← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 155

Sashe 4

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

         Baba da Gajeje sun iske ƙofar gidan a yamutse da hayaniyar Inna da wasu a mazan maƙwafta da suka kasa haƙuri suka tanka mata akan dukan Zinneerah da tahau yi tun bayan barin Baba gidan. Yayinda Zinneerah ke gefe tana murƙususun ciwon ciki.
     Ran Gajeje a ɓace da halin mahaifiyar tasu ta shiga cikin rikicin da ƙyar ta lafar da kowa. Kusan minti talatin aka samu wajen ya nutsa. Inna ta shiga gida mutanen dake a ƙofar gidan kuma kowa ya kama gabansa ana zagi da ALLAH wadai da halin Inna Asabe na rashin tausayi.
      Sai a lokacin Gajeje ta samu damar kama Zinneerah dake kwance gefe buɗu-buɗu da ƙasa tamkar an tonita a rami. Gidan ta shiga da ita, Inna zata fara sabuwar jaraba Gajeje ta haɗe fuska tana faɗin, “Innarmu! Innarmu!”.
     Shiru tayi saboda sanin halin babbar ƴar tata itama. Sannan duk yanda takai ga hawa akan masifarta da Gajeje tayi magana bata iya cigaba saboda wani dalilinta daba kowa ya gama saninsa ba.
       Itama Gajejen bata sake cewa komaiba sai kallon Tinene ƙanwarta tayi. “Ke Tinene ɗaukamin karauni a ɗakinku”.
     Baki Tinene ta cika da iska tana ƙunƙuni, sai dai kuma babu damar ƙinyi. Fuuu ta shige ɗakin kwanansu da ada can shine ɗakin mahaifiyar Zinneerah kafin tabar gidan. Wata tsohuwar tabarmar karauni ta ɗakko zuwa gindin bishiyar mangwaro dake a kusan tsakkiyar gidan. Zinneerah na zaune an jinginata da bishiyar, Baba na daga tsaye gefenta kaɗan yana kallonta dayin hawayen zuci. Sai Gajeje dake can kusa da Inna a gaban murhu taɗan kara ruwa jikin wutar ɗan waken Inna na saidawa dan yay ɗumi.
            Gidan yay tsit babu mai cewa uffan duk da kuwa kowa nada abin cewa a bakinsa. Musamman ma Baba, sai dai tsoron matarsa Inna bazai barsa iya furtawaba duk da tsantsar tausayin ƴarsa dake ransa.
      Gajeje ta juye ruwan ɗumin a wani roban wankansu ta sirka takai banɗaki tazo ta kama Zinneerah ta miƙar. Har banɗaki ta kaita da kanta. Bata wani tsaya jan zance ba ta ɗaurayema Zinneerah jiki da kanta duk da kuwa tanata mammaƙewa dan nauyin yayar tasu da suke kallo tamkar uwa a garesu. Tinene ta ƙwalama kira ta kawo mata zani da riga.
            Sosai Zinneerah taji daɗin jikinta da wannan wanka. sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi da lumshe idanu. Baba dake tsaye har yanzu da kansa ya gyara mata tabarmar ta kwantar da ita.
