← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 54

Sashe 26

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Narma kuwa tsaf ta shirya cikin riga da siket ɗnkin straight siket, ya kamata sosai ɗakyar take jefa ƙafarta saboda yadda ya kamata, ta yafa mayafi babu laifi ta saka da ɗan saka mai girma amma chantily ne gabaɗaya ana ganin jikinta. Wayarta taji yana ƙara ta duba ganin mai kiran sai ta ɗauka aka yi mata magana ta kashe ta ɗauki wayar ta ta sakko daga saman.

Harabar gidan ta fito duk ma'aikatan gıdan suka ƙarasa suka gaishe ta maza da mata, shi kam yana zaune abin sa gefensa Tk shida kunama. Kallon agogo ya yi yaga saura mintina biyar a lokacin da ya bata ya tashi ya tawo wajan Tk da kunama suna take masa baya, ya buɗe motar ya shiga ya yi mata key bai ce mata komai ba.

Narma sai da gabanta ya faɗi ganin yanayinsa a yau ya saka taji wani iri a zuciyarta, gudun kar abinda ya faru jiya ya faru ya saka ta buɗe bayan motar ta shiga Tk ya shiga gaba shi kuma ya ja motar suka fita. Ƙhamshin turarenta ya gama cika motar, ga ƙhamshin mai daɗi da tsayawa a rai bai ce mata komai ba itama bata ce masa komai ba.

"Tk."
"Allah ya ja da zamanin Madugu."
"Ina ne Arewa24?."
"Nan gaba ne babu nisa." Bai sake magana ba ya cigaba da tafiya Tk na nuna masa.

Yadda ya furta magana ta biyu sai ta kalle shi tana mamakin wai shine ya yi maganar ko ba shi ba, ganin shi ne yake maganar sai ta girgiza kai tana tunanin anya wannan É—an daba ne kamar yadda Dad yake faÉ—a? Anya shine Tiger É—in da ake faÉ—ar tsagerancinsa a duniya?. Kai gaskiya da sake tana tantama akan sa.

A bakin gate suka tsaye ta kalle shi kamar zata yi magana sai kawai ta fasa dan so take taga iya gudun ruwan sa. Fita tayi ta shiga ciki kamar yadda bata yi magana ba babu wanda ya kula ta.

Suna zaune shi da Tk duk da ba magana suke yi ba kowa harkar gabansa yake yi, shiru babu ita babu alamun ta kusan mintina talatin. Agogo ya kalla ya ga sha biyu na rana har ta kusa ya sake kallon inda ta shiga ya yi tsaki. Mintina goma ya ƙara mata in bata fito ba zai yi tafiyarsa ai ba driver bane ba shi da zata ajjiye shi a waje bata fito ba.  Ita kuwa an jima da gama interview tana sane tayi banza dashi tana so taga ƙarfin iskancin sa shiyasa tayi zaman ta.

Gajiya tayi da zaman ita kanta, bacci take ji hakan ya saka ta fito a lokacin ya kunna motar zasu bar wajan kenan. Ganin ta fito ya saka shi ya dakata ta buÉ—e ta shiga tana cewa, "wai da ban fito ba kenan tafiya zaka yi?." Tk ya ce, "to Damisa yaron ki ne da zai zauna yana jiran ki?." Narma ta ce, "kai ba da kai nake magana ba, kayi min shiru kafin na É—auki mataki akan ka."

"Mataki akan wa? Wai ni Tk? Gaskiya....." Kallon sa Omar yayi hakan ya saka ya ce, "Tuba nake Madugu ta zo ta rainin hankali ne." Narma ta zo iya wuya saboda ɓacin rai cikin masifa ta ce, "Kai wai waye kai? Me ka ke dashi da ina magana zaka yi min banza?. Me ka ke dashi da zaka tafi ka barni a kan titi iyeee!" Ta faɗa da ƙarfin gaske wanda hakan ya saka Omar taka burki da ƙarfi.

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 12.*

Yadda ya taka burki da ƙarfi sai da tayi gaba kamar zata kifa kafin ta koma daidai ta zauna, ya jiyo ya kalle ta suka haɗa ido bata ɗauke idonta shima bai ɗauke ba ya ce, "in kika sake yi min magana a motar nan wallahi sai kin sauka, ki aikata ki gani." Mamaki yake bata da tsoro, ita da motar gidan su shine yake cewa in ta yi wani abun ba daidai ba sai ta sauka? Lallai wannan anyi ɗan rainin hankali, rainin hankali mana, in ba haka ba ita zai kalla ya ce in bata yi shiru ba sai ta sauka daga motar da babanta ya siya.

Sai kuma ta kasa magana tayi shiru ya cigaba da jan motar yana aiyana wallahi in ta sake masa magana sai ta fita daga motar sai dai ta hau abin hawa ta koma. (Omar akwai ƙarfin hali).

A haka suka koma gida motar tsitt babu wanda yake magana a cikin su sai ƙhamshinta da ya cika motar gabaɗaya. Yana tsayawa a gidan ta buɗe motar ta fita, ta kalle shi bayan ta fita shima ya fito ta ce, "zan ga abinda ka ke taƙama a duniyar nan, zan ƙure maka gudu, zaka fahimci ni ba sa'ar wasan ka bace ba." Tk ne ya zabura ya yi kanta Omar ya ɗaga masa hannu alamun ya ƙyale ta, ya juyo ya kalle ta ya ce, "cigaba."

