Sashe 21
Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sallamar Nayla ya saka bai ce komai ba ta fito falon kamar munafuka tana kallon Didi. Didi ta ce, "ƙaraso ki zauna." Zama tayi a tsorace ta kalli Didi ta ce, "Su hajja ne basa nan, ni kuma naje gidan ƙanwar Abiy sai yanzu na dawo." Didi ta ce, "Ayya. To ki shiga kitchen ki zuba abinci in zaki ci."
"Na ƙoshi" ta faɗa kanta yana ƙasa dan har lokacin yana zaune bai tashi ba.
Didi ta kalli Omar da ba su yake kallo ba ya dai hakimce ya ɗora ƙafa kan ɗaya yana kaɗawa. Murmushi tayi tace, "Yayanki Omar ya ci awarar da kika dafa yana ta santi." Nayla ta ɗago tana kallon Didi haka kawai gabanta yake faɗuwa, babban abin mamakin faɗuwar gaban da take ji ta banbanta da irin wacce take ji in ta ganshi. Nayla dai bata ce komai, Didi tayi murmushi ta kalli Omar da yake murmushi sosai da alama akwai abinda ya bashi dariya a wayarsa.
Didi ta ce, "Omar!." Ɗago idanunsa yayi ya kalle ta suka sake haɗa ido da Nayla tayi saurin kawar da kai jin faɗuwar gaban da take ji tana neman wuce tunaninta. Hasken idanunsa kawai take a gani a idanunta, tana mamaki daman idanunsa suna da haske haka ko kuma dan yau ransa ba a ɓace yake ba?.
Muryar Didi taji tana cewa, "itace fa ta dafa awarar da ka gama ci." Bai ce komai ba,
amma yana mamaki meyasa Didi take son saka shi a lamarin yarinyar nan ne? Dan tsabar neman waje irin na Didi wai Yaya Omar, shi kaf duniya babu wanda yake ce masa Yaya.
Wayarsa take ƙara ganin mai kiran sai ya tashi ya fita daga falon. Didi ta bishi da kallo sannan ta kalli Nayla da itama kallon sa take yi Didi ta ce, "Yau kin yi mamakin mutumin naki ko?." Nayla tayi murmushi kawai bata san meyasa ta kasa furta komai ba. Ji take kamar an ɗaure mata baki harshenta ya sarƙe ta saka cewa komai. Didi ta ce, "wallahi ɗazu ya gama yabon awarar ki wai kar na sake kaiwa inda ake yi na dinga yin irinta, yau tsokanarsa nake tayi shiyasa yake ta murmushi."
Nayla ta ce, "abin mamaki, ban ɗauka yana dariya ba." Didi tayi dariya ta ce, "dariya har da ta ƙeta in dai Omar ne, kawai bashi da saurin sabo ne kwata-kwata, amma da zaku saba ke kan ki da kinga canji daga halayensa. Yana da hira sosai in ya so, zaku zauna ku yi hira cikin raha da wasa da dariya. Inda zaku saba murmushinsa bazai miki wahalar gani ba, kafin a saba ɗin ne ana jimawa." Nayla ta girgiza kai kawai ta sake kallon inda ya tashi sai take ji a zuciyarta dama ya dawo ta sake gani yana murmushi.
   Shi kuwa Omar ganin kiran Senator ya saka shi ya fita ya ɗauja da sallama, suka gaisa Senator kamar ko yaushe ya ce, "Tiger gobe Narma zata sauka a Kano, jirginta zai sauka bayana azahar in sha Allah. Akwai wanda na bashi number ka zai kira ka ya kai ka airport ɗin, in ya nuna maka ita sai ka karɓi motar ku wuce. Zan tura maka address ɗin gidan da zata sauka."
Omar ya ce, "Allah ya kaimu."
"Amin. Tiger please kar kayi wasa da wannan lamari, ka kula da Narma kar ka bar wani wanda baka yarda dashi ba a kusa ita. Akwai wanda basa son su ga Narma a Kano, na san baka da wasa shiyasa na zaɓe ka akan police."
"In sha Allah babu damuwa, sai dai in a samu damuwa daga wajanta."
"kar ka damu zan ja mata kunne sosai, in kaga abu ba daidai ba ka kira ni."
"In sha Allah" ya sake amsawa a taƙaice kafin su yi sallama ya kashe wayar.
"Zan wuce" yaji an faɗa daga bayansa muryata na rawa sosai alamun a tsorace take. Juyowa yayi ya kalle ta kanta yana ƙasa jikinta na ɗan rawa kamar wacce aka jonawa lantarki. Didi ya gano fito daga falo ta nufo inda Nayla take tsaye.
Bai ce komai ba kuma bai motsa ba har sai da Didi tazo wajan ta ce, "Omar ka bata hanya mana." Magana yake so yayi amma sai ya fasa ya shiga É—aki Nayla ta fita a guje, Didi tana dariya ta bi bayan ta sai da ta ga ta shiga gidan Hajja sannan ta dawo.
   Tana shiga ta dinga yiwa Salma masifa akan me ta san zasu fita bata faɗa mata ba, Salma ta ce, "Anty bala'i, na kira ki ban samu ba, kuma ba ga shi kin shiga gidan su mai baki tsoro ba?."
"Ke kin san halin da nake ciki da na dawo? Fitsari kamar ya kashe ni bani da zaɓin da wuce na shiga gidan." Salma tayi dariya tana bin ta da kallo ta ce, "ya ban ga fitsari yana bin jikinki ba? Dan na san gamuwar ku dole ki yi fitsarin wando."
