← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 155

Sashe 138

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

yawa yarinya ƙarama ta ɗana boom ɗin da a ƙarshe yake neman tashi da ita? Tayaya idonta ya rufe haka da yawa ne akan abinda yana a hannunta amma gashi sakacinta ya ta miƙashi ga mai shi?....... Cikin ƙunar Zuciya AK ya katse tunanin kowannensu ta hanyar faɗin, “Shima cikin da take dashi yanzu na ƙaryane kenan? Randa mukaje asibiti da nufin sake duba lafiyata kune kuka ƙulla?.” Kasa magana Farah da Zakiyya sukayi. sai Mammah ce cikin kuka tace, “Kayi haƙuri Abdul-Mutallab, tabbas wannan duk laifinane, da ace ban bata goyen bayaba babu yanda za'ai hakan ta kasance. Nayi nadamar saninki Zakiyya, wannan wane irin haline haka da kika nema jefamu a ciki. Har takai na saka hannu wajen cutama gudan jinina ta hanyar makircinki”. “Dama shi son zuciya ai ɓacin zuciya ne, daga lokacin da kake ganin wayonka ko dabararka zai baka abu to lallai a lokacin ka ɗaura ɗammara da ɗambar rasashi, dan koka samu sai ya suɓuce maka. Kin biyema yara ƙanana saboda wani shirmen banza da wofi Hindatu, yanzu da ALLAH bai ƙaddara yarinyarnan ta faɗo cikinmu ba yaya kenan? Duk da dai sanda sukayi na farko basu sanar miki ba, amma na biyun da'an haifesa fa? Shikam kinada kamasho a ciki ai”. Uncle Ahmad ne ke magana cikin ƙunar zuciya. Kauda kai AK yayi yana rumtse idanunsa saboda zafi da ƙirjinsa ke masa. ga kansa sai juya masa yakeyi alamar hawan jininsa na neman motsawa. Cikin harɗewar harshe yace, “Uncle idan wancan ya salwanta aiga waninan ma sun sake dasawa. Tunda sunce tanada ciki kuma likitoci sun tabbatarmin babu wani ciki tare da Farah”. Yanzu kam duk yanda mai martaba da mukarrabansa sukaso daurewa sun ƙasa. Cikin kaushin murya yace, “ALLAH zai sakamin ɓatamin suna da kukayi. musamman ke Zakiyya dan kece kika ƙulla komai, kece kika ɗora ƴar uwarki akan abinda sam babu shi a ranta, ni yanzu bamma san mizance mukuba wlhy, dan yanda nakejin raina zanma iya tsine muku. Amma inason sanin gaskiyar zancen shi cikin da akace tana dashi yanzu, dan nikam kotun musulinci zan kaiku a yanke muku hukunci dai-dai da laifinku”. Sosai Farah ta fashe da kuka. Ta rarrafo gaban mai martaba ta kama ƙafafunsa da fashewa da kuka. “Dan ALLAH Abba kayi haƙuri, nidai wlhy bazan sakeba, wannan ma kota haufa banaso zanyi haƙuri ALLAH ya bani nawa. Na tuba Abbah dan ALLAH na tuba”. Banza yay mata yama ɗauke kansa ya maida ga Zakiyya da itama kukan take. “Wai bada Zakiyya nake maganarnan ba?!” Zabura ta ɗanyi saboda yanda yay maganar a tsawace, ta shiga jinjina kanta da faɗin, “Abba hakane, shima dasawar akai, amma wannan ƴar Morocco ce, kuma da amincewarta itama wlhy”. Sake ɗaukar sallalamu falon yay gaba ɗaya, hajiya iya dake sharar ƙwalla tace, “Gaskiya baku ƙyautaba, wannan zaluncine wlhy dason zuciya. A barshima mutum shi ya yarda yay muku wannan aikin da sauƙi ai, amma kamar yarinyarnan aikun zalunceta. Inda