Wani irin baƙin ciki ya zo ya tokare mata a maƙogwaro, kenan ya mayar da ita shashasha mara hankali kenan ta cigaba da magana mahaukaciya. Juyawa tayi a fusace ta shiga cikin gidan ta cillar da mayafin jikin ta a haukace. Wayarta ce tayi take ƙara ganin sunan Ashraf ya saka bata ɗauka ba ta tashi ta hau sama a guje raina a ɓace matuƙa.

Da wannan ɓacin ran tayi sallah sannan ta yi wanka ta kwanta bacci zuciyarta nayi mata saƙa da kwancewa akan abinda zata yiwa Omar dan ta huce. Bata farka ba sai bayan la'asar, ta tashi ta sake sabon wanka ta sako riga da wando na shan isaka ta sakko ƙasa da niyar cin abinci. Kamar yadda ta zata mai dafa mata abinci ta dafa abinci ta ajjiye, ta a dining table zauna ta zuba abinda take so ta fara ci.

Wayar ta ce ta sake yin ƙara ganin mai kiran sai ta ɗaula ta ce, "ina ciki." Abinda tace kenan aka yanke wayar ba jimawa aka shigo falon.

Kyakykawan saurayi ne fari tass siriri mara jiki ya shigo yana kallon ta daga inda take zaune tna cin abinci. Kallon sa tayi sai ta miƙe ta ɗauko plate ɗin abincin ta shigo cikin falon tana cewa, "Welcome Baby." Ƙare mata kallo yake yi dan shigar da tayi ta yi masa kyau a idanunsa sosai. Surar Narma tana daga cikin abinda yake ɗaukar hankalinsa a kan Narma, duk lokacin da zai yi arba da ita sai yaji shauƙin son kasancewa da ita cikin yanayi na soyayya. Ya so hakan ya kasance tsakanin su amma taƙi ba da haɗin kai, da ya yi magana sai ta ce ya jira sai bayan auren su, shi kuma gani yake kamar bazai iya jurewa ba.

Ɗan hugging ɗinsa tayi daga gefen kafaɗarsa kana ta zauna a akan kujera ta ɗora ƙafa kan ɗaya tana cigaba da cin abincinta. Zama Shima ya yi yana kallon ta cikin yanayin da ya ke kasancewa da duk lokacin da suke tare, yanayin sa na sake yin gaba in ta yi hugging ɗinsa ko ta yi masa kiss sai ya ji kamar zai zauce. Ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce, "What wrong? Naga fuskarki da alamun damuwa."

Yatsine fuska tayi ta ce, "Wani banzan driver Dad ya haÉ—a ni dashi yake raina min hankali, wai ni yake É—agawa murya har yana cewa in na sake magana sai na fitar masa a mota." Ashraf ya ce, "Like Seriouly? Ke É—in yake faÉ—awa haka?." Bata amsa ba sai murmushin takaici da tayi tana girgiza kai.

"Waye shi haka?."
"Wani É—an iskan mutum ne dan daba wai shi tiger, ni yake yiwa tsawa saboda Dad yana son ya dinga kai ni ko ina nake so."
"Kuma Dad É—in ya san da haka?."
"Yes he knew, but today i won't inform him, i want to take action independently and how him my capabilities." Ashraf ya ce, "That's good my Love, you should teach him a lesson so he understands you deserve respect and won't tolerate any nonsense."

Kallon sa tayi taga yana kallonta ba, iya fuskarta yake kallo ba duka jikinta yake kallo sai tayi murmushi ta ce, "zan koya masa hankali."
"Nima zan taya ki." Murmushi tayi tana kallonsa  tace, "yaushe ka zo Kano?."
"ÆŠazu." Kai ta girgiza ya ce, "yaushe zaki fara event É—in Samra?."
"Lahh ka tuna min, gobe ne fa, ko makeup artist ban nema.

He looks into her eyes yana wani lumshe ido then he say, "My Narma event without makeup you looks magnificent." Tayi murmushi ta ce, "Duk da haka dai zan yi kwalliya." Ya bita da kallo ta É—auki waya ta kira tana magana da turanci nan da nan ta yi booking makeup artist za a zo har gida ayi mata home service.

Ashraf ya jima suna hira kafin ya tafi dan shima a gajiye yake ya tafi ya huta da niyar in anjima zai dawo. Narma bayan ya tafi sama ta hau ta buɗe balcony gidan tana kallon ma'aikatan gidan ɗaya bayan ɗaya tana mamakin rashin ganin Omar, wato ko ya taimaye ta ya ji babu inda zata je shine yayi tafiyar sa kamar itace take aiki a ƙarƙashin sa. Wayarta duba taga number sa Dad ya turo mata kawai ta dubawa number ido kafin ta girgiza kai tare da yin tsaki ta koma cikin falon.

      Omar kuwa ko da suka bar wajan shi da Tk ba gida suka koma ba sai da suka je wani wajan bai koma gida ba sai bayan la'asar. Yana shiga kai tsaye wajan Didi ya shiga, ya same ta a zaune tana shan magani ya ƙarasa ya zauna ya ce, "Ya jikin?." Ta kalle shi ta ce, "Jiki da sauƙi sosai, na sha magani." Ya girgiza kai ya ce, "kin tabbatar babu abinda yake damın ki?." Ta ɗaga kaii alamun eh.
Chapter 26 · 0% Book details