← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 155

Sashe 102

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

      Duk wani abinda mmn sadiq zata iya buƙata na abincin da ƴan uwanta zasuci da abinta tazo, hakan yasa suna isowa babu jimawa ta bada aka saya mata icce mai yawa, ta kuma ware kuɗin ruwa. Duk da abin yama baba ciwo baice mata komaiba, dan ganinta kawai sai da ya sakashi share ƙwalla, yanason Hauwa'u matuƙa, ƙaddarar iyakar zamace kawai ta shiga tsakanin su da sharrin Inna.
      Tuni Zinneerah ta shige cikin dangin mahaifiyarta da suka nuna damuwarsu akanyi watsi da lamarinta sunata neman afuwarta. Ita dai nata murmushi ne da tabbatar musu babu damuwa. Daga haka aka shiga shagalin biki.

         Batare da Zinneerah tasan da zuwan su Bahijja ba sai gasu suma kusan biyar na yamma driver ya kawosu, taji daɗi matuƙa dan sune dai ƙawayen dama. Garama isowar ƴan ɗan musa da sakina yasa taɗan samu ƙawaye, Tinene nata ɗari-ɗarin shiga cikinsu Zinneerah ta jawota tare da gabatar musu da ita.
    Sukam babu ruwansu basusan wulakanta mutaneba, hankali kwance suka amsheta babu wani nuna ƙyama gareta ko makamancin hakan.

*KANO*

        A kano ma dai gidan hajiya iya ya ɗauki haramar dangi da abokan arziƙi, dan dole AK yabar gidanma gaba ɗaya ya koma nashi dayasha gyara inda za'a saka amarya dama Uwargidan kanta. Dan ya ƙullama Farah batare data san dawan garinba tanacan katsina suna jiran tsammani ita dasu Mammah.
       Ƙiri-ƙiri AK yace bai yarda da wata dinner da shirme ba. Hajiya iya tasan kishinsa na tsiya, amma batai zaton zai nuna akan Zinneerah da aka aura masa babu neman shawara ba, dan duk da bikin Farah Mammah ta nuna musu iko akansa haka ya hana yin kowacce bidi'a. Ba kuma komai yasa hakaba sai kishi, dan AK nada matuƙar kishi gaskiya abin a jininsu yake kam da gaske.
      Amma duk da haka dai an shirya walima da liyafar cin abincin rana, dan Baffah yace bazasuyi biki lami ba, Khalipha kuma da su Huzaifa suka shirya fati iyakar su mazan kawai dan gayyato abokan AK na kasuwa dana makaranta sukai sosai batare daya sani ba. 
       Abin mamaki kuma sai ga Uncle Ahmad da iyalansa babu zato babu tsammani, sai baffah da AK ne kawai suka san da zuwansu. A take gidan ya ƙara harmutsewa da farin ciki, babu wanda yabi takan matarsa daketa faman yatsine-yatsine, ƴaƴanshi kuwa dake a ɗarare saboda rashin sanin dangi AK ya musu jan ido tunda shi ba baƙonsu bane. Aiko sai gasu sun saki jiki a cikin su Saifudden.
       Hajiya iya kuwa duk da haushin uncle Ahmad ɗin da takeji saita daure ta danne komai dake ranta ta tarbesu da farin ciki da ƙewa. Uncle Ahmad ya rungumeta yana hawaye itama tanayin nata. Daga ƙarshe dai su Mommy suka lallashesu akan suyi haƙuri.