ALLAH bai ƙaddara tamu bace kamar yanda Ahmad ya faɗa harta mutu baza'a daina mata kallon wannan tabon ba. Yaya zakuyi da alhakin wannan yarinyar kawai ma balle na sauran suma, sai dai idan da yardarsu kukayi sukam. Nikam dai ina bayan mahaifinku a kaiku kotun musulinci a bin kadin jikata na rainon cikin da tayi. kuma wlhy ko sama da ƙas zata haɗe ɗannan ya zama nata har gaban abada marasa mutunci”. A take su waziri suka shiga goyama hajiya iya baya, kowa na tofa albarkacin bakinsa. Mmn sadiq, Abba, baba sune dai basuce komaiba, sai dai duk sai da sukai ƙwallar tausayin Zinneerah harma da AK da little. Sai da ƙyar Baba ya fara magana ganin kowa ya yarda da zuwa kotin. “Ranka ya daɗe nikam kuyi haƙuri zance wani abu”. Duk hankalinsu suka maida garesa. Ya ɗan muskuta zamansa yana gyarama little dake a jikinsa kwanciya, dan shi yaune karon farko daya ga jikan nasa, “Kuyi haƙuri nasan tabbas basu ƙyautaba, kuma zaluncine abinda sukayi dan yarinyarnan taga rayuwa mai zafi kala-kala a dalilin cikin nan. To amma Alhmdllh ta wani gaɓar ya zamar mata alkairi. Dan a sanadin samunsa ta sadu da mahaifiyarta, ƙaddara ta ɗakkota ta kawota cikinku da har a yau ya zama sillar bayyanar komai, bugu da ƙari yay mata ƙyauta da miji uban ɗan kuma saboda hikimarsa. Sannan a sanadinsa nima kaina nabar gida harna samu waraka daga kaidin matata, na kuma ƙara aure a yanzu haka matata ta haifamin yara maza ƴan biyu guda biyu tun washe garin da suka koma gida. Waɗanan kaɗanne daga ni'imomin UBANGIJI gagara misali daya lulluɓe Zinneerah dasu a sanadin cikin yaron nan da batajiba bata ganiba. Tabbas duk mai haƙuri zai dafa dutse harma yasha romonsa. Su dai duk sun aikatane akan dalilai biyu zuwa uku. Mahaifiyarsa dalilinta kawai kar ya dawo hanun ubansa ne da rayuwa, sai kuma gashi ya dawo cikin sauƙi. Ita wannan yarinya saboda kar mijinta ya ƙara aure ne, kuma gashi ya ƙara ɗin harma suna zaune a inuwa ɗaya. Ita wannan ƴar uwa tata kar wata tazo ta haihu ba ƙanwartaba. Gashi kuma watan ta haihu ba kanwar tata ba. To idan mukai tsam a nazari zamu fahimci UBANGIJI ya bama kowa sakamako nan duniya dai-dai da shi da tabbatar musu cewar wayo ko dabarar bawa bata kaisa da nasara. duk saurinka kuma saika jirayi zartar da ƙaddarar UBANGIJI gamai ita. Tunda su duk sunyine a ɓoye domin bama kayinsu kariya akan abinda yake gaibu kuma dauɗar duniya amma daga ƙarshe gashi duk sun rasa, kuma wanda sokaso ƙwata daga wajensu ALLAH ya maido musu. A ganina kuma miya rage banda mu barma UBANGIJI ikonsa ya ƙarasa zartar da hukuncinsa. Basai anje kotuba, dan mu dukanmu ALLAH ya haɗamune a ƙarƙashin inuwar zumunci sai muyi haƙuri wajen haɗiye duk wani saɓani da zaizo a garemu duk da kuwa wannan ya banbanta ba abune mai saukiba. Amma idan mun sauƙaƙashi a ranmu sai ya zame mana alkairi kamar yanda ya zamewa Zinneerah. Sai dai kuma su sauran yarenne bamuda hurumi a kansu inhar suma tirsasu sukai ko yaudararsu. Abin na gaba shi annamimin