← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 155

Sashe 95

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tayi zurfi a tunani sosai Hajiya iya ta shigo, harta zauna Zinneerah batasan da zuwantaba, sai da ta gama mata kallon nazari tsaf sannan ta taɓata. Nufashi Zinneerah ta kawo a zabure, sai dai ganin hajiya iya ya sakata sauke ajiyar zuciya da ɗan ƙaƙaro murmushi. “Granny ashe kin shigo? Bara na ɗauka miki maganinki kisha”. Tai maganar tana ƙoƙarin tashi. Kamo hannunta Granny tayi ta maida ta ta zaunar. Hakan yasa Zinneerah ɗan kallonta. Amma ganin itama kallonta Granny keyi saita maida kanta ƙasa dan kallon ya banbanta da wanda ta sani. “Kamannin Abdul-Mutallab da Moddibo na ruɗaki ko? Muma haka suke ruɗamu a koda yaushe. Sai dai nasan jinine kawai yasa Hauwa'u haifo mai kama da Moddibo”. Ɗan murmushin yaƙe kawai Zinneerah tayi kanta a ƙasa har yanzu, Hajiya iya taci gaba da magana batare da ta damu da yanayin Zinneerah ɗin ba. “Ki shirya zuwa anjima da yamma hajiya Zulai zatazo ku wuce katsina akwai wani aike da zaku kaimin amma ke da ita kawai zakuje”. Saurin ɗagowa Zinneerah tai ta kalli Hajiya iyan a karo na farko, dan itafa tama kanta alƙawarin bazata ƙara taka ƙafarta katsina ba saboda tsoron karsu Hajiya su ganta. Duk da a yanzu tafi ƙarfin a ƙara kaita inda aka kaitan, kuma tasan ba gidan yankan kai baneba kamar yanda ƙuruciya ta sata kiran wajen a baya. Cike da basarwa Hajiya iya tai ɗan dariya, “Oh wai kokin taɓa zuwa Katsina ne Inno?”. Murya a raunane Zinneerah tace, “Sau ɗaya Granny”. “Kai, duk da kasancewarki bakatsina? A to karma ki faɗa gaban su Jamal sumiki dariyar Danya kawai kika sani”. Ƴar dariya tayi saboda yanda hajiya iya tai maganar cike da raha. Batare da tunanin komaiba tace, “Granny ai shima aiki Inna tasa wata mata taje dani nayi bama yawo naje ba”. “Aiki kuma? Kina nufin aikatau fa kenan?”. A take damuwa ta bayyana akan fuskar Zinneerah, ƙwalla suka ciko mata idanu, murya a raunane tace, “Eh aikatau Granny, ni bansan miyasa Inna bata sonaba. Dagafa wata ƙawarta tazo ta bata labarin kuɗin da ake samu shikenan tasa na bita ko baba bai saniba. Amma tsabar sharri dana dawo sai tace wai yawon banza naje, wlhy kuma ba yawo najeba”. “Toke miyasa baki faɗama Babanki gaskiyar abinda ya faruba?”. “Haka kawai naji inajin tsoro Granny, koma nayi niyyar faɗa masa saina kasa dan Baba tsoron Inna yakeji saboda masifarta wlhy, bama shi kaɗaiba ƴan garinmu da yawa tsoronta sukeji dan jarababbiyace sosai”. “Kai wannan mata ALLAH ya wadaran halinta, ina daɗi ace miji na tsoronka. To amma ke miya faru har tasa aka tafi dake aikatau babu wanda ya sani, harma ta samu damar miki sharri kinje yawo?”. Hannu Zinneerah tasa ta share hawayenta daketa sakkowa saboda tuna a yanda tabar Danya wancan lokacin, babu wani tunanin wayon manya Hajiya iya ke mata ta fara zayyana mata yanda abin ya kasance. “Hajja lanti ƙawar inna ce sosai, dan nidai tare na sansu tunda na fara wayo, dan Hajja Lanti dillaliyace a garinmu, tana kuma saida abubuwa iri-iri. Daga baya kuma ta koma ɗaukar yara tana kaiwa aikatau a birni. Hajja lanti ba sona takeba itama, shiyyasa bana murna da zuwanta