      Inna na kallonsu a kaikaice, watsama Baba wata uwar harara tayi tana yin ƙwafa. Sai dai kuma batace komaiba ta cigaba da tsame ɗanwaken ta.
        Duk da Gajeje taga harar da Innar tasu taima mahaifinsu bata tankaba. Sai ma kwance gefen zaninta tayi tana ciro nera hamsin data sha ƙudindina. “K Tinene zokije nan wajen Dijen kamaye ki sayo mani kunu da suga”.
     “Yaya Gajeje tallafa zan ɗauka, kina ganin Inna harta gama kwashe ɗanwake, gahi Sa'a bata dawo ba, Karima kuma na rimaye”.
      Wani mugun kallo gajeje ta watsamata, a hasale tace, “Ni kike hiɗima haka Tinene?”.
      Kafin Tinene ta bata amsa Inna ta dubesu a hasale. “Wai Gajeje miyasa ke baƙya son zaman lahiyane? Ai gaskiya Tinenen ta hiɗi, inke idonki bai gane miki na kwashe ɗanwakenba”.
       “To amma Innarmu koda shirin ɗaukar ɗanwaken take nanda gidan Dije ne zai gagareta zuwa ta sayo mani kunu? Kenan iya shegen da sukema kowa nima ya hwara zuwa bisa kaina?”.
       Yanda Gajeje ke magana a hasalene ya saka Inna cewa, “K Tinene amshi ki sayo mata, ni bansan wani kace-nace”.
      Tinene na faman tunzura baki da ƙunƙuni tazo ta amshi hamsin ɗin ta fice bayan ta ɗauki wani tsohon kofi. Babu jimawa sai gata da kunun kuwa. Kusan tare suka shigo da Sa'a ɗauke da ƙaton botiki mai ɗauke da sauran gyaɗa da riɗi da taje talla.
      Da sauri ta ƙarasa shigowa tana fadin, “Kai, Kai, Zinni! Yaushe kika dawo?”.
       Murmushin ƙarfin hali Zinneerah taima Yayar tata da itama ke ƙaunarta a gidan, sai dai kuma ta kasa bata amsa sai Yaya Gajeje ce dake zuba suga a kunun da Tinene ta sayo ta bata amsar.
    Kafin Sa'a da hawaye suka cikama ido tace wani abu Gajeje ta maida hankalinta ga Tinene. “K samo mani lidde”.
      “Mu bamu da lidde nan gidan”. Cewar Tinene tana murguɗa baki.
    Jikake bamm! A goshin Tinene, Gajeje ta jefa mata murfin kwano dake kusa da su.
     A take ta zube ƙasa ta fara kururuwar ihu kamar wandda aka kashe. Inna ta saki kwanon yaji a ƙasa ta nufi ƴar tata da sauri. “Gajeje kashemin yarinya zakiyi akan wannan sheɗaniyar yarinyar data gudu yawon tambaɗarta?”.
      “Kaɗanma na mata Innarmu”.
Gajeje ta bata amsa rai ɓace.
      Cikin raɗa-raɗa Sa'a data je ta ɗakko mata ludayin tace, “Yaya Gajeje ki ƙyalesu dan ALLAH, karki tahi gida a huce kan Zinni. Kindai san halin Innarmu ai”.
     Shiru Gajeje tayi bata tankaba. Baba ma dake tsaye har yanzu bai tanka musunba, hasalima hankalinsa na kan Zinneerah da ke shan kunun cike da zalamar yunwar da takeji.

