Sashe 44
Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Didi ta ce, "na lura gabaÉ—aya a sanyaye ka ke, me ya faru ka koma haka?." Ya bita da kallo yana tunani. Bashi da aboki a duniya sai ita, babu mai bashi shawara sai ita, babu wanda yake iya faÉ—awa damuwarsa sai ita, babu da wanda ya saba sai ita É—in dai. Itace kawai mafitarsa, dole ya faÉ—a mata abinda yake faruwa ko zai samu wata makama a wajan ta.
Niyar zama yake yi aka shigo falon sai ya fasa zama yana kallon wacce ta shigo. Didi ta miƙe tsaye ganin wacce ta shigo cike da mamaki, shi kansa sai da gabansa ya faɗi balle Narma da take kallon sa. Didi ta ce, "Barr Nass."
Wajan Didi ta ƙarasa ta ce, "Sister laifi ne dan mace ta fara soyayya? Laifi ne dan ma fara son wani a lokacin da ban shirya ha? Laifi ne dan na fara son wani ba tare da na san hakan ba?."
Didi da mamaki take jin abinda take cewa ta girgiza mata kai ta ce, "A'a." Ta nuna mata Omar ta ce, "Amma Faruk ya kasa gane da gaske ina sonsa, wallahi sister daga Abuja na taho nan akwai dan na furta masa kalmar Ina sonsa. Ina sonsa da gaske, ki faɗa masa ba yaudararsa nake yi ba. In ya cigaba da tafiyar dani a haka a yadda nake jin sonsa zan iya mutuwa!" Ta ƙarasa faɗa a sanyaye tana kwantar da kanta a kafaɗar Didi.
Didi suman tsaye tayi tana jin sautin kukan Narma a kunnenta, tunani take yi wai ko dai mafarki take yi? Sai kuma taga ai ko a mafarki abinda take ji bai kamata ace yazo gare ta ba. Omar É—in ta ake magana akai, kuma Æ´ar Senator É—an takarar gwanma ce take wannan maganar. Tabbas wannan maganar indai ba mafarki bane to tabbas wasan kwaikwayo ne.
Bata iya bata amsa ba ta ji Narma ta ɗago daga jikin ta ta ce, "Sister bazan yi ƙarya dan na yaudare shi ba, ki kalli idona wallahi da gaske Ina son sa. Tun farkon ganina dashi na fara jin wani abun a kansa, da ya zo ɗauka na a Airport a nan na sake jin abinda naji. Da ya taimake ni a lokacin da aka ƙwace min waya a nan na tabbatar da ya shiga zuciyata. Ba wasa nake yi ba, ba yaudara na shirya ba, gaskiya nake faɗa Sister."
Shi dai Omar yana tsaye kaiwa bai fita ba kuma bak ce komai ba yana kallon ikon Allah. Didi sai a lokacin ta samu damar kallon Narma ta ce, "Wai Omar É—ina ki ke so?." Ta É—aga mata kai alamun eh, Didi ta zuba mata ido kafin ta kalli Omar da yake kallon su sannan ta ce, "Narma kalaman naki ne kamar a mafarki, Omar É—in ki ke so?" Ta faÉ—a tana sake nuna mata shi da yake tsaye.
Narma tayi murmushi ta lura sun kasa gane abinda yake ji a kansa, ta ce. "Shi nake so, saboda son da nake masa aka fasa maganar aurena da Ashraf É—an gov katsina state, na faÉ—awa iyayena Ina da wanda nake so su bani lokaci, yanzu sun bani lokaci suma jira na kai musu shi matsayin wanda nake so. Wallahi a yadda nake ji bazan iya auren wani in ba shi ba, ki taimaka min, kece kawai hope É—ina Sister. Nazo har nan jiya na bayyana masa amma ya ce min A'a!."
"Tirƙashi!" Didi ta furta tana sake kallon Narma dan ta tabbatar a hankalin ta take, sannan ta kalli Omar da yake jin su bai ce komai ba.
Motsawa yayi zai fita Didi ta ce, "Ina zaka je?."
"In na tsaya me zan yi Didi? Me zan ce in na tsaya? Gwara na tafi" ya faÉ—a yana kallon ta.
Narma ta kalle shi ta ce, "kana ganin kamar wasa nake yi ko?" Sai tayi murmushi ta ce, "dole zaka ji haka saboda a saba namiji ne yake bayyana cewa yana son mace kafin ita tace, ni kuma sai gashi nice nazo ina yin abinda mazan ma baza su yi ba. Ni ban iya ɓoye abinda yake raina ba, in dai akwai zan faɗa ne kawai na huta. Kuma ban ɗauki dan nazo har gidan ku na ce ina sonka da wani abun ba, gaskiya na faɗa ba ƙarya ba. Amma wallahi ko dm namiji ya yi min a social media sai na shekara ban buɗe ba, namiji sai ya shekara biyu yana so nace masa hii amma ban ce ba. Duk wannan ajin da nake dashi soyayyarka ta kawar da ita Faruk!. Kuma har yanzu kace kana tantama? Didi kina ji fa" ta faɗa tana kallon Didi da take ganin abun kamar almara.
Didi ta ce, "Ko da gaske ki ke, ko da wasa kike Narma kin fi ƙarfinki ce kina son Omar, ke ba irin matan da ya kamata ace suna son Omar bace. Kuma amsar da ya baki ta a'a itace daidai Narma, dan ke ba daidai dashi bace, ki tuna matsayin ki dana mahaifinki."
