← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 54

Sashe 35

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Narma kallon sa take yi shi kuma bai yi magana ba kuma bai zauna ba, kuma koma inda ya fito ba. Narma kallon sa take yi kafin ta ce, "Yayan ki ne?." Didi tayi dariya kaɗan ta ce, "kusan hakan, tunda ya fini tsaho da suffar manya, Yayana ne." Narma ta kalle shi a lokacin ya kalli Didi ya ce, "ina abincin su?." Didi ta san su wa yake nufi sai ta ce, "yana nan, ka jira na sallami baƙuwa sai na ɗauko maka ko?" Ta faɗa tana harararsa ganin ko kula ta bai yi.

Komawa ya yi ya bar falon bai ce komai ba, to me zai ce? Shi sam bai iya magana da baƙi ba, kuma ga gidan na su ba baƙi ake yi ba ko yaushe shiru babu mai zuwa, shi kuma damn ya son baƙi, shiyasa bai iya magana da baƙo a cikin gidan ba.

Bayan ya fita Didi ta ce, "in baƙi sun zo sam baya sakewa, sai ya yi ya abu kamar yaro." Narma tayi murmushi kawai bata ce komai ba dan taji haushin ƙin kula ta ɗin da ya yi. Ai ko babu komai tunda har ta tako har gidan su ta zo ya kamata ko hello ya ce mata.

Didi ta ce, "na jima ina bibiyarki a instagram, ko yaushe cikin fegin ki nake har Omar ya gane ya kan ce ke dai kina son yarinyar nan. Yadda ki ke tsayawa ƙananun yara musamman akan fyaɗe yana min daɗi sosai." Narma ta ce, "na gode" ta faɗa tana murmushi kaɗan.

Miƙewa tayi ta kalli Didi ta ce, "zan koma, dama nazo na duba ki ne." Didi ma ta miƙe tana yi mata godiya har bakin mota ta rako ta. Narma ta yiwa motar key ta buɗe mazaunin driver ta shiga tana sake kallon gidan ko zata ganshi, babu shi babu alamunsa duk sai taji babu daɗi ita ba haka taso ya faru ba.

Ajiyar zuciya tayi ta kunna motar amma taƙi tashi tana neman yi mata yadda tayi mata har aka ƙwace mata waya. Tsaki tayi ta fito daga motar a lokacin ta hango shi sai ya ƙaraso ta bashi hanya ya shiga gaban motar, yana shiga ya kunna sai ta tashi ya zauna bai fito ba. Zagayawa tayi ta buɗe gaban motar ta shiga tare da saka seat belt shi kuma ya ja motar yana mamakin dalilin shigar ta gaba maimakon baya mazaunin ta.

Tafiya suke bai bari ya kalle ta ba dan kallon ta yana yi masa illa a jikinsa, sanye take da kayan bacci riga da wando masu santsi rigar tana da tsaho tazo har guiwa amma ƙaramin hannu ne da ita. Sai wandon da yake dogo har ƙasa ta yafa mayafi ƙarami a kanta.

Har suka je gidan bai ce mata komai ba sai da ya tsaya sannan ya ce, "mun gode." Cikin shagwaɓa ta ce, "Sai yanzu zaka ce? bayan har gidan ku naje ko ka kula ni? Ina tausayin mara lafiya kuma sister ka ce shiyasa naje gaishe ta amma kayi min banza kamar baka sanni ba. Da na sani ban je." Yadda take maganar sai da ta saka shi yin ajiyar zuciya, ya kalle ta yaga shi take kallo ya ce, "mun gode" ya sake faɗa yana janye ido daga kanta.

"Amma sai yanzu ka ce, ko magana fa baka yi min ba." Shiru ya yi dan bai san me zai ce mata ba kuma, ita kuma ta kafe shi da ido tana mamakin abinda take aikatawa amma umarnin zuciyar ta kawai take bi.

Shiru ya ratsa motar kafin ya kashe motar ya ce, "zan koma" ya faɗa yana ƙoƙarin buɗe ƙofar.
"Baza ka bani haƙuri ba?" Ta faɗa tana kallon sa da narkakkun idanunta. Kallon ta ya yi zuciyarsa na bugawa sosai, ya tsaya cak da buɗe ƙofar kamar an hana shi ya sauke ajiyar zuciya yana dana sanin biyo ta ma da ya yi.
"Sai da safe" abinda ya ce kenan ya buÉ—e motar ya fita dan ya ga so take ya tarwatsa masa tunani.

Narma ta bishi da kallo ta kwanta a kujerar motar tana sauke ajiyar zuciya cikin sabon yanayin da bata san daga ina yake zuwa ba. Haka kawai taji tana son ganin sa shiyasa ta tashi zuwa gidan su, ganin na sa da tayi sai taji kamar wani sabon yanayin wanda yafi na ɗazu tsayawa a rai da shauƙi a ranta. Ta kwashe mitina goma a haka kafin ta buɗe ƙofar ta fito bayan ta zare ɗin ta shiga cikin gida.

Kiran Dad take gani yana zuwa video call ta zauna a falon ta É—auka tana kallon sa ta ce, "Hii Dad."
"Hiii Baby, how was your night."
"It was fine.."
"Good. Yaushe zaki dawo ne?." Narma ta É—in yi jim kafin ta ce, "maybe next week." Dad ya ce, "no, kin shirya ki taho Monday."