Nayla ta ce, "kee abin mamaki, yau bai min komai ba, hasalima da na shiga suna hira da Didi murmushi bawan Allah nan yake yi. Wai daman yana murmushi?." Salma ta ce, "mai zai hana ya yi? Kawai ba kowa yake yiwa bane." Nayla ta ce, "naga alama" ta faÉ—a tana shiga É—aki tana sake hango murmushinsa a idanunta.
Washe gari har rana ta fito Nayla ta kasa mantawa da fuskar Omar yana murmushi, da ta rufe ido shi take gani da lokacin da suka haÉ—a ido hasken idanunsa ya shiga cikin nata ido. GabaÉ—aya ta kasa mantawa da abin ta kwana, tayi-tayi ta manta amma abin ya ci tura.
     Omar kuwa lokacin da driver ya kira shi ko Didi bai sanarwa ba ya fita, ya same shi yana jiransa a mota ya shiga motar suka ɗauki hanyar airport. Mutumin yana ta jan Omar da hira shi kuwa ba amsawa yake ba yayi shiru abinsa.
A cikin airport suka ajjiye motar Omar ya fito ya jingina da motar shima driver ya fito yayi kamar yadda Omar ya yi. Kallon Omar ya yi ya ce, "Abokina sai kayi haƙuri da yarinyar nan bata ji, tana da rawar kai sosai sannan tana da gadara duk abinda yake so shi za a yi mata." Omar ya ɗago ido ya kalle shi mutumin ya ce, "Wallahi sai kayi haƙuri dan bata da kunya ko kaɗan, mulki take ji dashi da isa, hatta buɗe ƙofar mota zata ce kai zaka yi mata. Ga tsawa da kyara kamar waɗanda ta haifa."
Omar ya girgiza kai kawai mutumin ya sake cewa, "Ni ai naji daÉ—i da aka ce wannan karon ba ni zan dinga kai ta inda take so ba, wallahi sai sha biyu na dare zata yi min waya na baro gidana nazo na siyo mata pizza ko shawarma. Ta tara Æ´an mata irinta Æ´aÆ´an manya a gidan suna ihuu kamar ba dare ba."
Omar duk yana jinsa kawai bai san me zai ce masa ba ne, amma duk abinda yake faÉ—a baya tunanin ko babanta zai yi masa shi balle ita. Drivern ya ce, "Abokina gata nan ta fito, Hajiya Narma kenan shugabar masu shigar banza nigeria."
Omar ya ɗaga kai yana kallon inda yake kallo, Narma ya hango cikin atamfa fitted gown ta atamfa ta kama ta sosai ɗakyar take motsawa, mayafi ne siriri ta yafa shi a kafaɗa, hannun rigar gabaɗaya da net aka yi shi hakan ya bayyanar da farin dantsen hannunta, hatta pink colour ɗin bra ɗinta ana gani. Tahowa take fuskar ta ɗauke da baƙin glasess, gabaɗaya ilahirin jikinta a bayyane yake, daga wrist ɗinta zuwa hips ɗinta an kama shi ɗam, a kuma cike sosai. Duk yadda ka kai ga kushe sai ka yabi surar Narma, dan Narma akwai sura ma sha Allah, shiyasa take ɗaukar hankalin maza nan take.
Omar gani yayi wanda suke tsaye ya ƙarasa da sauri ya karɓi trolly bag ɗinta ya saka a bayan mota, sannan ya buɗe mata bayan motar ta shiga. Omar ya bawa key ɗin motar ya ce, "Allah ya fushsheka lafiya mutumina, ni daga nan zan wuce." Omar ya kalle shi ya ce, "na gode. Amma kazo mu je gidan tare ban gane kwatancen ba."
"To mu je" ya faÉ—a yana buÉ—e motar ya shiga shi kuma ya shiga gaba.
Drivern ya kalle ta ya ce, "Hajiya barka da zuwa." Danna waya take yi ta ce, "barka." Bata sake magana ba shima bai sake ba ya kunna motar suka bar cikin airport ɗin. Tafiya suke babu wanda yake magana a ciki su, ƙhamshin turarenta ya gama mamaye motar gabaɗaya.
Wayar Omar ce tayi ƙara ya duba yaga Didi ce ya ɗauka yana cewa, "Na fita zan dawo anjima." Abinda ya ce kenan ya cire wayar daga kunnesa, hakan ya saka ta ɗago kai tana kallon inda Omar ɗin yake.
"kai meye ma sunan ka?." Driver ya ce, "Yahya Hajiya,"
"Waye wannan muna tafiya yana amsa min waya?." Yahya ya ce, "baƙo ne Hajiya, bai san dokokin ki ba."
"Ka sanar dashi" ta faɗa tana cigaba da danna wayarta. Omar bai ma kalle shi ba ya cigaba da danna waya a haka suka isa katafaran gidan da yake cikin nasarawa gra, mai gadi ya buɗe masu ƙofa suka shiga.
Yahya ya fito da sauri ya buɗe mata ƙofa ta fito ya ɗauki jakar ta yabi bayan ta a guje. Omar ya bushi da kallon mamaki dan shi bai ga abu ɗaya da zai iya yi mata ba, daga buɗe ƙofar da ɗaukar jakar. Yana nan tsaye Yahya ya dawo ya kalle shi ya ce, "Abokina wannan matar bata da kunya na faɗa maka, gwara ka ja girmanka, in ba haka ba zata yi maka abinda bazai maka daɗi ba. Ba a waya a mota in tana ciki, ka kiyaye."