima sannan ya koma lallashi yana mata dariyan mugunta.
    Kamar yanda tai hasashe kuwa suna kimtsa jikinsu sai da yaci abinci waishi duk ta sakashi jin yunwa. Murmushi kawai ta dingayi dan dai al'amarin nasa yakanfi ƙarfinta wani lokacin, babu abinda ya damesa ɓaro mata zance yake kansa tsaye kamar ba yayansun nan sarkin mazurai da tsare gida ba. A yanzu haka idan su Jamal na tsogumi akansa sai taita dariya kawai dan tasan dai mazuran iya na waje ne. Itama dai sai da tacin danya tsiyayeta tas ga yaransa a gefe da nasu suma.
Chapter 150 · 0% Book details