← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 155

Sashe 94

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

.........Koda akazo yin breakfast yau gaba ɗaya gidan aka haɗu harsu Momie domin nuna murnar dawowar Hajiya iya. Aiko taji matuƙar jin daɗi dan bakinta yaƙi rufuwa. Little na jikinta tana bashi da kanta. Ita Zinneerah ma har mamakin yanda ya saki jiki da kowa takeyi, gashi yanzu ta fahimci dai yana neman zama ɗan gidan. Har ranta tanajin daɗin yanda kowa bai taɓa gano alaƙarta da little ɗinba. Amma idan ta tuna randa zasu iya sanin abin na damunta da sakata a fargaba.
        Tunda ta zauna bata yarda ta kalli inda AK yake ba, dan ta samu ta ɗan maƙale ne jikin aunty Safiyya ba sosai ake iya ganinta kamar kowa ba. Garama Huzaifa da yazo zai zauna sai da ya tsokaneta. Murmushi kawai tayi dan ita kam ba iya irin wannan wasan tayiba saboda miskilancin ta. Shima dai ya fahimci miskilarce, hakan ya sashi faɗin, “Like Husband like wife”.
     Murmushi su Baffah duk sukayi, yaran kuwa kowa yay ƙasa da kai yana gumtse dariya. Ita dai Zinneerah ba sanin inda ya dosa tai ba. AK kuwa yi yayi kamarma baiji mi Huzaifa ya faɗaba, ya maida hankali gacin abincinsa kawai dan hajiya iya ta riga tai musu sabon idan suka zauna gaban abinci shi kaɗai suke bama dukan nutsuwarsu har sai sun kammala.
      Shine farkon tashi, kamar an tsikari little shima ya miƙe daga jikin hajiya iya yana faɗin, “Abbana zanje”.
      Yanda yay zaram ɗin ya miƙe da maganar tasa data fita raɗam ya saka kowa yin dariya, banda Zinneerah da aranta take raya (kajimin yaro da shegen ɗafa, wai Abbana).
     AK kam dawowa yay da baya yasa hannu ya ɗaukesa yana murmushi, ba komai kesa little na ƙara manne masaba sai yawon da yake fita da shi, shiko yaro dama akwai son yawo shiyyasa duk inda sukaga maza koda basu da wayo suke maƙale musu. Balle little dake da wayo masha ALLAH.
       “Sweetheart kaima fa ka iya yawo na lura”. AK ya faɗa lokacin da suke nufar ɗakinsa shi da little.
      Mommy dake binsu da kallo ita da Baffah tace, “Ƙuruciyar little tamkar Adnan, har wayon tsiyar ya kwaso bai rageba. Wani irin bugawa ƙirjin Zinneerah yayi a take, har takai ta ɗago ta kalli Mommy batare data saniba. Haɗa ido sukai da Hajiya iya dake kallonta cike da nazari ita, tai saurin maida kanta ƙasa. Harga ALLAH maganar ta daketa shiyyasa duk abincinma ya fita mata a rai.
       Ganin yanda taketa faman juya cokali a cikin abincin Hajiya iya tace, “Inno kin ƙoshi ko?”. Da sauri tako ɗaga kanta jin ta samu mafita, kafinma Hajiya iya ta sake cewa wani abu ta miƙe da sauri. Sauran da duk basu san mike faruwaba basu fahimci komaiba. Da wannan damar Zinneerah ta samu ta silale daga wajen ta koma ɗaki.
Chapter 94 · 0% Book details