Cikin shagwaɓa ta ce, "Dad ina son zaman Kano sosai."
"Dole ki dawo akwai aiki a company da yake jiranki kin manta ne?." Shiru tayi tana tura baki gaba kafin ya ce, "kin fita ne?."
"Yes Dad, naje gidan su Tiger sister shi babu lafiya na gaishe ta."

Dad ya wara ido ya ce, "What? Kin je gidan su Tiger?." Narma ta ce, "Yeah, yanzu ya dawo dani."
"Kina cikin hankalin ki kuwa?." Shiru tayi bata ce komai ba Dad ya fara faÉ—a ya ce, "meye haÉ—inki dashi da zaki je gidan su gaishe da sister shi? Waye na ki? He's just your driver not your friend. Wai what is your problem ne Narma? Ina hankalinki ya tafi ne?."

Ganin yadda Dad ya ke faÉ—a sosai sai ta ce, "I'm sorry Dad, kawai naje ne saboda bata da lafiya sosai, sannan...." Dad ya katae ta ya ce, "Then what? Narma Tiger is not your mate, na faÉ—a miki reasons É—ina na barin ki tare dashi ba wai dan ya kai matsayin ya zauna É—in bane. Aikin sa ya kula da lafiyarki na biya shi, ba dan ki ji gidan su im wani babu lafiya ba. Ke ko mutuwa ya yi matsayin kin wuce ki je gaisuwa kin gane?."

Narma ta ce, "Dad ka san ina tausayin mara lafiya shiyasa."
"Na sani, na san halin ki na tausayi mara lafiya amma ba irin famliyn Tiger ba. Wanda yake daidai dake ko ya fiki matsayi shi zaki tausayawa ba shi ƙasƙantacce ba. Aikin driving ɗin ma da ya samu daga gare ni ina da dalilina, ke kin san da ko mai gadin gidan da ki ke bai isa ya zama ba."
"Is okay, I'm sorry."
"Sorry for yourself. Dan haka ranar Monday ki siyo ticket ki dawo gida. Ki zo ayi maganar auren ki kawai, akwai mutane da yawa suke so su aure ki." Narma ta ce, "Okay."
"Ki je ki ci abinci sannan ki kwanta." Ta sake amsawa sannan ta kashe wayar tana turo baki ta hau sama. Shirin kwnaciya tayi amma babu bacci a idanun ta hakan ya saka ta tsaya a varander tana kallon motoci zuciyarta cike da tunanin Omar.

Omar a irin yanayin Narma ya ke tafiya, zuciyarsa gabaɗaya ta cushe babu abinda yake gani sai ita, kuma ta burge shi sosai zuwan ta gidan su ba ƙaramin girma ya bata a idanunsa ba, duk wanda ya san da Didi bata da lafiya har yazo ya duba ta ai abin ka girmama shi ne balle ita ga yadda matsayinta yake, ga kuma yadda ake faɗar rashin kırkinta. Kuma batu ake na Didi rabin ransa aka zo akazo dubawa, dole ya ji daɗi. Gaskiya in ya ce bai ji daɗin zuwanta gidan su ba ya yi ƙarya, har zuciyarsa ya ji daɗi haka ya samar mata da matsayin sosai a wajan sa. A karo na farko a rayuwarsa wata mace ba Didi ba ta burge shi, a karo na farko ya ji yana ganin girman wata mace ba Didi ba a zuciyarsa.

Koda ya shiga gida Didi ma zancen ta take yi, tana aikin faÉ—ar ashe tana da kirki har haka ake mata kallon mara kirki, shi dai bai ce mata komai ba dan shi kaÉ—ai ya san abinda yake ji a jikinsa a haka ya tafi ya kwanta, sai dai babu bacci babu alamun sa saboda tunani.

Nayla ma a irin yanayinsa take, gabaÉ—aya murmushinsa take gani a idanun ta zuciyarta na bugawa sosai, ajiyar zuciya tayi a bayyyane ta ce, "wannan wanne irin yanayi ne?." Babu mai bata amsa, ta sake yin shiru tana kallon bangon É—akin, ta kulle ido ta buÉ—e tana jin sautin muryarsa da yadda ya amsa gaisuwarta. Murmushi tayi ta ce, "he's so handsome." Salma da ta shigo ta kalle ta ta ce, "waye ya kama zuciyarki haka?."

Nayla ta kalle ta Salma ta ce, "tun É—azu na shigo kina tunani kina ta murmushi alamun kin faÉ—a soyayya, sai naji kina yabon kyaunsa, waye shi?." Gaban Nayla ya faÉ—i, sai a lokacin ta farga da hakan yana nufin soyayya, kenan son Omar take yi?. Tuna hakan sai ta wara idanu waje Salma ta ce, "meye na buÉ—e idanu, ai duk wanda yaga yanayinki a kwanakin nan ya san akwai bayani. Kenan É—an Kano kika samu ko? Yaya Abbas yana can yana haukan sonki wani ya É—auki zuciyarki."

Nayla ta haÉ—É—iye yawu ta ce, "Salma ba haka bane."
"To faÉ—a min ya ne?." Shiru tayi bata ce komai ba, ta juya baya ta kwanta tana tunanin lallai dole ta bar Kano tun kafin dare ya yi mata.

Hajiya Nayla ita soyayya ai duk inda ki ke yana tare dake. lol 😝😂

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

             ©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t

*Book 1*
*P 17.*
Chapter 35 · 0% Book details