← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 155

Sashe 100

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

        A washe garin da aka kai lefe hajiya iya ta samu Zinneerah a gidan Hajiya Falmata ita da Adilah. Yanda Zinneerah ta ƙara canjawa a cikin sati ɗaya ya saka hajiya iya jin daɗi matuƙa, hakama Adilah da sau ɗaya kawai suka taɓa ganin juna a london rungume tayi dan tunda ta ga yarinyar dama ta shiga mata rai, da Hajiya iya ta bata labarin komai kuma shima AK ya bata sai ta ƙarajin tausayi da ƙaunar Zinneerah, tare da ƙara taya ɗan uwanta murnar samun mata dai-dai da shi da zata kawo ma rayuwarsa farin ciki tunda Farah taƙi kwantar da hankalinta ta daina biyema Mammah ta riƙe mijinta kamar yanda ta fara a farkon aurensu.
     Daɗin yanda Zinneerah tai ƙyau mai ɗaukar hankali yasa hajiya iya harda ƙarama hajiya falmata kuɗi tana jera mata tagwayen godiya. Cike dajin daɗi itama hajiya falmata tace, “Ai hajiya namaso ace daga gidan nan sai gidan mijinta za'a kaita, amma hakanma babu laifi tare dani zata tafi can ƙauyen muɗan ƙarasa abubuwan da suka rage”.
         Hajiya iya taji daɗin wannan karamci na hajiya falmata, dan duk da yanda Zinneerah ta canja kogi bayaƙin ƙari. Da wannan damar hajiya iya ta zauna ta sakema Zinneerah nasiha, a yau kuma ta sanar mata an ɗaura mata aure amma bata sanar mata da waye ba. Share-share sai ga Zinni na kuka da hawaye tana kallon haijiya tamkar wata sokuwa.
     Cike da kulawa hajiya iya ta kamo hannunta cikin nata da sigar lallashi tace, “Nasan bamu ƙyauta mikiba Inno, amma insha ALLAH wannan shine gatan da zamuyi miki na har abada. Ki saka a ranki wannan itace taki nasarar cin jarabawar, insha ALLAH nasan bazakiyi kuka ba a wajen wanda muka baki, inamiki fatan alkairi da tarin farin ciki mai ɗorewa a rayuwarki da rayuwar aurenki”.
     Kasa magana Zinneerah tayi sai kuka, ta faɗa jikin hajiya iya tana abinta. Itace kuma aka ɗaurama aure bayan taci alwashin bazata taɓa aureba. Gaskiya da anyi shawara da ita da haka bata kasanceba, batason tai aure a gorantama little, batason tai aure a aibantata akan ta taɓa haihuwa a waje. Bata da burin daya wuce yin karatu mai zurfi a rayuwarta, sai dai kuma duk waɗanan burikan nata da farga basu kai daraja da kimar hajiya iya ba a wajenta. Ta cancanci sadaukar mata da komai kodan alkairinta a gareta. Takumayi imani hajiya iya bazata badata ga wanda zata cutuba insha ALLAH, dan haka zatai haƙuri tayi biyayya a gareta insha ALLAHU. Ashe shiyyasa mmn sadiq keta mata nasiha mai harshen damo ita da hajiya falmata.
     Lallashinta sosai hajiya iya tayi da sake mata nasiha itama tana hawayen, dan dauriya dama kawai takeyi, amma harga ALLAH tana tsananin ƙaunar yarinyar, wannan kuma hukuncine na ALLAH mai saka soyayyar wani a zuciyar waninsa dominsa badan wani abu dake garesaba. Sannan ta sanar mata yau za'a kaita danya wajen babanta, daga can za'a ɗakkota insha ALLAH zuwa gidan mijinta.
      Nanma dai Zinni tayi kuka dajin fargabar tunkarar garin nasu data baro bisa ga dalili mai ƙarfi, takumaji ɗokin zuwa taga babanta da akace ya dawo da ƴan uwanta kuma.
       Hajiya iya na gidan har Zinneerah da hajiya falmata suka kammala shirinsu na tafiya, sai Saifudden da zai kaisu wanda ya iso gidan hajiya Falmatan daga baya ya samesu.

★★★★★

       Koda suka baro gidan hajiya Falmata gidan mmn sadiq suka nufa domin ɗaukar Gwaggo Maryama, ai ko Zinneerah nayin arba da ita ta faɗa jikinta tana kukaama. Ta basu tausayi daga ita har maman sadiq, to amma wannan shine kawai gatan da zasuyima rayuwarta koda ace babu ransu ta dinga tunawa sun mata gata. Dan little ga mahaifinsa kawai zai kasance itama ta samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya. Lallashinta suka sake zamanyi da mata nasiha, kafin Gwaggo Maryama ta shirya su fito dan da ita zasu wuce danya kafin su Mmn sadiq su biyosu suma daga baya.
       Tunda suka ɗauki hanya Saifudden ne kawai ke hira da hajiya falmata da Gwaggo Maryama, itako tayi shiru lafe cikin kujera idanunta a lumshe. Kasancewar tafiyar ba ita kaɗai bace sai taji fargabar tunkarar danyan ta ragu mata a zuciya. Har suka iso gidan mutun ɗaya suka ɗauka hanyar kusada bata buɗe idoba. Sai da taji sun hau hanyar Danya ta buɗe idanu da kallon hanya cike da kewar garinta da tunano abubuwa masu yawan gaske da suka gudana. Isowarsu cikin garin yasa zuciyarta karyewa, sai gata tana hawaye shaɓe-shaɓe.
     Zuwa yanzu kam ƴan Danya sun saba ganin yawan shigowar waɗanan manyan motoci, dan haka kai tsaye aka fara ƴan ƙananun maganar cewar angon Zinneerah ne yazo.

