Sashe 6
Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon sa take yi ta ce,"Kar na gane Omar, Sai aukin iya karin magana kamar goyan Kaka." Murmushi ya sake yi ta sake kallon sa ta ce, "Murmushi yana sake fito da asalin kyaun ka Omar, Meyasa baka son yin murmushi sai wa ni kawai?."
"Ba kowa ya cancanci ya gani ba."
"Sai ni sai matarka?." Kallon ta ya yi jin kalmar mata da ta saka, ya É—an sosa walwatacciyar girar sa kamar yadda ta zama al'adar sa na É—ora yatsu biyu akan goshin sa ya É—an murza kaÉ—an amma bai ce komai ba.
Didi ta ce, "Hmm! Zan ga matar da zaka aura dai Omar."
"Au za a samu wacce zata aure ni?." Ta wara ido da mamakin kalaman sa ta ce, "Meyasa ka ce haka?."
"Haka nan" ya bata amsa a taƙaice.
"Za a samu mana Omar. Shiyasa nake so ka ajjiye wannan ɗabi'ar ta ka, in kana a haka ba ko wanne uba ne zai baka auren ƴar sa ba." Ya taɓe baki ya ce, "nima ba a wajan ko wanne uba zan nemi aure ba." Murmushi ta sake yi jin abinda ya ce dan kuwa ba a kayar dashi a bada amsa. Bata sake cewa komai ba sai sauraron muryar Narma da ake hira da ita akan yadda take gabatar da aikin ta da sauran rayuwar ta.
"Gobe zan je Abuja." Kallon sa tayi jin abinda ya ce ta ce, "Abuja? Me ake yi?." Ya ɗora ƙafa kan ɗaya wani baƙin zare da yake ɗaure a ƙafarsa ya bayyana, yana ɗaure a tsintsiyar ƙafarsa kamar sarƙar ƙafa ta mata. Ya yi masa kyau sosai ya haska farar ƙafarsa matuƙa. Ya ce, "aiki." Didi ta ce, "wanne irin aiki ne haka? Wai me yake kai ka Abuja akai akai haka Omar?. A mota zaka je ko a jirgi?."
"Hmmm Didi kenan" ya faɗa yana ƴar ƙaramar dariya kana ya ce, "ai na wuce zuwa Abuja a mota tun tuni." Ta fuskance shi sosai ta ce, "Omar me yake kai ka Abuja haka? Daga fitowar ka daga prison ka je Abuja sau uku kenan. Me ka ke yi a can?."
"Aiki ne yake kai ni."
"Wanne irin aiki?" Ta faɗa tana yi masa kallon tuhuma kafin ya yi magana ta ce, "yaushe ka fara aiki babu labari? Yaushe ka fara ɓoye min abu?."
Shiru yayi bai amsa mata ba ta ce, "Omar da kai nake fa, yaushe ka fara aiki babu labari sannan wanne irin aiki ne haka?." Kallon ta yayi ta ƙasan ido ya ce, "kin san ni ba ɗan kidnapping ba ne ba ko?."
"Nima ban ce ba, amma me yake kai ka Abuja haka?."
"Aiki ne yake kai ni can Didi." Wayarsa da take ƙara ya saka bata sake magana ba shi kuma ya miƙe ya fita. Mamaki take yi wanne irin aiki ne ya kai shi Abuja haka? Anya babu abinda yake ɓoye mata game da rayuwar sa?. Babu mai bata amsa sai shi ta kuma san babu lallai ya amsa mata.
     Bai jima ba ya dawo ya koma inda ya tashi ta ce, "tunda baza ka faɗa min ba kaje ka kulle mana gidan kar a shigo mana." Kallon ta ya yi a kaikaice ya ce, "ai ko shekara gidan nan zai yi a buɗe babu halittar da zata iya shigowa da niyar cutarwa. Ko aljani sai dai wani gidan ba dai wannan ba."
"Har da aljanu a masu tsoron na ka kenan?."
"Hmmm!" Shine abinda ya furta kawai yana É—an sakin fuskar sa kaÉ—an.
"Ko bara almajiri baya shigowa saboda kawai ana jin tsoronka, ni dai ina nan ina yi maka addu'ar canji daga wajan Allah, wannan ɗabi'a har ina? In sha Allah canji yana nan zuwa rayuwarka. Ina yi maka fatan ka amsa kiran ƙaddararka da kuma rabo. Maƙota babu mai shigo min saboda kai, kowa tsoron ka yake ji."
Bai ce komai ba yayi shiru muryar Narma na tashi a falon hakan ya saka ya sake kallon Tv kafin ya yi tsaki ya É—auka kansa zuciyarsa na wani tunani daban.
Babban burinsa a rayuwa bai wuce Didi tayi aure ba, amma auren ya gagara saboda baƙin fentin da yake ganin mahaifin su ya shafa musu. Shekarar ta talatin biyar amma bata taɓa aure ba, da an fara batun auren sai ya lalace, ya rasa meye dalilin hakan. Shi ba ya hango lamarinsa yana daga cikin dalilin da ya hana Didi aure, kawai abinda yake hange daban kuma ya tabbatarwa kansa da shine silar da ya hana Yayar sa yin aure.
Numfashi ya sauke da ƙarfi hakan ya saka ta kalle shi ta ce, "ka je ka kwanta, Nima gobe ina da aiki zan yi jollop rice ta mutane ɗari, bacci zan yi." Tashi tayi ta barshi a falon ta shiga ɗaya daga cikin daƙuna da yake falon guda biyu.
