Sashe 7
Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Minister ya sake kallon Tiger da yake kallon wani wajan daban kamar ba dashi suke magana ba, fuskar nan a cushe kamar ko yaushe. Minister ya ce, "Dan samari ka burge ni fa, gabaɗaya yanayin ka ya bani mamaki sosai." Kallon Miniter ya yi a kasalance ya ce, "na gode." Sen ya kalli Minister ya ce, "jiya baka ga ya saka an kama wani da ya ƙwacewa wani waya sannan ya kashe shi ba? Maganar da take trending kenan a media ai."
"Yeah...yeah..I saw it. Ya bani mamaki sosai Sentor." Yayi murmushi ya kalli Tiger ya ce, "Tiger!." Ya jiyo ya kalle shi ba tare da ya amsa ya ce, "Daman magana ce akan zaɓen chairman da za a gabatar da kano. Kai ka san na mu shine a DPD so bama buƙatar wata damuwa da zata haifar mana da matsala shiyasa na kira ka." Omar ya kalle shi ya ce, "kamar ko yaushe zan maimaita, babu abinda zai faru. Amma mun jima da daina tayar da hayaniya a wajan zaɓe, an daina jiwa kowa ciwo, amma na tabbatar da komai zai tafi yadda ake so."
Minister ganin yadda Tiger yake magana sai ya murmusa ya ce, "Tiger I like your confidence." Kallo minister yayi amma bai ce komai ba dan ba kasafai ya cika so ayi masa turanci ba, ba komai yake fahimta yadda ya kamata ba shiyasa baya so ma ayi. Senator ya sake kallon sa ya ce, "na san in kace babu matsala babu ɗin, shiyasa nake matuƙar jin daɗin aiki da kai."
"Na gode" ya furta a taƙaice ba tare da ya saki fuska ba balle murmushi.
Sen ya ce, "Magana ta gaba; Akwai daughter na da zata zo Kano biki next week,ina so duk inda zata je ka kasnace a kusa da ita saboda an taɓa attacking na kashe ta kwanaki baya. Nafi yarda da kai akan jami'an tsaro dan na san zaka fi bani abinda nake so. Kuma mutanen Kano duk sun sanka babu wanda zai kawo mata raini in tana tare da kai, Kana ganin kana da damar Hakan?." Tiger ya girgiza kai yana tunani, aiki da Sen yana matuƙar kawo kuɗi, shi kuma yana buƙatar su a yanzu. Zai karɓa ne kawai saboda kuɗi da yake so wanda ya ke adanawa saboda bikin Didi zai iya zuwa ko yaushe, kuma shine uba shine uwa a gareta, duk abinda ya kamata shi zai yi.
Hakan ya saka ya ce, "Akwai dama, amma bana kwana a wani wajan in ba gida ba. Zan iya zama tare da ita daga safe har dare amma a gida zan kwana."
"No problem, buƙata ta daman ka kasance da ita din a duk inda zata je, If possible ka zama mai kai ta ko ina."
"Ka É—auka an gama" ya faÉ—a yana kallon sa.
Sen ya yi murmushi ya ce, "Dakyau Damisa!." ÆŠan sakin fuska yayi kaÉ—an ya juya suka haÉ—a ido da Minister da tun É—azu kallon sa yake yi dan shi mamaki yake bashi sosai, maganarsa da yanayin komai ya yi masa.
"Hello Dad, how are you?" Narma ta faÉ—a tana shigowa falon amma sai ta tsaya cak ganin mutane biyu a zaune. Minister ya kalleta ya yi murmushi ya ce, "Our Barrister." Tayi murmushi ta ce, "Daddy good morning."
"Morning my dear, how's your day going?."
"Been good Dad. Ina ilham?."
"Ilham tana Canada, tayi miki wayo ta tafi phd."
"Oh Dad! I'm so tired from studying, I really need some rest" ta faÉ—a tana É—an sauke numfashi kaÉ—a tare da juya ido alamun gajiya.
Minister ya yi murmushi ya ce, "As your wish." Kallon Tiger tayi da yake zaune kamar bai san ma ta shigo ba amma a zuciyarsa yana so ya tuna inda ya san maganarta, dan tunda tayi sallama ya É—au murya amma ya kasa gane a ina yana santa.
Ita kuma Narma ta É—auka tare suke da Minister hakan ya saka ta ce, "Hiiii" ta faÉ—a tana kallon Tiger wanda ya É—ago idanunsa ya watsa shi a cikin nata. Da sauri ta kawar da kai jin idanunsa a idonta kamar jan wutar lantarki, mamaki take yi waye wannan haka da idanunsa suke da ban tsoro a kallo É—aya haka?. Shima ya É—auke kansa ba tare da ya amsa ba dan lokaci É—aya ya gane itace wacce suka gani da Didi jiya a tv.
Sen ya kalle ta ya ce, "Narma ina aikin?." Cikin shagwaɓa ya ce, "Dad I need to talk to you about something ."
"Alright, ki koma gida zan shigo in na gama."
"Dad ka yi sauri."
"Okay Daughter." Yana faÉ—a ta fita da sauri.
Kallon Tiger ya yi sannan ya ce, "She's my second daughter Narma, Itace wacce nake maka magana a kai. Itace wacce na amince da kai na baka ragamar kula da ita." Omar ya kalle shi ya ce, "babu damuwa." Ya girgiza kai cikin gamsuwa dan ya gama amincewa da aikin Omar.
