← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 54

Sashe 20

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin yadda take magana murya a sanyaye sai ya ɗago ido ya kalle ta ta ƙaraso inda yake ta ce, “ka zauna don Allah, ba don ni ba.” Ba shi da mafita dole ya zauna ta wuce kitchen sai gata ta dawo da lafiyar jollof rice da kuma ƙaramin plate na awara ta ajjiye masa. Kallon shinkafar ya yi ya ce, “bazan ci shinkafa ba, wannan ya isa” ya faɗa yana ɗaukar ƙaramin plate ɗin awarar ya riƙe a hannunsa ya ɗora ƙafa akan ɗaya.”

Fara ci yayi kusan mintina biyar kafin ya kalle ta ya ce, “Amma ya yi daɗi sosai, kuma babu yaji.” Didi tayi murmushi ganin ya sake ta ce, “na san baka son yaji ai shiyasa sauce ɗin ma babu abinda zai saka ta yaji.” Kai ya girgiza cikin izza da ƙasaita ya kalle ta ya ce, “ina jinki.”

Didi ta ce, “Kamar yadda kaji sunansa haka sunansa yake, ma’aikaci ne ya taɓa aure amma basa tare da matar. Kuma alamunsa ba da wasa yazo ba gaskiya.” Ya girgiza kai ya ce, “haka ake so. Yanzu ya maganar ta tsaya?.” Ido ta zuba masa sannan ta ce, “ka san ba ni zan bayar da kaina ba ko? To na tura shi wajan Kawu.”

Cak ya dakata da abinda yake yi ya kalle ta suka haɗa ido tayi sauri ta ce, “babu yadda na iya ne, ya nemi ganin dangin babana dole na yi masa kwatancen gidan Kawu. Kai ka san ai ba ni zan aurar da kaina ba dole a nemo ganin dangina.” Ajjiye plate ɗin hannunsa yayi bai ce mata komai ba ya miƙe tsaye ya fita.

Daman ta san ƙarshen cin abincin na sa yazo kenan tunda ta ambato maƙiyansa, taji daɗi da bai yi magana ba dan ta san da faɗa zasu yi dashi. Su Bashir ta kira ta basu abincin sannan ta shiga tayi shirim kwanciya. Tunanin baya ne yake dawo mata dawo mata cikin kanta, ta yi ajiyar zuciya tana tuna abinda ya wuce.

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 09.*         

Ranar asabar da daddare Omar da Didi suna zaune a falo yana aikin danna waya ita kuma tana kallon tv, bata ce masa komai ba ganin ya ƙi ya saki rai, sai ɗaure fuska yake yi ba kamar jiya ba, bata so ta yi masa wata maganarta tsokano shi hakan ya saka ta yi shiru. Shirun ne yayi yawa  hakan ya saka ta kalle shi ta ce, "Omar." Ya ɗago manyan idanunsa ya kalle ta sai ta langwaɓar da kai ta ce, "don Allah ka daina buɗe idanunka akan fuskar mutane, wannan idanu naka sai ya firgita mutum cikin dare."

Bai yi magana ba ta ce, "zan faɗa maka wata magana amma kar ranka ya ɓaci don Allah."
"To" ya amsa a taƙaice kafin ta ce, "Ɗazu Kawu ya kira ni, maganar AbdulHamid ce. Ya samu Kawu ɗazu da yamma, shi kuma ya ce ya bashi lokaci zasu ɗan yi bincike a akansa."

Ta ɗauka da ta kira sunan Kawu ransa zai ɓaci kamar kullum amma sai taga yayi murmushi mai ƙayatarwa da daɗin kallo. Murmushi yana yi masa kyau matuƙa, yana fitowa da asalin kyaunsa da kwarjininsa. Ya ce, "Allah ya tabbatar da alkhairi."

Sai taji daÉ—i sosai a ranta ta har hakan ya bayyana a fuskar ta ta ce, "Amin Habibin Mama. Yaushe zaka nemo taka matar? Kaga in Allah yayi aurena dashi sai a haÉ—a gabaÉ—aya ko?." Kallon ta yayi tare da É—aga yalwatacciyar gashin girarsa ya ce, "Tare mu ka zo duniyar da zamu yi aure tare?."

"Ba tare muka zo ba, amma zan so mu yi aure tare."
"Ke kika fara zuwa duniya, ke zaki fara aure."
"Ai abin ba daga nan yake ba, yara nawa aka haifa a bayana duk suna yi aure har yaran su duk sun girma?."
"Su daban Omar daban" ya faÉ—a yana kallonta.

Didi ta ce, "to naji, Amma ya kamata dai kaima ka fara neman matar aure, kaga in nayi aure gidan nan bazai maka daÉ—i ba, waye zai maka girki ka ci da sauran su?." Omar ya ce, "kin san dai na iya girki ko?."
"Na sani, amma yadda baka zaman nan zaka so ace kana dawowa abinci zaka ci ba sai ka dafa ba." 

"Ni wannan bai dame ni ba, ki yi auren dai kawai yafi komai a yanzu." Tayi murmushi cikin tsokana ta ce, "faɗa min wacece budurwarka, baka ɓoye min komai amma baka taɓa faɗa min wacce ka ke so ba." Murmushi ya saki mai sauti yana kallon ta ya ce, "Ni aka ce miki ina da budurwa?." Didi ta harare shi ta ce, "Santalelen saurayi mai kyau da kyaun zati kamar ƙanina ai bazai rasa budurwa ba. Ina jin ka ya sunanta."