Tana shiga ta tsaya a jikin ƙofa tana goge idanunta cikin tausayin ƙanınta da ita kanta, Tabbas mahaifin su shine silar shigar Omar wannan hali saboda yawan aibata yaran mutane da yake yi Allah ya ɗorawa na sa. Amma ta tabbatar da Allah ne ya rubuta faruwar hakan a gare su, tana kuma sake gode masa yadda aka so su wulaƙanta a duniya basu wulakanta ba sun samu rufin asiri daidai gwargwado.
Shi kansa Omar É—in yadda aka so ya lalace bai kai haka ba, duk da ta san tasirin addu'arta ne da ta malaman islamiyyar da take zuwa su taimaka mata da addu'a kansa. Duk da ana kallon su a matsayin masu cin kuÉ—in haram amma ita ta san ba haram suke ci ba shiyasa maganar mutane akan wannan baya damun ta. Da wannan tunanin tayi alwala ta fito falon ta samu baya nan ta kashe kayan wuta na falon ta koma ciki.
       Washe gari.
Kamar yadda Omar ya saba bai cika bacci bayan sallar asuba ba, gari yana haske ya fita motsa jiki bayan ya dawo yayi wanka ya shirya. A lokacin Didi ta fito tsakar gidan shima ya fito ya shirya cikin ƙananun kaya kamar ko yaushe. Riga ce fara a jikin sa sai ta sama da ya ɗora baƙa mai zip amma bai kulle zip ɗin ba ya zama ana ganin farar. Sai dogon baƙin jeans da ya saka, sai takalmi wanda ya rufe ƙafarsa gabaɗaya. Kallo ɗaya in kayi masa baza ka ce yana taɓa dabanci ba saboda gabaɗaya yanayinsa bai gwada hakan ba, wani lokacin kana kallonsa zaka tabbatar da tantiri ne, wani lokacin in ka kalle shi sai kaga kamar ba shi ba. Murmushi tayi tana kallon sa kafin ya ce, "Ina kwana Didi."
Sai da ta ƙaraso kusa dashi sannan ta ce, "Ka tashi lafiya?."
"Lafiya lau, na shirya zan wuce, a yau zan dawo ba kwana zan yi ba."
"Baza ka ci abinci ba?."
"Uhum bana jin yunwa." Ta girgiza kai ta ce, "To Allah ya dawo da kai lafiya."
"Amin. In akwai abinda ki ke so su Tk suna nan." Tayi murmushi ta ce, "To a dawo lafiya." Ya É—aga kai kafin ya juya ya fita daga gidan.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleemaâ¤ï¸
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
Â Â Â Â Â Â Â Â©ï¸ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t
*Book 1*
*P 03*
*ABUJA*
*11:00am.*
Senator Sagir Sani yana zaune a babban falo mai kyau da ƙayatarwa ya ɗora ƙafa kan ɗaya yana ƙadawa. Su biyu ne shi da wani abokinsa mai kuɗi da mulki kamarsa. Yanayin yadda suke magana zai baka tabbacin sun saba sosai. Sen Sagir ya kalli abokin na sa ya ce, "Wallahi shine abin ya dame ni, bana son zuwan Narma Kano gabaɗaya, kai ka san abinda ya faru kwanaki."
Minister ya kalle shi ya É—an dariya ya ce, "Haba Senator, yanzu meye abin damuwa a nan? Wancan lokacin ma ai akasi aka samu yanzu kuma baza a maimaita irin sa ba. Duk jam'ian tsaron da suke Kano sai hankalinka ya tashi dan Narma zata je can?."
"Kai baka san yadda na tara maƙiya bane shiyasa ka ke faɗar haka."
Minister ya sake yin dariya ya ce, "ko shekara zata yi a Kano babu abinda zai sameta, akwai fa masu tsarom lafiyar ta ka manta ne?. Akwai police da za a bata, in ta kama a bata sojoji ma duk normal ne ba abin damuwa bane." Sen ya kalle shi ya ce, "kuma fa haka ne. Ni na san da wanda zan haÉ—a ta."
"To ka gani, meye na damuwa?."
Wayar Senator ce tayi ƙara ya duba kafin ya saka a kunne ya ce, "Ya shigo mana." Sauke wayar ya yi ya kalli minister ya ce, "Yanzu mutumin zai shigo." Minister ya ce, "Waye kenan?."
"Masu bada ransu a kan mu mana, wanda nake faÉ—a maka ina da shi a Kano."
Minister zai yi magana Omar ya bayyana a falon da sallama cikin dakakkiyar muryarsa. A tare suka kalle shi suka amsa Senator yana kallonsa yana murmushi har ya ƙaraso ya zauna akan kujera kamar yadda suke akan kujera kana ya ce, "Barka da safiya Senator."
Murmushi ya yi sosai ya ce, "Tiger! Ka tashi lafiya?."
Omar ya É—aga kai sannan ya ce, "lafiya lau" ya kalli Minister da yake kallonsa ya ce, "Barka da safiya." Minister yayi murmushi ya ce, "barka." Sen ya kalli minister ya ce, "minister wannan shine Tiger! Babban makami na a garin Kano, Tiger ga Minister" ya faÉ—a yana kallon Omar da burgewa.
Minister ya ƙare masa kallo ya ce, "wai shine Tiger ɗin da ka ke bani labari ko yaushe?." Sen ya amsa yana kallo Minister shi kuma ya zare glasess ɗin idon sa yana kallon sa ya ce, "Wow! He seems really nice, babu wanda zai kalle shi ya ce he's the one. Kalle shi fa kyakykyawa kamar balarabe." Sen yayi murmushi ya ce, "shiyasa ake masa laƙabi da damisa, komai cikin nutsuwa ake gabatar dashi babu hayaniya balle ɓata lokaci."