      Zuwan Gajeje gidan ya matuƙar taimakawa wajen bama Zinneerah kulawa. Inda kuma ya katange duk wani bala'i da masifar dake cin Inna a rai. Dan bayanma ta kammala saida ɗanwakenta su Tinene sun ɗauka wani sun wuce talla zani ta ɗauka ta fice gidan wai taje barka wani ƙauye dake can gefensu shima.
     Hakan yama baba daɗi sosai. Dan koba komai sa samu damar jin yaya akai Zinneerah tabar gida a kwanaki ashirin da shida da suka shuɗe, da kuma yanda akai ta dawo musu yau a wannan halin?.
          Suna zaune shi da Gajeje suna tattaunawa akan hakan Zinneerah dake barci tun ɗazun ta farka a firgice da ciwon ciki. Duk kanta sukayo suna tambayar ko lafiya?. Bata iya amsasuba sai da ya lafa mata.
    Ta share hawayen dake sauka a kumatunta. “Yaya Gajeje cikina kemin ciwo”.
     Basu kawo komai a ransuba sai yunwa. Dan haka Gajeje tace, “Zinni yunwace nasani. Sannu kinji. Idan zaki iya tashi kiyo alwala kiyi sallar azahar da la'asar sai kizo ga abinci kici”.
           “Zan iya yaya Gajeje” 
Ta faɗa tana maida kallonta ga baba dake kallonta cike da raunin zuciya dana idanu.
   “Baba ina wuni”.
Murmushin ƙarfin hali yay mata da shafa kanta. “Lafiya lau Uwata yaya jikin?”.
      “Da sauƙi baba”.
“To madalla. tashi kiyi sallar maraice na ƙara yi”.
      Bata musaba ta miƙe. Jin gidan shiru ya sata sanin Inna da su Tinene duk sun fice. Hakan ya mata daɗi. Alwala tayo tazo ta wucesu zuwa ɗakin kwanansu. Babu abinda ya canja a ɗakin nasu sai ma shirgin kayan dauɗar su Yaya Sa'a. Dama itace mai kimtsa ɗakin dayi musu wanki. Kayan taɗan ture gefe ta tayar da salla cike da ƙarfin hali dan batajin daɗin jikinta gaba ɗaya. Duk da sallar ba'a cikin tsari akayitaba tadai gabatar ta sake komawa wajen baba da yaya gajeje.
          Abinci yaya Gajeje ta fara bata taci. duk da yunwar da take ji har yanzu taci abincin a nutse dan sam dama ita bata da garaje ko gaggawa. Bayan ta kammala ta wanke hannu ne Yaya Gajeje ta ce, “Zinni kinga marece yayi inason na koma gida nabar su Rabi'u. Munason ki nutsu ki faɗa mana yaya akai kika bar gida ne batare da sanin kowaba? Ina kuma kikaje?”.
          Duk da ƙarancin shekarunta hakan bai hanata jin ɗaci ba a ranta. Ta share hawayen dake rige-rigen zubo mata tana gyara zama. “Baba wlhy ban gudu ba. Bayan tafiyarka kasuwa sai I.......
       Jin tayi shiru tana kallon hanyar shigowa yasa Baba da Gajeje saurin kallon wajen suma. Inna ce ke shigowa cikin gidan tamkar wadda aja jeho.
     Ganin yanda duk suka watso mata idanu ya sata fara magana a harzuƙe. “Halan cin nama na akeyi kuka watso mani idanu haka?. Wani annamimancin kike hiɗi masu a kaina ko?”.
     Ta ƙare maganar tana watsama Zinneerah mugun kallo.
        Gajeje ta dubi Baba da yay ƙasa da kansa. ta dubi Zinneerah da itama kan nata ke a ƙasa tana hawaye. Wani irin tausayinsu da jin zafin mahaifiyar tasune ya ɗarsu a ranta, musamman yanda take ƙasƙantar musu da mahaifi a gabansu duk da tsufansa. taɗan girgiza kanta tana dubanta. “Amma Inna miya kawo wannan zancen daga shigowarki? Yarinyar da ke cikin halin ciwo wane kuma munahincinki zatayi?. Ni a ganina kamata yayi kema ki shiga jerin masu murna da dawowar Zinni gida kodan tashin hankalin da muka shiga na rashin sanin inda take a kwanaki ashirin da shida ɗin nan”.
       “Tunda uwatace ta ɓata ko? Kune kuke ɗauka ɓata tayi dama ai, yarinyar da ta tafi yawan taɓaɗanta data saba har kuke damuwa da inda taje. Inda ba guduwa taiba wane shege ne ya dawo da ita yanzu da ƙahwarta?. adai jura zuwa rafi, wataran muna zaune za'a shigo mamu da ɗan dakan kuka na tabbacin yawon tazubar....”
    Tsam baba ya miƙe batare da cewa uffanba ya fice gidan. Itama Gajeje rai ɓace ta miƙe tana magana cike da rawar murya. “Innarmu wannan hurucin naki dai kau sam bai dace ba. Dan koba komai itama Zinni ɗiya take garegi, yanda kuwa take mace haka Sa'a da Tinene da Karima suke mata. Baƙya tsoron mugun alkaba'in da kike hiɗi gareta ya dawo bisa kanmu ne”.
      Wani mugun kallo Inna taima Gajeje. Kamar zatai magana sai kuma tai shiru. Itama Gajejen bata sake tankawaba sai miƙar da Zinneerah da ke kuka tayi suka shige ɗaki. Sai da taga ta kwanta sanann ta fara magana. “Zinni bara naje gida, insha ALLAHU gobe da hwarar sahiya zan dawo, dan akwai raɗin suna gidan malam mato dama da zamu shigo. To daga can nan zan wuto na yini. Ki ƙara haƙuri da halin Innarmu watarana sai labari kinji”.
       Kai Zinneerah ta ɗaga mata tana share hawaye. Muryarta na rawa tace, “Nagode Yaya Gajeje”.
    Murmushi kawai Gajeje tayi da shafa kanta ta fito a ɗakin. kai tsaye ɗakin Inna ta nufa dan tanaso suyi magana.............✍

      *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.

*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_
Chapter 4 · 0% Book details