gidanmu, dan duk randa tazo da wahala kaga harta tafi Inna bata dakeniba saboda tsaban iya haɗa gulmanta. A wata ranar asabar na dawo daga tallan gyaɗa da riɗi a gajiye na iskesu zaune a tsakar gidanmu suna magana da ban san kota micece ba. Ni dai na gaidasu na bama Inna kuɗin tallar na shige ɗaki dan tace karna sake zama a tsakar gida idan tayi baƙi. Ban jima da shiga ba ta ƙwalamin kira. Koda na fito sai da suka gama min kallo na wani lokaci ne naji hajja Lantin na cewa “Ai wannan ma itace dai-dai a yanzu. Dan za'a jima ana samu tattare da ita”. Bansan ina zancen nasu ya dosaba. Ni dai Inna tacemin naje na canja kaya nawuce can bakin ɗorawar kan hanya na jira Hajja Lanti zamuje anguwa. Ban musa mataba naje na canja kayana na fito, saita sake korani da cewar naje na saka kayan sallata. Zuwa nai na sake canjo kayan na fito, a gabansu na tafi inda tace naje na jira hajja Lanti ɗin. Na jima a bakin ɗorawa zaune sannan hajja lanti tazo ita da wasu yara da ban sansu ba. Batare da itama tamin bayaniba ta bani hijjabi da nikab wai na saka. Nidai ban musa mataba na saka. bayan na sakane ta kira masu mashin su uku suka daukemu zuwa Gozarki. A Gozarki muka kwana dan maraice ya rufa lokacin. Washe gari tunda farar safiya muka tafi inda ake hawa mota muka shiga motar Katsina da naji ana faɗi a wajen. Nasha mamaki amma a raina ina ɗoki zanje katsina da nakeji a labari. Koda muka isa Katsina an saukemu a wani waje mai tarin jama'a, mudai muka shiɗa a motar kamar yanda tace mana. Daga nan an ɗibemu a napep zuwa wani waje da naji hajja Lanti ta kira da suna anguwar yari. Kamar yanda ƴan uwan tafiyata basa gane komai a wannan tafiya nima dai ba ganewa nakeba. Sai dai ina lure da komai da akeyi. Kamar sunayen wajajen da muka sauka da inda muke tafiya. Mun isa anguwar yari da tace a kaimu. Inda aka saukemu a wani gida mai matsakaicin ƙyau da girma. Koda muka shiga cikin gidan mun samu kusan mutane goma a cikinsa, Sai wata dattijuwar mata da tafi hajja Lanti shekaru dajin daɗi. Yanda ta tarbemu ne yasa naji ɗan dadi ga raina. Sai dai yanda maza da mata ke shiga da fita gidan baiminba a rai. Mun jima zaune suna hira kafin a kawo mana abinci muci, bayan mun koshi aka haɗamu da wata a gidan mai suna Sadiya. Itace ta kaimu wani ɗaki wai anan zamu zauna. Nidai kallon kowa nake da mamaki da tunanin mi mukazoyi nan? Miyasa Inna tace na biyo wannan matar nan batare da Baba ma ya sani ba?. Banda mai bani amsa, shiyyasa naja bakina na tsuke. Daga wannan lokaci ban sake ganin hajja Lanti ba a gidan, ban kawo komai a rainaba sai tunanin ko taje wani wajene ta dawo tazo mu dawo gida. Amma sai naji shiru har tsayin kwana biyu. Duk da ana bamu abinci muci mu ƙoshi, ga television muna kallo hakan baisa hankalina ya kwantaba, sai dai inajin tsoron na tambayi wani ina hajja Lanti take?. A randa muka cika kwanaki uku a gidan naga an kwashi abokan tafiyata su uku aka fita dasu a gidan, daga haka ban sake ganinsuba suma. Hankalina ya tashi na shiga yi musu kuka akan nidai su maidani garinmu, danni na ɗauka kodai ƴan yankan kai ne ma. Ranar naga ruwan masifa wajen matar nan, dan kamar zata dakani a turmi saboda masufar data dinga min. Dolena