← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 54

Sashe 13

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon na gefen sa ya yi nan take suka taho da wuƙa suka ƙaraso wajan. Omar ya sake kallon mutanen yaga duk sun tsorata gasu kuma manya dan suna cikin manyan unguwar.

Ɗaga musu hannu yayi alamun kar ya ƙarasa inda mutanen suke ya ce, "Maganar da ku ka faɗa a kaina da Didi naji kuma zan ɗauki mataki akan hakan, abinda ya saka bazan iya yi muku komai ba kun girma iyayen wasu ne ku. Ba dan ina jin tsoro ko kunya ba, sai dan haka na yi niya."

Bash ya ce, "Damisa ai in babba bai ji tsoron hawa jaki ba, jaki bazai ji kunyar kayar dashi ba."
"Allah ya baka haƙuri" ɗaya a cikin su ya faɗa yana kallon Omar. Omar zai yi magana wani matashin saurayi ya ƙaraso wajan ya ce, "Baba lafiya?."

Omar ya kalle shi ya kalli wanda ya kira da Baba bai ce komai ba yana jira ya ji ne zai ce. Murya na rawa Baba ya ce, "lafiya lau." Yaron ya ce, "lafiya naga wannan a tsakiyar ku da wuƙa a hannunsa?." Omar Bash ya kalla yayi masa alamun da a kawo yaron, ai kuwa suka damƙe shi aka ɗukar dashi a kusa da Omar.

Cikin takaicin da ya ke ji a zuciyarsa ya fara tsinke fuskarsa da mari cikin tsananin fusata. Ya jawo rigarsa ya kalle shi ya ce, "ku hana iyayen ku yin magana a kaina da rayuwata, in ba haka ba wallahi duk abinda nayi musu ku yi kuka da kan ku." Ya sauke numfashi cikin baƙin cikin da yake ji a zuciyar sa ya ce, "ina yiwa mutum alfarma sau ɗaya tak a rayuwarsa, to na yiwa iyayenka, na ga girman su duk da basu duba girman su ba suke faɗar ko wacce magana a kaina, ina gargaɗin ka da su kansu akan abin yazo ƙarshe daga yanzu, In hakan ya sake faruwa bazan ɗagawa kowa ƙafa ba" ya faɗa yana sakin yaron tare miƙewa zai bar wajan.

"Me ka ke taƙama dashi?." Yaron ya faɗa yana kallon sa." Juyowa kawai yayi bai ce komai ba ya juya ya bar wajan, inda zai je ɗin ma ya fasa dan in ya tsaya wallahi zai iya yiwa yaron kaca-kaca da fuska kawai ya bar wajan yafi alkhairi.

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t

*Book 1*
*P 06.*

      Duk abinda ya faru a kan idanun Nayla da Salma da suka ta dawo daga unguwa aka ajjiye su a farkon layin suka shigo a ƙasa. Sai da suka tabbatar ya shiga gida sannan suka shiga wajan Hajja Salma tana faɗin, "Shi wai wannan bawan Allah babu abinda ya iya sai mugunta?." Hajja ta kalli Salma ta ce, "wa kenan?." Nayla ta ƙaraso ta zauna ta ce, "Waye in ba wannan basamuden na gidan Didi ba, Hajja kin ga yadda ya kama fuskar wani yaro yana mara kamar Allah ya aiko shi?."

Hajja ta ɗan yi tsaki ta ce, "wai a cikin ku Hauwa'u da Salma wacece take son Ummaru ne?." Salma da take shan ruwa sai da ta ƙware jin abinda Hajja ta ce ruwan ya dawo mata ta fara tari. Nayla ta kalle ta ta ce, "Sannu Sis, dole ki ƙware fa, wannan kalami na Hajja sai ya saka zuciyarka ta daina aiki na wucin gadi. Wai so, Allah na tuba meye abin so a wannan mutumin? Sai dai hasken fata."

Salma da ta dawo daidai ta kalli Hajja ta ce, "So fa Hajja?." Hajja ta kalle su ta ce, "bai kai a so shi ɗin bane ba?." Nayla ta taɓe baki ta ce, "ya kai, amma a wajan ƴan jagaliya kamarsa. Da ilimin mu da komai Hajja ki faɗi wannan maganar a kan mu? Wannan ai kamar babban saɓo ne wallahi."

Hajja ta ce, "to tun ɗazu ku ke maganarsa har yanzu kun kasa dainawa, wanda ake so shi ake yawaita magana a kansa ai." Nayla ta kalli Salma suka ƙyalƙyale da dariya Nayla ta ce, "Shi tantirancin sa ne ya saka mu ke magana a kansa, kuma abin alfaharin sa ne ma mata masu class kamar mu suna maganarsa. Batun so kuma Allah ya tsari gatari da saran shuka, Allah na tuba ya wuce na zaunar dashi na koya masa karatu?. Wai a taƙaice ma yayi makaranta kuwa? Dan irin su wallahi basu cika karatu ba, addini ma gararar su yake yi."

           Hajja ta murmusa kawai bata ce komai ba Salma ta ce, "to ina ya ga lokacin yin wani karatu kullum ana yawo da wuƙa? Kuma wallahi laifin ƴan unguwar nan ne da ba a samu wani shegen da yafi shi hauka ya koya masa hankali bane shiyasa yake abinda ya ga dama. Haka kawai ya kama mutum yana zabga masa mari ga iyayensa a zaune." Hajja ya ce, "na faɗa muku Omar bashi da matsala, kuma tunda ki ga haka ɗayan biyu ne, in ma an zagi mahaifiyarsa ko kuma an yi magana mara daɗi akan Aisha."

