← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 54

Sashe 4

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

          Kyakykyawar farar budurwa ce ƴar kiminin shekaru ashirin da huɗu zaune a ƙasaitaccen falo mai kyau da girma tana danna waya. Falon yana da girma sosai ya kuma tsaru matuƙa, kana ganin falon ka san na masu kuɗi ne ba na talakawa ba. Tana da haske da kyawawan idanu da ƙaramin baki mai ɗaukar hankali, tana da ƴar ƙiba kaɗan ba mai yawa ba, yanayin jikin ya dace da ita sosai dan komai ya yi daidai da halittar ta.

Tana zaune tana danna waya fuskarta ɗauke da kyakykyawan murmushin da yake bayyanar da dimples ɗinta, kana kallon ta ka san duk abinda take kallo a wayar yana bata nishaɗi sosai. A yanayin ta zaka hangi tsantsar nutsuwa da kuma fara'ar da take da ita. Hauwer Abdallah Ahmad kenan, wacce ake yiwa laƙabi da NAYLA.

         "Nayla me ki ke kallo haka ki ke dariya?." Juyawa tayi ganin wacce tayi mata magana sai tayi dariya cikin murya mai daɗin saurare ta ce, "Mama ina kallon comady ɗin ƴan TikTok ne. Abiy ya fito?." Wacce ta kira da Mama ta zauna a kusa da ita tace, "Yanzu zai fito."

"Gani na fito." Jin muryar mahaifin nata mafi soyuwa a gare ta sai ta miƙe tsaye tana murmushi ta ce, "Abiy sannu da zuwa." Ya dafa ta ya ce, "Yauwa Mamana. Ya aka yi ki ke nema na?." Zama yayi bayan ya zaunar da ita tana murmushi ta ce, "Ina so daman zan je Kano cikin gari wajan Hajja na yi kwana biyu." Nan da nan annurin fuskar sa ta gushe ya ɗago ya kalle ta ya ce, "Nayla!." Gabanta ya faɗi jin a yadda ya faɗi sunan ta, kasancewar bai cika faɗa ba sai dai ya ce Mamana. Ta kalle shi ta ce, "Na'am Abiy."

"Meyasa ki ke son zuwa Kano ko yaushe? Meyasa bakya son zaman gidan nan?." Nayla ta kalle shi bayan ta rausayar da kai ta ce, "Ba haka bane ba Abiy, waya mu ka yi da Hajja tace min yaushe zan zo shine nace mata sai na kammala nysc. Kuma yanzu Abiy na gama services, tahfiz ɗin ma da na shiga na gama shiyasa nake naje" ta faɗa cikin yanayi na shagwaɓa wanda zai tabbatar da ita ɗin ƴar gata ce.

"Amma kin san bana son zuwan ki Kano ko yaushe ko?."
"Na sani Abbiy, amma Hajja kakata ce tana so na je na dinga gaishe ta. Kuma duk dangin Ummana a can suke, suna jin daÉ—i in naje na gaishe su."

Abiy yayi shiru bai ce komai sai kallon ta da yake yi ganin haka sai ta sunkuyar da kai tana addu'ar Allah ya sa ya barta ta. Abiy ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "zan bar ki ki je amma baza ki jima a can ba, sannan ban yarda da yawo ba." Nan take tayi murmushi mai bayyanar da kyaun ta da ƙuruciya tace, "in sha Allah Abiy. Na gode sosai." Ganin tana farin ciki shima sai ya yi murmushi sannan ya tashi ya yi musu sallama ya fita.

Nayla ta kalli Mama da farin ciki ta ce, "Mama bara naje na fara shirin tafiya Kano." Mama tayi murmushi ta ce, "to sai kin dawo. Sannan kar ki damu da yace kar ki jima, in kika tafi ba sai ya gan ki ba?." Nayla tayi dariya ta ce, "Kuma fa haka ne Mama, bara naje na dawo" ta faÉ—a tana tashi da sauri ta shiga ciki.

Da muguwar harara Mama ta bita bayan ta ja tsaki ta ce, "na rantse da girman Allah sai kin bar gidan nan, yadda uwar ki ta barshi kema sai kin bari. Wannan soyayyar da yake nuna miki sai ta koma ƙiyayya nan ba da jimawa ba. Sai na saka kin zama abin ƙyama a idanun mahaifinki. Irin wahalar da uwarki ta bani a gidan nan sai kin an ninka miki ita a gidan aurenki. Bazan taɓa bari samarin da suke tururuwar son auren ki su aure ki ba, in suka aure ki ai ban yi riba ba, ɗiyar Bilkisu ta rayu a cikin gidan aure mai ɗauke farin ciki bayan ni ta wahalar dani a nawa gidan auren?. Hmmm ai duk wanda ya ci tuwo dani miya ya sha, wallahi sai kin gwammace ba a haifo ki ba. Mu je zuwa Nayla!."

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Tsakanin Narma, Nayla da Omar waye zai amsa KIRAN RABO..?🤩

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t

Book 1
P 02

           Omar ko da ya fita a ƙofar gida ya tarar da yaran sa su uku suna jiran fitowarsa, suna ganin ya fito sa suka miƙe ya ƙaraso cikin su yana kallon su sannan ya ce, "ehmm matan Alhaji Yusuf na wa?." Ɗaya daga cikin su ya ce, "Alhaji Yusuf nan baya?." Ya ɗaga masa kai alamun eh ya sake cewa, "Matar shi ɗaya ce." Omar ya girgiza kai bayan ya saka hannu a aljihu ya ce, "mu je gidan."