Sen ya ce, "Akwai inda zaka je in ka bar nan?." Omar ya É—aga kai alamun eh ba tare da ya yi magana ba.
"Okay I think it's okay, zaka iya tafiya. In yaso in lokacin tafiyar na ta yazo zan sanar da kai. Zan tura maka kuÉ—in mota."
Minister ya kalli Omar kafin yayi magana ya ce, "Tiger ya kamata ace ni na biya kuɗin motar zuwa garin nan, zan iya samun account number ɗina ka?." Omar ya kalle shi kai tsaye ya ce, "Me zai hana?." Ya karanto masa account number shi kuma ya saka masa kuɗi. Omar da ya ji ƙarar shigowar saƙo wayar sa ya ce, "na gode."
Minister ya ce, "you deserve it, kar ka damu. Yadda ka ke yin komai a nutse ya burge ni sosai, Nima zan so na shiga cikin wanda za a dinga taimakawa." Omar bai ce komai ba ya kalli Sen da yake kallon sa sai ya ce, "Zamu yi magana Tiger, na san in kana nan babu matsala."
Miƙewa Omar ya yi ya ce, "A duk inda nake matsala bata zama, koda tana wajan da naje zata kama gaban ta.Kamar yadda ruwa da wuta basa haɗuwa waje ɗaya haka ni da matsala bama zama waje ɗaya." Sen yayi murmushi cikin jin daɗi ya ce, "ni na san da wannan."
"Na bar ku lafiya" ya faɗa yana fita da hanzari cikin takunsa na isa da ƙasata.
Minister ya kalli Sen bayan ya fita ya ce, "Amma wannan yaron sam bai yi kama da ƴan daba irin na mu ba, Anya kayi bincike akansa sosai?. Ka duba fuskarsa fa, irin kyawawan mazan nan ne masu kwarjinin tsiya." Sen yayi dariya ya ce, "kai ka san bazan fara mu'amala dashi ba in ban san shi ba, na san shi tun da jimawa na kuma san komai akansa. A kaf kano tsoron yaron nan ake ji in dai a ɓangaren daba ne, har ta kai ta kawo ƴan sanda su kan neme taimakonsa a ɓangaren kama wani ko wani abun. Duk yadda ka kai ga jin kai jan wuya ne da yazo waje ya kalle ka ya ce ta shi ka bi wannan ɗan sandan sai ya je. Dabarsa mai tsafta ce duk da a sanin da nayi masa a baya yafi haka jagaliyanci. Jikinsa mai matuƙar tsafta ne, baza ka taɗa ganinsa ka ce ɗan daba bane, amma kallo ɗaya zaka yi masa gabanka ya faɗi."
Minister ya ce, "Amazing! Ya burge ni sosai fa, especially yadda yake magana da izza kamar shi ne senator É—in."
"Bai yarda da wulaƙanci ba, tun farkon haɗuwa ta da shi ya faɗa min wannan. Kai baka ganin akan kujera nake akan kujera yake baka yi mamaki ba?."
"Nayi mamaki sosai, na saba ganin thugs suna warin wiwi da sun ganka su zube a ƙasa suna magana mara kan gado, But he's different gaskiya."
"That's why I choose him, kar ka yi mamaki in nace maka bai jima da fitowa daga prison ba."
Minster ya ce, "a yadda ka ke bani labarinsa prison a wajan irin su ai is just normal, kamar a shiga gida ne a fito."
"Ya yi hidima a lokacin zaɓe, yana daga cikin wanda suka bani kujerar da nake kai. Sannan ka san shi baya kisa a lamarinsa, in ya zauna a ake zaɓen ma ganin sa zawo yake saka maza balle ya ɗauko wuƙa. In kaga ya zubarwa da mutum jini shi ya so, Minister, totally Tiger is different"
Minister ya yi murmushi ya ce, "I see. But yana da karatu?."
"Bashi da ilimi, bana tunanin ya yi SSCE."
"Ya aka yi ka ke mu'amala dashi kai da baka zama inuwa É—aya da wanda bashi da karatu?."
Sen ya yi dariya ya ce, "shi ai daban da sauran mutane. Shi rayuwarsa ya ke sadaukar min, dan in aka kashe shi akan aikin da yake yi min an kashe banza da wofi, kuma ina amfani dashi ne daga lokacin ya wuce shikenan. In ba dan haka ba shi da ganina sai dai in a waya." Dariya suka yi gabaɗaya minister ya ce, "Yaran ba su da hankali, muna gina rayuwar mu suna ɓata ta su."
"Rashin ilimin kenan."
"Kaga in ka haÉ—a Narma dashi babu sauran damuwa."
Sen yayi dariya suka tafa kafin Minsiter ya ce, "Yaushe zamu yi bikin Narma ne?." Sen ya ce, "tana da damuwa, taƙi mayar da hankali a kai. Akwai ɗam Sarkin Gombe yana sonta amma wai Gombe tayi mata nisa, Ina jin dai da Asharfa ɗan gidan gwaman Katsina za a yi."
Minister ya ce, "wow! yaron yana da hankali sosai."
"Sosai ma kuwa, Maganar baza tayi nisa ba ina so ta nutsu sosai ne."
"Hakan yana da kyau, a barta ta zaɓi abinda ta ke so." Daga nan suka cigaba da tattauna abinda ya shafe su kafin Dad ya shiga ciki minister ya fita.