      Su Zinneerah dai basusan anaiba, dan motar na tsayawa a ƙofar gidansu daya sha gyaran biki da aketa shirye-shiye sai zuciyarta ta ƙara karyewa. Itace ƙarshen fitowa jiki a sanyaye, sai da ta ƙarema anguwar tasu kallo da yara da suka baibaye motar waɗanda takeda tabbacin babu wanda ya shaidata, wasuma basu santaba. Murmushi tayi a karo na farko da ambaton Alhmdllhi cikin matuƙar rauni.
       Da sauri ta buɗe idanun nata saboda jin maganar baba dake fitowa yanama Saifudden sannu da zuwa. Juyawa tai a hankali ƙirjinta na harbawa da sauri-sauri. Shima baban tunda idanunsa suka sauka akanta dukkan maganar bakinsa ta gagara fita. Yay tsai yana kallonta zuciyarsa fal wasiwasi. Tabbas fuskarnan dai ta ɗiyarsace, kuma irinta tsohuwar matarsa mafi soyuwa a garesa. Sai dai kuma yana tantama ace Zinneerah ɗinsa ce ta zama budurwa haka tamkar wata jinin larabawa. (Dan gyaran datasha ya sake ƙawatata da ƙyawu mai ɗaukar hankali)
     A wani irin slowly Zinneerah ta nufi baba, batama san ta faɗa masa a jikiba ta fashe da kuka ba. Hakan yayi dai-dai da isowar Tinene ƙofar gidan wadda tun ɗazun aka aiketa amma sai yanzu take dawowa gidan, dan yanzu bata samun damar fita yawonta saita hanyar aikan.
       Da mamaki take kallon wadda ke runme musu da baba, dan haka cikin sassarfa ta nufi cikin gidan kai rahoto. A zabure Inna data gama yima yarinyar karima wanka ta miƙe, hakama Sa'a dake wanke-wanke. Karima ma madai da Yaya Atine dake a cikin ɗaki sai gasu waje wuff babu shiri. Yaya Gajeje dake can gaban murhu ita da ɗiyar Baba Sabi'u suna suyar naman ragon sunan Karima suma dai duk duban Tinenen sukai, amaryar baba dai datasan ina zancen ya dosa tana ƙofar ɗaki zaune tana gyaran ƙumba da tsohon cikinta, murmushi kawai tayi hankali kwance. Kafin bakin wani ya samu damar furta kanzil sai ga baba ya shigo baki washe yana sharar ƙwalla, hannunsa riƙe da Zinneerah dake kuka rurus. Hajiya Falmata da Gwaggo Maryama biye dasu suna faman murmushin jin daɗi.
            Yaya Gajeje ce ALLAH ya bama ikon gane Zinneerah, a take ta saki ludayin hannunta tana ƙwalalo idanu waje da faɗin, “Zinneerah!!”.
      Da gudu Zinneerah ta saki hannun Baba tai kan Yaya Gajeje. Bata damu da a yanda yaya Gajejen takeba ta faɗa jikinta suka saki kuka tare. Tuni Sa'a ta saki soson wanke-wanke itama tayo kansu. Su kansu su Yaya Atine da ba ƙaunar Zinneerah ɗin sukeba, kuma tunda aka kawo kayan lefen nan nata ƙiri-ƙiri suka nuna hassadarsu suda Inna basu san sanda suka nufo ƴar uwar tasuba suka haɗu wajen rungumeta.
     Hakan da sukai ya matuƙar saka baba jin daɗi, yayinda Inna ta daka musu wata irin gigitacciyar tsawa. Sai dai ina su bama susan tanaiba. Amaryar baba kuwa tashi tai da ƙyar tanama su Gwaggo Maryama barka da zuwa, waɗanda sai yanzu Inna tama gansu. Gabanta ne yay matuƙar faɗuwa datai tozali da fuskar Gwaggo Maryama, dan sarai ta ganeta. A kiɗime tace, “Dangin Hauwa a gidana?”. Karaf kuwa sai a kunnen baba. Kansa tsaye yace, “Hauwarma tana nan tafe a gidan naki”. Ya raɓata ya wuce abinsa dan tabarma zai amsa ya kaima Saifudden.
       Ba ƙaramin dukan ƙirjinta furucinsa yayba. Tai baya tana neman faɗuwa ALLAH ya taimaketa ta dafe bango. Babu wanda ya lura da halin da take ciki dansu ta murnar ganin ƴar uwarsu sukeyi.
Chapter 100 · 0% Book details