Tafiya suka fara yi yana tsakiyar su fuskar nan tashi a tamke matuƙa, babu alamun fara'a a tare dashi gabaɗaya babu damar kawo wasa ko raini a kan fuskarsa. Duk inda ya wuce kallon sa ake yi amma babu damar ayi masa magana saboda kwarjinin da yake dashi.

        "kai Ummaru!."

Aka faɗa daga bayansa ya tsaya cak tare da juyawa dan ya san kaf unguwar mace ɗaya ce ke ɓata masa masa ta kira shi da Ummaru. A hankali ya juya kamar yadda ya yi tunani kuwa ita ce ya sake haɗe fuska ya ƙarasa wajan ta yaran sa suka rufa masa baya ya kalle ta ya ce, "Omar sunana, in baza ki faɗa ba ki ce Tiger."

Ta harare shi ta ce, "bazan faɗa ba, ko zaka saka ni na faɗa ne?. Na faɗa Ummaru." Ɗan kawar da kai ya yi ya ɗan saki fuska kaɗan domin yana matuƙar girmama tsohuwar da babu abinda zai hana bai yi mata warning ɗin da baza ta sake ganganci ce masa Ummaru ba. Hajja ta kalle shi ta ce, "Kwana biyu baka shigowa mu gaisa ko?." Ya kalle ta ya ce, "zan zo."
"Allah ya kawo ka, a daina rashin ji a san an girma dai. Ka gaishe da Aisha mutuniyar kirki."

Bai ce komai ba ya juya suka cigaba da tafiya yana ɗan murmushi jin abinda Hajja ta ce wai a daina rashin ji. Tafiya suke yi har ƙofar gidan Alhaji Yusuf kamar yadda suka yi niya. Ɗaya daga cikin yaran sa ne yayi sallama a ƙofar gida aka amsa daga ciki. Kafin ka ce kwabo mutane sun taru a wajan saboda mamakin ganin Omar a ƙofar gidan a tsaye, wannan dalilin ya saka aka tsaya kallo dan a ga me zai faru.

Alhaji Yusuf ya fito ganin Omar shi kansa sai da gabansa ya yanke ya faɗi dan bai san dame yazo ba. Ya dake bai nuna tsoro ba ya kalli wanda ya yi sallamar ya ce, "Lafiya?." Omar jin maganar sa sai ya ƙaraso yana kallon sa ya ce, "Ka jawa matar ka kunne, kar ta dake faɗar abinda ta faɗa in ba haka ba zata yi dana sani." Alhaji Yusuf ya ce, "me tayi maka?."

"Har gwara ace ni ta taɓa da zata fi zama lafiya, in ka tambaye ta zata faɗa maka. A dai ja mata kunne saboda gudun gamuwa ta gaba" abinda ya ce kenan ya tafi daga wajan. Yaron sa mai suna Tk ya kalli Alhaji Yusuf ya ce, "a ja mata kunne, Tiger gargaɗi ɗaya kawai yake yi. Tunda kaga yazo har nan tabbas Didi aka taɓa, ka tambayi matar ka abinda ya haɗu su zaka fahimta" yana gama faɗa ya bar wajan aka bar Alhaji Yusuf da sakaken baki yana bin su da kallo.

        Kamar yadda ya faɗa cikin unguwar Yakasai suka shiga kasancewar magriba gabato garin a cike yake da ƴan kasuwa da ake dawowa. Har inda ya san ƴan dabar yakasai suna zama suka shiga, kai tsaye ya hango wanda yake nema ya ƙarasa wajan su yana kallon su kamar yadda suke kallon sa. Zama yayi a cikin su yana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya kafin ya kalli babban su ya ce, "Meyasa akuyar ka ta shiga gidana ta cinye min dusa?."

Kallon sa ya yi ya ce, "Tiger ban fahimce ka ba." Tk da yake tsaye a baya ya ce, "Tiger yana magana akan yaron da aka kashe a nan bayan kun kwace wayarsa, É—an arear Tiger ne."

Kallon Omar ya yi ya ce, "Tiger afuwa ban mu san na ku bane da hakan bai faru ba. Ka gan shi nan yanzu maganar ma mu ke yi" ya faÉ—a yana dukan kan yaron. Omar ya kalli wanda aka nuna masa kafin ya dawo da kallon sa ga Jijiya ya ce, "Wanne mataki aka É—auka akan hakan?."
"Babu abinda mu ka yi a yanzu."
"Ya zama dole a hukunta shi! Bazai kashe banza ba, kai ka san bazan ƙyale ba."

Jijiya ya ce, "Haba Tiger duk an zama É—aya fa, kuskure ne kuma baza a sake maimaitawa ba." Ya sauke ajiyar zuciya ya sake kallon Jijiya ya ce, "ya san an zama É—ayan ya kashe rai?."
"Tiger kana da abin mamaki, meye aibu a kashe rai kamar yau aka saba?."
"Ko ku bari hukuma tayi aikin ta ko mu mu yi aikin mu, wanne ku ka zaɓa?." Jijiya ya kalli Tiger ya ce, "yadda ka ce haka za a yi." Omar ya miƙe ya ce, "ku tashi mu je wajan ƴan sanda"

Wanda ya aikata laifin yayi tsiru-tsiru da ido jin ana zancen Æ´an sanda ya kalli Jijiya ya ce, "Haba Jijiya ai ba a yi min adalci ba." Jijiya ya kalle shi ya ce, "Kenan na bar ka da Tiger ya hukunta ka?." Kai ya sunkuyar cikin rashin abin yi, ya kalli Tiger da yake kallon wani wajan daban.
Chapter 4 · 0% Book details