← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 54

Sashe 43

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wannan tunanin ya ce, "kina ji.....!" Baya tayi tana kuka kamar wacce ta rasa hankalinta ta ce, "ba wasa nake maka ba, ba ƙarya nake maka ba, ba yaudararka nake ba, ba plan na shirya maka ba. Wallahi Ina sonka da gaske ba da wasa nake ba. Dama ana cire zuciya da na cire zuciyata na nuna maka abinda nake ji a kan ka. From the moment i saw you in our house fell in love with you, saboda zuciyata bugawa ta dinga yi da na ganka, na ɗauka kwarjini kayi min a lokacin, amma a yanzu na fahimci sonka nake yi. I'm not joking about my feeling, it's not a game or drama or whatever you think about it. I truly love you" ta haɗe hannayenta waje ɗaya ta ce, "Please believe me" ta faɗa tana zubewa a wajan tana kuka sosai.

Kama ƙugu Omar ya yi yana kallon ta, wai shi Omar wata mace take ɗuke a gabansa take kuka da sunan tana sonsa. Ya kasa banbance yanayin da yake ciki, tausayinta yake ji ko haushi take bashi shi kam bai sani ba. Bugawar zuciyarsa yake ji na tausayinta ne ko na meye dai shima ba sani ba.

Ba ya so Didi ta dawo ta tarar da ita a wannan yanayi, hakan ya ya buɗe baki zai yi magana amma ya kasa. Shi bai san ya ake rarrashin mace ba har ta daina kuka, bai taɓa ganin kukan mace a gaban idanun kamar haka ba sai a wannan lokacin, bai san ta ya zai fara ba kwata-kwata. Ya sake kallon ta ya ce, "ki bar kuka ki tashi daga wajan nan."

Bata daina kukan ba amma ta miƙe tsaye ya ce, "na ce ki bar yi min kuka bana so!" Ya faɗa cikin tsawa kaɗan wacce ta sakata haɗɗiye kukan nata. Ya kalle ta ya ce, "Yanzu ki je gida zan zo zamu yi magana anjima."

A sanyaye ta ce, "ka tabbatar zaka zo?." Ya É—aga mata kai alamun eh. Ta kalle shi ta ce, "in ma baka zo ba zan dawo, Ina so naji amsar ka akan abinda na faÉ—a maka. Bazan koma Abuja ba sai na ji amsar ka." Bai ce komai ba sai cize bakinsa da ya yi, ya kalli fuskarta ya ga ta koma ja sannan da gaske ta É—an rame kaÉ—an.

Wuce shi tazo yi ta sake kallon shi ya ce, "Faruk ka kawar da duk tunanin da ka ke yi a kaina, da gaske nake Ina sonka." Kulle ido ya yi ya buɗe sai yaga ta bar wajan da alama ta fita. Ƙarasowa ya yi ya ganta ta fita a guje ta ƙarasa mota ta shiga ta ja motar da ƙarfin gaske.

"Wai ni za a yaudara" ya faɗa a bayyane bayan motar ta fice daga layin. Sai kuma kalamanta suka dinga dawo masa cikin kansa ya kulle ido ya ce, "ni dai ba sonta nake yi ba, kawai na kasa mantawa da tunanin ta ne. Wannan film ɗin da tazo ta shirya kuma duk zai ƙare."

"Kai kuma kai da wa ka ke magana kai kaÉ—ai?"Didi ta faÉ—a tana shigowa gidan.

Da sauri ya buÉ—e ido ya kalle ta ya daidaita nutsuwarsa kana ya ce, "kin dawo?."
"Eh na dawo" ta bashi amsa tana wucewa bata ce masa komai ba. DaÉ—i yaji da ta bata tarar da Narma ba da bai san me zai ce mata ba.

Bai shiga inda take ba ya koma É—aki yana tunani kala-kala akan abubuwan da suka faru wanda yake kallon sa kamar a mafarki, tsaki ya yi kawai cikin tunanin da ya rasa wanne zai kama ya yi.

Didi bata sake ganin sa ba sai bayan sallar magriba ya shigo cikin gidan. Duk da yadda yaso ɓoye abinda yake ransa sai da Didi ta fahimta. Ta kalle shi sosai ta ce, "lafiya ka ke kuwa?." Ya girgiza kai ya ce, "lafiya lau." Bata ce komai ba ya zauna yana kallon ta yana ji kamar ya faɗa mata yaji me zata ce, amma kuma yana ji kamar ba sai ya faɗa mata ba yaudara ce kawai ake so a shirya masa.

Didi ganin yana kallon ta kuma bai yi magana ba sai ta ce, "ya dai?." Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Didi a misali namiji kamar ni wacce irin mace ce zata iya cewa tana sonsa?." Didi da mamaki ta ce, "kamar ya kenan?."