Hajja ta kuma cewa, "kun san mutanen hausawa da wani banzan tunani, tunda Aisha bata taɓa aure ba kuma suna zaune gida ɗaya da ƙaninta shikenan ake musu kallon ƴan iska. Majalisar maza ake zama ana dasa gulmar su wai neman junan su suke yi." Nayla ta buɗe idanu ta ce, "a'uzubillahii! Kaji wani jahilci don Allah."

Hajja ta ce, "Wannan maganar ba baƙuwa ba ce ba a unguwar nan, sau da yawa za a zo neman aurenta amma da wanda yazo neman auren ya
tafi shikenan bazai dawo ba an je an zuga shi an ce ai tana bin ƙaninta suna lalacewa a gida. Jinkirin aure bashi da daɗi, dan babu yadda zaka canja ƙaddararka ne amma wanda yake cikin irin yanayin shi kaɗai ya san halin da yake ciki. Aisha kam tana ganin jarabawa, wanann ya zo sai an fara abu kamar na kirki sai a watsar, gobe ma wani yazo shima ya gudu."

Salma cikin tausayi ta ce, "Allah sarki Didi! Amma duk masu faÉ—ar wannan kalami mai munin tsiya ba su yi mata adalci ba, kuma sai Allah ya yi musu hisabi."

Hajja ta ce, "tunda ku ga yana wannan hukuncin daƙyar ba maganar yaji suna yi ba, dan shi zaki iya zagin shi ya wuce ki amma kar ki taɓa Aisha, sonta yake kamar ya bata ran da yake dashi ta haɗa da nata, saboda Aisha itace kamar uwarsa da ubansa."

Nayla ta ce, "gaskiya indai haka ne yayi daidai wallahi, in ma ƙara ya kai su gaban hukuma ai daidai ne. Wannan wanne irin ƙazafi ne mai baƙin muni haka?." Salma ta dawo kusa da Hajja ta zauna ta ce, "Hajja to ina ƴan uwan su ne?." Hajja ta kalli Salma ta ce, "ke bacci nake ji, in Allah ya kaimu gobe na baku labarin asalin su Aisha da Ummaru." Nayla ta ce, "kai Hajja ki faɗa mana yanzu mana." Hajja ta harare ta ta ce, "yanzu da nace wata tana sonsa cikin ku sai kuka ce a'a, in ba so ba meye na son jin labarinsa?."

Nayla ta gimtse fuska ta ce, "Hajja ki daina kawo batun nan ko da wasa don Allah, kawai muna so mu sani ne ba dan wai wani abun ba. So ki ke Daddy yaji labari ya zane mu?" Ta faɗa tana kallon Salma suka ƙyalƙyale da dariya. Hajja tunda taji sun ce Daddy ta san mahaifin Salma suke nufi babban ɗanta kenan. Hajja ta ce, "ko shi daddyn in ɗaya tana son Umar ɗin ina ruwansa?."

Salma ta wara idanu ta ce, "Maza ki yi istigifari Hajja, dan wannan babban saɓo ne." Hajja tayi dariya ta girgiza kai ta ce, "Ni ko labarin gidan Daddyn ma baku bani ba, kun shigo kuna yi min hirar saurayin Hauwa'u" ta faɗa tana kallon Nayla da tsokana.

Nayla ta ce, "Hajja ki daina cewa saurayina, saurayina yana Kaduna ba a Kano yake ba. Sannan ba sunana Hauwa'u ba Hawwa nake, ki dinga cire u É—in nan don Allah."
"Bazan cire ba, Hauwa'u zance, Kuma na faɗa Umar saurayinki ne." Nayla rai ta ya ɓaci amma ganin Hajja tsokanarta take yi sai tayi dariya suna hira da Salma dan Hajja ya shiga ɗaki.

        *Kaduna.*

Abiy da Mama a zaune a falo, Abiy yana cin abinci Mama na gefensa ganin ya kammala cin abincin sai ta kalle shi ta ce, "É—azu Nayla ta kira ni, na ce mutanen Kano ya Hajja." Abiy ya murmusa ya ce, "nima daga dawowa ta gidan nan zuwa yanzu sau biyar ta kira ni, Ai naga alama tana son zama wajan Hajja sosai."

Mama ta yi murmushi ta ce, "itama Hajjan tana matuƙar jin daɗin zama da Nayla ai, kasan Nayla ba dai hankali da iya magana ba." Abiy ya murmusa kawai bai ce komai ba kafin ta ce, "Kwana nawa ka bar ta yi ne?."
"Sati É—aya."
"Haba Abiy, ina laifin ka barta tayi sati uku tunda dai ta kammala service É—inta kuma baka samar mata aiki ba. Tahzif É—in da ta shiga ma ta kammala tana gida a zaune. Hajja na son zaman ta a can, ita take É—auke mata kewar mahaifiyar ta da ta rasa take kallon Nayla tamkar Bilkisu."

Abiy ya kalle ta ya ce, "Bana son zaman ta a Kano ne gabaɗaya, kar ki manta abinda ya so faruwa da ita a shekarun baya, ba dan Allah ya kiyaye ba da an cutar da ita. Tun daga nan zaman ta a Kano ya gama fita daga raina, da ina da iko ma ko kwana ɗaya baza tayi a can ba, to ban isa na rabata da dangin mahaifiyarta da suke can ba. Kuma suna tsananin son Nayla da ƙaunar ganinta, dole ne na barta ta je gare su."

"Na sani Abiy, Amma ai komai ya wuce kuma yanzu Nayla ai tana da hankali da wayon da abinda ya faru a baya bazai faru yanzu ba sai dai ƙaddara. Hajja tana sonta, tun farko ta nuna maka ka bar mata Nayla kawai dai ka ƙi ne. Kuma suma sun yi mana kara a kanta sosai."
Chapter 13 · 0% Book details