"Aisha" ya faɗa cikin gatse yana kallon ta da murmushi. Dariya tayi jin sunan da ya faɗa ta ce, "ka ce takwara ta ce ma, Yaushe zata zo na ganta?." Bai ce komai ba kuma bai daina murmushi ba ta ce, "Wai! zan so naga mace da Omar zai so, zan so naga lokacin da Omar zai fara soyayya. Allah ka bani aron rai da lafiyar da zan ga Omar na matuƙar son wata mace bayan Didinsa. Wacce kalar mace ka ke so? fara ko baƙa?."

Kallon ta yake cikin mamaki ganin yadda ta saka shi a gaba tana yi masa wannan tambayoyi kamar wanda ya ce mata neman aure yake yi. Murmushi ya yi ya ce, "ni wai na ce miki aure zan yi ne?."
"Ko baka ce ba na san zaka yi."
"To ba yanzu ba." Tayi murmushi tana kallon sa ganin shima murmushin ya ke yi ta ce, "Allah ya kaimu lokacin, Allah ya kawo macen da zata gyara min kai ka hau kan hanya mai kyau ka sauka daga wacce ka ke kai."

"Hmmm" shine abinda ya furta kawai amma murmushi yake yi. Sai kuma tayi ajiyar zuciya alamun akwai abinda ta tuna amma bata ce komai ba.

Ganin yanayinta ya canja sai ya so ya kawar da damuwarta ya ce, "ai ki kiyaye ganin matar da zan aura, sai na baki mamaki." Jin abinda ya ce sai fara'arta ta dawo ta ce, "Allah ya nuna mana lokacin, Allah yasa baza a samu matsala a aurenka. Allah yasa kar ka nemi wacce za a ce tafi ƙarfin ka."

Ga mamakin ta sai taga yayi dariya kaɗan ya ce, "har akwai macen da tafi ƙarfin namiji ne a duniya?." Didi ta ce, "sosai ma kuwa, akwai inda kai baza kaje kace ma a baka aurenta ba, saboda matsayin ku ba ɗaya ba ba." Ya girgiza kai ya ce, "ni kam ban ga macen da za a ce tafi ƙarfina ba, sai dai in bana sonta." Kallon sa take yi jin da gaske yake yi ta ce, "kai dai Omar ayi shiru kawai, amma akwai matan da sun fi ƙarfin ka nesa ba kusa, tazarar ku kamar tazarar sama da ƙasa. Kyaun da ka ke dashi ba komai ba ne."

Taɓe baki yayi kawai bai ce komai ba, amma shi kam a wajan sa bai ga macen da za a ce tafi ƙarfinsa ba, in dai yana sonta tana sonsa to bata fi ƙarfinsa ba.

        A wannan lokacin Nayla tana ƙofar gidan Hajja hannunta har rawa yake yi wajan kiran number Salma, tana ɗauka ta ce, "Salma ya naga gate ɗin gida a kulle?." Daga can ɓangaren Salma ta ce, "Wallahi mun fita, mun je dubiya kuma bamu taho ba."

Nayla ta ce, "Innalillahi na shiga uku, Salma fitsari nake ji kamar nayi hauka. Yanzu ina zan shiga? Kin san ba kowa na sani a unguwar nan ba."  Salma ta ce, "Wallahi bamu taho ba, ki shiga gidan Didi kawai."
"Gidan Didi kuma? Ni ce zan shiga gidan Didi?."
"To ba lalaura ba ce? Ita kaÉ—ai ki ka sani a unguwar kawai ki daure ki shiga." Tsabar haushi Nayla kashe wayar tayi ta fara zaga wajan saboda fitsarin da take ji kamar zai zubo.

Haka kawai ta shiga gidan Didi Omar ya ganta yayi mata tsawar da zata yi fitsarin a wando, me ya kai ta shiga gidan Didi..? ai gwara ta yi fitsarin a wando ta san a wandon ta yi. Runtse ido tayi saboda yadda take a matse sosai, kawai sai ta fara hawaye cikin matsuwa da rashin mafita. Hango ƙofar gidan Didi take yi daga inda take, kamar wacce aka bawa umarni ba shiri ta kwasa a guje ta afka gidan.

   Kamar a cilla ta ta shiga falon da sallama, idon ta bai faɗa kan kowa ba sai Omar da ya kalli ƙofar yana kallon wacce tayi sallama. Idanunta ne ya faɗa cikin nasa, ga mamakinta murmushi yake yi kuma ganin ta bai saka ya daina ba sai ma ɗauke kai da yayi daga kallon ta.

Didi ganin ta ƙame a jikin ƙofa sai ta miƙe ta ce, "Nayla lafiya na gan ki a firgice haka?." Nayla a wahale ta ce, "Didi fitsari nake ji." Didi ta ce, "maza shiga ki ciki mana" da sauri ta wuce ta shiga ɗakin Didi.

Didi ta koma ta zauna tana kallon Omar da har lokacin fuskarsa a sake take bai yi wani abu da zai tsorata Nayla ba. "Ita wannan yarinyar kullum sai ta shigo ne?." Jin abinda ya ce sai ta ce, "Eh mana, tana sona ne nima ina sonta, tana girmama ni nima ina girmamata." Kai ya girgiza kawai, yana tuna a gaban ta Didi ta dinga yi masa faÉ—a harda cewa zata mare shi.
Chapter 20 · 0% Book details