"Ina nufin ko wacce mace ma zata iya son namiji kamar ni?." Didi ta ce, "ita soyayya ai baka sanin lokacin da ka ke fara ta Omar. A yadda ka ke a haka in ƙaddarar soyayya ta gifta sai ka fara son ƴar gwamnan garin, kuma so bana wasa ba na gasken gaske, kuma dai kaga a zahiri ka san tafi ƙarfinka amma soyayya bata duba wannan Omar. Ko kuma ita ƴar gwamna ta fara sonka so mai tsananin gaske, so na gaskiya ba wai na wasa ba, saboda ba ita ta yi sonka a zuciyarta ba Allah ne da kuma taimakon zuciya. To soyayyar ce yanzu duk ta gaskiya ta gushe sai dai sama-sama, kafin a samu soyayyar gaskiya a yanzu an samu ta ƙarya sau dubu, kuma da yawa yaran manyan mutane yanzu ƙwarya tabi ƙwarya ake yi, me ka kai me za a kawo maka. A dah dai ɗan mai kuɗi ya auri ƴar talaka, ƴar mai kuɗi ta auri talaka kuma an zauna lafiya. Amma yanzu wannan zamani ya gushe Omar."

Yayi shiru jin kalaman Didi sai ya kalle ta ya ce, "misali ace ƴar mai kuɗin unguwar nan ta ce tana sona zaki amince da gaske takr?." Didi ta yi dariya ganin da gaske yake maganar sai bata saka wasa a ciki ba ta ce, "zan amince mana Omar, ai ba ita ta halicci kanta ba, kuma ba ita ta saka son naka a zuciyarta ba, babu yadda Allah baya tsarawa ɗan adam ƙaddara da rabonsa. Allah ne  ya kaddara hakan kuma babu wanda ya isa ya canja faruwar sa. Kuma da yawa in yaran masu kuɗi mata suka fara soyayya da wanda bai kai matsayin su ba yawanci soyayyar gaskiya ce, saboda mata rauni gare su, soyayya tana saurin kama zuciyarsu."

Shiru ya yi kawai bai ce komai ba yana tunanin kenan dai da gaske Narma zata iya fara sonsa ko dai hasashen Didi ne kawai?.

Didi ta ce, "kai dai ka bar so kawai Omar, nima ba wai sanin soyayyar na yi ba, amma so babban abu ne. Kai ta addu'a Allah kar ya ɗora maka son wacce tafi ƙarfinka, daga lokacin da ka fara son wacca tafi ƙarfinka daga lokacin zaka san meye azabar so. So ai mugun abu ne wani lokacin."

"Ni ai Didi na faɗa miki bana tunanin akwai wacce tafi ƙarfina a duniya, in har akwai ɗin sai dai in bata sona." Didi tayi dariya tana jinjina maganar sa ta ce, "ko tana son naka iyaye da ƴan uwa sai sun dakusar da soyayyar."

Ya yi shiru bai ce komai ba yana É—an girgiza kai ba dan ya yarda ba. Disi ta ce, "wai me ya kawo wannan maganar ma yau?."
"Zan faɗa miki" ya fɗa  yana tashi ya fita ya barta da tunani dalilin yin wannan maganar, ita da ta san baya magana akan soyayya, ko akan mace baya magana balle irin wannan ta soyayya. Ko tsokanarsa ta yi wani lokacin ko tanka mata baya yi, amma tunda ta ji ya yi wannan maganar tabbas akwai dalili.

        Yana fita yaga message ɗin Narma ta rubuta, _Daman na san baza ka zo ba, in na rasa raina kaine sila Faruk! Da Ina da iko da na cire son da make maka tuni na ajjiye shia a gefe. Amma babu komai na gode._

Sai yaji wani irin abu ya tsirga masa mai kama da tausayi sosai, ya sauke ajiyar zuciya yana jin zuciyarsa na bugawa sosai cikin rashin sanin dalili. Shi dai bazai je inda Narma take ba gaskiya, in ya je dagula masa lissafi zata yi ya rasa abinda zai ce mata gwara ya ƙyale ta in ta gaji ta koma gida.

"Kenan in da gaske so na take su masu kuɗi babu ruwan su da cewa in mace ta fara cewa tana son namiji zubar da aji ne? Tunda gashi tun daga Abuja ta ɗauko ƙafa tazo Kano saboda ta furta min tana sona. In kuma yaudarata take yi ta taro match wallahi, za tayi dana sanin aikata abinda ta aikata. Amma taya zan gane soyayyar gaskiya ce ko ta ƙarya?." Shafa kansa yake yi ya kasa gane inda zai kama dan ya kamo bakin zaren.

"To wai ni me nake ji a kanta?" Ya faɗa yana shafa ƙirjinsa daidai inda zuciyar take, yana jin wani irin abu yana fizgarsa daga ta ciki. Da wannan tunanin ya kwanta yana ta juyi ya rasa abinda yake damun sa.

        Narma yanayin ta babu daɗi, raba dare tayi tana kuka zuciyarta ma bata shawara kala-kala, har shawarar kashe kanta tayi ta fasa, tayi shawarar fita taje gidan su Omar ta kasa. Ta jima tana kuka daƙyar ta samu bacci ya ɗauke ta.

         Ya jima yana bacci har goma na safe sannan ya tashi, bai fito ba sai da ya yi wanka jikinsa duk a sanyaye yake ya rasa abinda ya kamata ace ya yi. Lokacin da ya shiga wajan Didi ta idar da sallar walha ta kalle shi ta ce, "yau ka sha bacci, da fari na ɗauka ka fita ashe kana nan." Ya girgiza kai ya ce, "na jima ban yi bacci ba ne jiya, daƙyar na iya tashi sallar asuba."

Didi ta ce, "ga idanunka nan har yanzu da sauran bacci. Ga abinci can in zaka ci." Ya girgiza kai ya ce, "bana son cin komai gaskiya."
Chapter 43 · 0% Book details