Narma ta ce, "ni dai in har yana sona duk wannan ba damuwa ta bace, iyayena suna son duk abinda nake so, ko yanzu na kai musu shi nace shi nake so zasu yi maraba da zuwan sa. Kuma na sanar dasu ma fara sonsa kuma sun yi min fatan alkhairi." Didi ta ce, "Omar ɗin ki ka ce kin fara so?." Narma tayi murmushi ta ce, "Didi kema ɗauka ki ke ƙarya nake ko?."
"A'a Narma ban ce ba, amma maganar ce dole ta saka mana shakku a zuciyar mu."
Narma ta ce, "me zan yi da zai goge shakkun? Na shiga social media nayi video ce Ina sonsa? Ko gidan tv zan je ma bada labarin yadda ma fara son sa?. Ko kuma na sanar da iyayena su zo su nemana min auren sa?. Wanne zan yi da zai tabbatar da ba ƙarya nake ba?."
Didi ganin Narma ta gigice sai ta kwantar da murya ta ce, "Ki kwantar da hankalin ki Narma, yanayin matsayin da kike dashi ne dole ya saka mu tantama a kan ki."
"Shiyasa nace me zan yi ya goge?." Didi ta ce, "babu ko É—aya da kika lissafa. Na amince da gaske kina son Omar so na gaskiya kuma so na aure."
Narma a sanyaye ta ce, "Amma shi ya ce ƙarya nake yi." Didi ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Narma ban san me zance miki ba a yanzu, amma ki koma gida zan yi ƙoƙari na shawo kansa ya faɗa min abinda yake ji ransa a kanki, in yana ji zai karɓi soyayyar ki shikenan, in baya ra'ayin hakan sai dai ki yi haƙuri."
Narma ta goge idon tana murmushi ta ce, "Hakan ma na gode. Amma Didi in kika samu labarin wani abu ya faru dani wallahi Faruk ne sila, soyayyarsa itace silar da zata jefa ni ko wanne irin yanayi. Yin acting ɗin ƙarya akan soyayya ba ajina bane, bazan taɓa iya furta ina son mutum ba indai ba da gaske nake ba Didi. Abu ɗaya kawai na sani, ina sonsa koda shi baya sona, zan rayu dashi koda baya sona."
Kallon Omar Narma tayi ta matso kusa dashi ta ce, "zan koma gida, zan je na samu likitoci naji zasu canja min zuciya. Indai zasu iya zan amince a cire tawa a saka min wata indai zan rabu da abinda nake ji. In kuma baza su iya ba ina tabbatar maka wani abun zai same ni akan abinda nake ji a kanka. Na tafi, amma ka sani zan dawo, zan dawo dan jin amsarka. Bazan iya rayuwa da wani in ba kai ba, bazan taɓa iya rabuwa da kai ba" ta faɗa tana ficewa a guje kamar walƙiya.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleemaâ¤ï¸
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
Â Â Â Â Â Â Â Â©ï¸ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
*Book 1*
*P 21.*
Didi tana kallon ta har ta fice ta dafe ƙirji ta kalli Omar da yake tsaye har lokacin ta ce, "wai da gaske ba mafarki nake yi ba?." Ƙoƙarin fita ta ga yana yi ta ce, "Ina zaka je?" ya juyo yana kallon ta ta ce, "Dawo, ai fita bata kama ka ba Omar. Daman shine silar magangangun da kayi min jiya? Daman akan Narma ne Omar?."
Yana daga wajan da yake tsaye ya ce, "na rasa abinda zan ce ne Didi, ban san me zan yi ba, ban kuma san a wanne matsayi zan ajjiye hakan ba."
Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Omar ni na amince da gaske Narma tana sonka." Ya kalle ya ce, "ta ya kika tabbatar a lokaci É—aya haka?."
"Kalamanta, yanayinta, matsayinta. Omar a matsayin da Narma take dashi a Nigeria baka kai matsayin wanda zata yiwa wasa da hankali ba, ko ta yaudare shi ba. Soyayya bata duba cancantar mutum ko kuɗi ko mulki, dan zuciyarta faɗa a soyayyarka abu ne mai sauƙi tunda ba itace tayi kanta ba. Mace kamar ta baro Abuja kawai saboda ta zo ta ce maka tana sonka daga ji ka san wannan abin ya kai zuciya."
Kallon Didi yake yi har ta gama magana kana ya ce, "in kuma film aka shirya fa? Ni Ina ganin kamar da wata manufa hakan ya faru. Ta ya za a ce lokaci É—aya ta baro garin su tazo ta ce tana sona? Har yaushe ta sanni? Yaushe muka yi sabon da zata fara sona? Yaushe muka yi mu'amala tare da hakan zai faru?."
Didi ta murmusa ta kalle shi ta ce, "Wacce manufa kenan? Me ka ke dashi da Narma zata yaudare ka Omar? kai waye a Nigeria da za a yi amfani da ita wajan yaudararka?. Da gaske na san ana amfani da mace a yaudari mutum amma sai mutum ya kai inda ya kai ake aika masa haka. Allah na tuba kai wanne matakin rayuwa ka taka da za a yi amfani da ita a cuce ka? Ai in ma cutar taka za a yi sai dai ayi amfani da mata irin na lunguna ba dai ita ba."