likitan dake wannan aikin ya kamata a dakatar dashi, dan gwara ace ma'auratan dake buƙatar hakan da kansu suka amince suka kai kansu bawai ta irin wannan hanyar dabita wagga ɗiya Zakiyya tabi ba. Wannan al'amarima malamai sunata nasiha akansa. barinsa yafi alfanu fiye da yinsa. Dan UBANGIJI shine yasan miya gani har bai bakaba, zata iya yuwuwa rashin haihuwar sai yafi zame maka alkairi fiye da yinta. To mizai hana bazaka dogara ga UBANGIJIN talikai harya baka ba kuma?. Sai kuma ina roƙon alfarmar ku taimaka kuje can garinmu ku wanke wannan yarinya agaban al'ummarmu, dan inba hakaba harta mutu wannan tabon na biye da ita. Haka shima wannan yaron bazasu taɓa kallonsa da darajaba dan ɗan shege zasuke kallonsa bayan ba haka bane. Ayi haƙuri da juna ayi sulhu dan ALLAH shine mafi alkairi a garemu fiye da mu tonama kammu asiri kodan kasancewar ku manyan mutane danmu namu mai sauƙine iya garine kawai, idan yazu kuma mukace mun barsa zance ya ƙare. Kuko magauta sun sami abin faɗa a gareku kenan har takai shi yaron ana goranta masa duk da kuwa ba alfasha aka aikata wajan samuwarsa ba kai tsaye”. Harga ALLAH kowa maganar baba ta sanyaya masa ransa. Kuma kimarsa da darajarsa ta ƙaru a cikin idanunsu, hajiya iya ta shiga jera masa tagwayen addu'oi shi da zuri'arsa kowa na amsawa da amin. Sai da kowa ya natsa sannan mai martaba ya fara magana bayan yayi gyaran murya. “Ni a nawa hukuncin to Abdul-Mutallab da Sageer (mijin aunty Zakiyya) duk ku saki waɗanan marasa mutuncin, kowacce ta koma masarauta sai sunyi zaman shekaru bibbiyu kafin na barsu su dawo gareku idanma kuna sha'awa kenan, kokuma su sake auran wasu mazan suji, dan masu iya magana sunce idan kai nada tsoka taɓa naka kaji. hukunci na biyu koda na faɗa ko ban faɗaba musilinci ma ya bama wannan yarinya yaro duk da dai malamai sunyi bayani kala-kala akan hakan, dan haka ko da wasa idan kuka ɗauka yaron nan kuka bama Farah matsayin uwarsa ALLAH ya isa ban yafe mata ba idan ta amsa. Yaro na Zinneerah ne har abadan kuma itace zata cigaba da iko da shi matsayin mahaifiyarsa har ƙarshen rayuwarta, kai bamma yarda koda wasa wani ya dangantashi da Farah ba zan ɗauka mataki mai tsauri koda kuwa Abdul-Mutallab ne yayi hakan. Koda alaƙa zata shiga tsakaninta da shi sai dai ta zumunci ko matsar ubansa amma ba uwa ba. Hukunci na ƙarshe idan waɗancan da sukaima wannan ƙullalliyar yazam suma bada saninsu bane to lallai zan kaisu kotu a bi musu kadin haƙƙinsu. Wannan shine hukuncina a matsayina na maihaifinsu”. Kuka wiwi Farah da Zakiyya keyi musamman akan zancen sakin da mazajenau zasu musu dana haramta mata Little. Dan Farah a yau karo na farko ƙara ganin little yasa ya shiga ranta dan kamar an ɗakko ƙaunrasa mai tsanani an dasa mata a ƙirji takeji. Babu wanda ya iya jayayya da wanan hukuncin na mai martaba dan shine kawai zai iya zama darasi garesu. Sai dai yanda suke kuka dolene su baka matuƙar tausayi..............✍
Chapter 138 · 0% Book details