shanye kukana saboda tsoronta. Da maraice aka sake kwashe sauran abokan tafiyata su biyu da suka rage aka barni ni kaɗai sai waɗanda na samu a gidan. Ranarma nayi kuka har takaini gayin masassara. Magani kawai suka bani nasha, daga haka babu wanda ya sake bi takaina, sai ma da daddare kusan ƙarfe takwas hajiyar tace a tasoni zamu fita. Ina jinta daga ɗaki danba barci nakeba, tunanin asibiti zata kaini yasa ban kawo komai a rainaba na tashi na fito bayan na saka hijjab ɗina. Tsaye na sameta a tsakar gida cikin gayu, na gaisheta jikina duk a sanyaye saboda zazzaɓi dake cina. Gaba tai na bita baya batare damin maganaba. Muna fitowa ƙofar gida muka iske mota mai ƙyau. Motarnan muka shiga, gabana nata faɗuwa nidai inata tunanin lokacin yanke nawa kan yayi. Dan haka naita addu'a kala-kala ina sharar hawaye a ɓoye da roƙon gafarar babana a zuciya, a haka muka iso wata babbar anguwa dabansan sunantaba, sai dai yanda ko'ina ke ƙwanyar da hasken lantarki zai tabbatar maka da anguwar masu kuɗice. Katafaren gida mai blue gate aka buɗe mana muka shiga, kasancewar darene bazan iya banbance tsarin gidanba, sai dai lallai ya haɗu matuƙa. Koda muka fito a motar hajiya ce ta kama hannuna muka shiga ciki. Anan ne na sake tabbatar da gidan ya haɗu, masu shi kuma sunada kuɗi. Waɗanda muka samu a falon ne sukai mana iso zuwa ciki bayan mun gaisa, an sake kaimu wani falon, inda muka zauna zaman jiran matar gidan. Munfi ƙarfin awa ɗaya zaune kafin ta fito, ƙyaƙyƙyawa ce sosai baƙa, daka ganta kaga bafulatanar bakatsiniya, dan ƙyawun nata ya fita sosai masha ALLAH. Sai da ta gama mana kallon tsaf kafin ta amsa mana gaisuwa tana sake ƙaremin kallo, cikin maganar daban ganeba hajiya tace, “Ranki ya daɗe ga wata ki duba ko zata iya, yau kwana uku da kawomin su daga wani ƙauye”. Kallona ta sakeyi sama da ƙasa tana ɗan yamutsa fusaka. Ta ɗage kafaɗunta cike da isa tana faɗin, “Uhm babu laifi kam, dan tafi waccan komai, girma kawai waccan zata fita. Amma ina zuwa”. Tai maganar tana miƙewa, fita tai, babu jimawa sai gata ta dawo ɗauke da waya, batare da tayimana maganaba ta shiga haskani da hasken wayarta daban fahimci ma'anarsaba a wancan karon, sai dai a yanzu inaji a raina camara ne. Bayan ta gama kuma ta fara waya, da turanci take magana shiyyasa banji komaiba, bansan dai ga hajiya ba. Ta ɗauki lokaci mai tsaho tanayi kafin ta ajiye ta dubi hajiyar, “Ba damuwa zamu gwada mu gani, bara na ɗakko miki sauran saƙonki ko, idan akwai wani matsala zan nemiki daga baya kafin ki wuce, namafison sai mun kammala komai mun fara wucewa kafin taki tafiya”. Baki a washe Hajiya tace, “Ato babu damuwa ranki ya daɗe, ni bani da matsala duk yanda kukeso sai ayi, fatana dai ALLAH yasa a dace akumayi nasara”. Cike da yanga ta amsa da amin. Daga haka taje ta kawo mata saƙon da tace. Inaji ina gani hajiya ta miƙe tana faɗamin aini nan zata barni, nanne zanyi nawa aikin, dan haka sai nayi biyayya, yi nayi bari na bari. Sosai na fara hawayen fili saɓanin na zuci, yanda zuciyata kemin zugi da zafi ya hanani yin magana harta fice ta tafi bayan ta bani ɗari biyar a kuɗin danaga an bata masu yawa, itama haijiyar gidan ta
Chapter 95 · 0% Book details