*KATSINA*

       Ta wajen su Mammah kuwa yau Farah ta haɗa kayanta tunda safe tace zata wuce kano sabida cimata ƙaniya da Mahma tayi a ɓoye a daren jiya, ta kuma nusar da ita inhar bata daina biyema Mammah da aunty Zakiyya ba to wlhy ƙwaɓarta na gab dayin ruwa. Dan AK zai iya ɗagama mahaifiyarsa ƙafa kodan kasancewarta uwa a garesa amma ita wahala zatasha, ƙarshema ta ƙare da saki idan bata maida hankalinta jikintaba.
     Kalmar sakin nan itace ta rikitata tun a daren ta shiga kiran AK amma yaƙi yin picking call ɗinta, daga ƙarshema ya kashe wayan duka. Wannan ruɗanin ya sata shiryawa da farar safiya tace itafa sai kano.
    Masifa Mammah da Aunty Zakiyya suka shiga mata akan hakan amma taƙi saurarensu tace suyi haƙuri itadai zataje ƙilama ta samo amsoshin da suke zaman jiran nema ga wanda ke musu bincike. Ba ƙaramin haushi abin ya basuba, musamman ma aunty Zakiyya data nuna har a fuskarta, sai dai tai shiru bata faɗi abinda ke bakintaba saboda wani dalilinta.
     Lallaɓa Farah Mammah tasoyi. Ta kamota jikinta cikin lallashi take faɗin, “Haba Farah, kinsan dai komi muke akanki mukeyinsa, bakuma zamuyi abinda zai cuta miki ba. Indai Abdul-Mutallab ne zaiyi fushinsane ya gama ma ya dawo lallaɓaki da kansa. Ni banason ne dangin ubansa su maidaki kamar wata mara gata shiyyasa kikega ina haƙilon nan. Dagani harke taimakon juna mukeyi, banason rasa Abdul-Mutallab a rayuwata, kema kuma nasan bazakiso ki rasashi ba ai. Kuma wannan sakacin namu shi zaisa ya suɓuce mana ɗin dan wannan kakar tasu da Kabeer kansu kawai suka sani, sosuke su rabani da shi”.
      Cikin rashin damuwa Farah tace, “Amma Mammah sai nake ganin kamar bata hanyar da mukebi zamu iya maidoshi garemuba. Kinsan dai yanada taurin kai, garama ki bari na kasance a kusa da shi maybe naji komai dake faruwa sai mu magance cikin sauƙi”.
      Wani alama Mahma taima Farah da ido tana sakin murmushi da ɗauke kanta gefe kamar batasan sunayi ba.
     Cike da masifa Aunty Zakiyya tace, “Mammah dan ALLAH barta taje, itace zatasha wahala a hannunsu ai bawani shege ba, su dangin miji har wani abin kwantarwa kai ne. Wlhy banason dangin miji bakuma zan taɓa sonsuba musamman irin naki. Kina dai ganin duk sadaukarwa da Mammah tayi ta bar karatunta da ƙasar data tashi a ciki ta biyo Abbansa daga ƙarshe mata har uku ya aure sai kace wani bazazzage (zazzagawa😂😜🙏🏻), mi ake da namiji mai shegen aure-aure. Kema idan kikai wasa haka kakarsu zatasa Abdul-Mutallab ɗin yayta aure-aure shiyyasa mukeson baki kariya tunkan faruwar hakan amma kina neman watsa mana ƙasa a ido”.
      Wani irin tuƙukin bakin cikine da kishi ya tasoma Farah, a take tsanar da Mahma ta fara rage mata nasu Hajiya Iya ta ƙara dawo mata sabo, ganin yanda ta fara nutsuwa da maganar aunty Zakiyya yasa Mahma saurin tsoma musu baki.
      Nikuwa da zakuji dakun barta ta tafi ɗin, ta hakanne kawai zamusan mike faruwa? Sannan muji ta tushiyar da aka samar da yaro, tun farkoma da haka kukayi da an wuce wajen, dan irinsu Abdul-Mutallab kwantar da kai sukafi so ga matansu ba shirme da hayaniya ba. Yanda yakeson Farah data lallami kuka bisa ko kuka sakata tabisa ita da kun kamo bakin zaren. Su kuma danginsa wannan kauɗin da kuke sakata tana musu shi zaisa su sakashi ƙara auren dan zasuga tanada ƙarancin tarbiya, tun farko data bisu a yanda sukeso da bahaka ba, kudaiyi tunani gaskiya”.
        Zaram Farah ta miƙe tana faɗin, “Mahma maganarki gaskiyace wlhy, ni dai kuyi haƙuri Mammah bara naje, duk halin da ake ciki zakunaji ta waya insha ALLAH ”.
    Daga haka bata saurari cewarsuba ta fice abinta dan Mahma ma tama driver dazai kaita magana.
    Daga aunty Zakiyya har Mammah sun shaƙa, sai dai yanda Mahma ta haɗe gabas da yamma yasasu kasa cewa komai. Sunaji motar data ɗauka Farah ta wuce badan sunso ba.

     Tafiyar Farah kano da kusan awa shidda wanda suka saka ya musu bincike ya iso gidan. Ko gaisuwar kirki basu bari sunyi dashi ba suka fara jera masa tambayoyi akan aikin da suka bashi. Sanin halin aunty Zakiyya yasa baice komaiba ya miƙa musu takardun hannunsa.
      Mahma data fahimci komai zai iya faruwa ta dakatar da Mahma daga bude envelope ɗin, “Nikam da kun sallamesa ya wuce sannan zaifi”.
    Babu musu Mammah ta miƙe ta ɗakko masa sauran kuɗin aikinsa ta bashi, yaji daɗin haka kuwa ya tafi yana musu godiya, dan ya tabbatar da ace sai da suka duba babu abinda zai samu.

         Aunty Zakiyya ce ta fara cin karo da invitation ɗin walima da za'ai jibi idan ALLAH ya kaimu da liyafar cin abinci, jikinta har rawa yake wajen miƙama Mammah. Itama da taci karo da hoton Zinneerah da AK a take ta miƙe cikin rawar jiki tana kallon invitation ɗin. Wani shegen ashar ta kwaso ta dire akan Baffah.
     Mahma da dariya ke neman kufce mata tai saurin riƙo hannunta tana girgiza mata kai ganin ta doshi ƙofar fita. “Hindatu ki nutsu mana, faɗamin mike faruwa?”.
     “Ai komaima ya faru Addah, ni Kabeer zai rainama hankali, yasan mi yake ƙullawa akan Abdul-Mutallab shiyyasa yace muyi game. Na rantse da ALLAH sai na nunama guy ɗin nan asalin color ɗina. Na shiga uku shikenan ya ƙwacemin yarana. Wlhy bazan bashiba ko sama da ƙasa zai haɗe......”
      “A'a bama sai sama da ƙasa ya haɗeba kwantar da hankalinki”. Mahma ta faɗa tana zaunar da ita a kujera. Amma ina Mammah zillewa take tana botsewa hawaye fal fuskarta wasu na korar wasu. Sai masifa take tamkar zata haɗe harshenta. Tana ta rantsuwar saita maka Baffah kotu akan ƴaƴanta dan bazata yarda ya rabata dasuba. Kuma auren AK ta rantse saita rabashi da Farah kawai zai rayu.
    Aunty Zakiyya ma masifa take iyakar iyawa. Sai dai ita Mahma batabi takantaba dan nata mai sauƙine. Da ƙyar Mahma ta samu ta taushi Mammah akan ta bari sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu suje Kano ɗin suyi nagana da Baffah. Sanin Baffah na matuƙar ganin girma dajin maganar Mahma yasa ta haƙura akan sai zuwa goben, sai dai tanata neman no ɗin AK a kashe, dan dama Mahma ta sakashi ya kashe wayar, baƙon na zuwa ta turama AK text message.

___________★
Chapter 102 · 0% Book details