← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 54

Sashe 5

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya tuna kwanaki da wani ya aikata irin abinda ya aikata yaƙi yarda ya kai kansa ga ƴan sanda, aka bar shi da Omar yana da ƙafafunsa basa takuwa saboda sun tashi aiki. Omar ba ya kisa, amma za a yi maka abinda zaka gwammace kashe ka aka yi.

Ajiyar zuciya yayi ya ce, "mu je ga hukumar." Omar ya koma gefe kamar ma bai san ana yi ba, tare suka tafi police station aka gabatar da mai laifi kamar yadda maganar ƙwace wayar ta zaga duniya saboda irin kisan da aka yiwa wanda aka ƙwacewa wayar. Video aka yi masa aka yaɗa a duniya ana tabbatarwa da mutane wanda ya yi kisan ya shiga hannu, kuma za a yi masa hukunci daidai da abinda ya aikata.

         A nan suka yi sallar magriba gabaɗaya, DPO yana ta yabawa Omar akan abinda ya yi, duk da an saba ire-iren wannan laifin ya kan kawo wanda ya aikata don a hukunta shi.  Shi kuwa ko maganar kirki samu daga gare shi ba burinsa a hukunta shi in ba haka ba shi ya ɗauki mataki.  Ya tsani yadda ake ƙwacewa mutane waya kuma a cutar dasu, kai da abin ka a ƙwace maka kuma a cuce ka saboda tsabar zalinci. In da iya ƙwacen ne ma da sauƙi, amma bayan a ƙwace sai an cutar da kai. Shiyasa baya ɗagawa kowa ƙafa akan ƙwace, ko da kana daga cikin yaran ka aikata sunan da ake kiran sa zai yi tasiri a kan ka. Damisa ƙi sabo!.

Suna idar da sallah suka koma unguwar su kamar yadda suka saba. WaÉ—anda suka kalli video da aka yaÉ—a sai kallon Omar suke yi suna mamakin yadda wani lokacin yake yin aiki irin na masu hankali wani lokacin kuma ya yi aiki irin na Æ´an daba.

Tare suka shiga gidan da yaran sa su uku har shi na huɗu. A lokacin Didi tana zaune akan sallaya a tsakar gidan tana sauraron abinda ake faɗa a video da aka yaɗa na yaron da Tiger ya saka aka kama. Ganin shigowar su sai ta kalle shi ta ce, "ka ɗauko mu ku abinci." Bai ce komai ba ya nemi waje ya zauna dan sun san bazai dauƙo ba. Goje ne ya ɗauko abincin da kansa dan gidan ba baƙon su bane, babu inda basa shiga dan sune kamar ƴan aiken ta. Abincin ya kawo kowa ya zuba abincin yana ci.

"Omar amma abinda ka yi ka kyauta sosai, ina nan ina fargabar kar ka É—auko min magana ashe gyara ka je kayi. Da haka ka ke yi da ba ayi maka wani kallo na daban ba" Didi ta faÉ—a tana kallon sa.

Numfashi kawai ya sauke bai ce komai ba sai tayi murmushi bata damu da shirun na sa ba ta ce, "Tukur meyasa bakwa yiwa mai gidan ku faÉ—a ne? Meyasa bakwa faÉ—a masa gaskiya?." Tk ya kalli Didi yana murmushi dan itace kawai take ce masa tukur a zauna lafiya, Tk shine sunansa ba Tukur ba. Ya ce, "Didi Tiger fa ba yadda ki ke tunani ya ke ba, mutum ne mai son zaman lafiya in kinga an samu matsala dashi akasi aka samu."

        "Ba wani nan, kawai kana kare mai gidan ka ne, kuma bakwa faɗa masa gaskiya" ta kalli sauran da suke cin abinci suna murmushi ta ce, "Sai murmushi ku ke yi babu mai faɗa masa gaskiya a cikin ku, na tabbatar in Omar ya watsar da makaman sa kuma za ku watsar, domin kuwa ya zamar kamar shi ne komai na ku, in ya ce ayi kuna yi, In ya ce a bari kuna bari. Da tattara ku ya yi ku ka koma kasuwa duk da hakan bai faru, da nima na huta da ɗauko min maganar da ku ke yi." Ƴar dariya suka yi dukkan su dan in da sabo sun saba da wannna maganar ta Didi. Shi kam ko motsin kirki bai yi ba balle yayi magana abinci kawai yake ci.

Da kansu suka kwashe mata kayan aka shiga dashi kitchen kafin su miƙe tsaye Goje ya ce, "Tiger zamu wuce." Shima tashi yayi suka fita gabaɗaya ta bisu da kallo tana yi musu fatan shiriya. Sallah i'sha tayi bayan ta idar ta kunna tv kasancewar suna da wutar solar, rana tsaka ta ga Omar da masu haɗawa aka haɗa a gidan. Da ta takura masa da tambayar inda samu kuɗi sai ya ce sadaka aka bashi. Ta kuma san gatse ya yi mata, kawai bazai faɗa bane shiyasa ta haƙura.

Babu jimawa ya shigo da sallama ta amsa ya samu waje ya zauna ta kalle shi ganin yayi shiru yana kallon hoton da yake kafe a falon. Hoton su ne shida ita da mahaifiyar su a ranar da ya cika kwana bakwai a duniya. Ganin abinda ya ke kallo ya saka ta kalle shi ta ce, "ko dan saboda ita nake so ka gyara rayuwarka ka koma mutum kamar kowa saboda tayi alfahari da kai a ranar tashin qiyama. Ko dan saboda Mama da Baba...." Kafin ta ƙarasa ya kalle ta ya ce, "iya Mmaan dai, ki cire na ƙarshen."

Da mamaki take kallon sa ta ce, "wai tsaya! Omar Baba ba shine ya haife ka? Meyasa baka so a dinga zancen sa kamar ba uban ka ba?."
"Bai cancanci na dinga tunawa dashi ba ko kaÉ—an."
"Mahaifin?."
"Shi fa" ya bata amsa kai tsaye.
"Me ya yi maka?."
"komai ma" ya bata amsa yana ɗora ƙafa kan ɗaya.

         "Omar ko dan saboda ƙasa da ta rufe idanunsa ya kamata ka manta da abubuwa da suka wuce a baya. Kuma abinda ka ke fushi a kai baka san an yi ba labari aka baka, amma ka ara ka yafa." Ya sauke ajiyar zuciya bai yi magana ba, ganin hakan sai ta canja batun ta ce, "Baba Adamu ya yi min waya ɗazu yana tambayarka na ce baka nan."
"Waye haka?" Ya faÉ—a yana danna waya.

Ta sake kallon sa ta ce, "Baba Adamu fa nace maka." Ya kalle ta yana É—aga yalwatacciyar gashin girarsa ya ce, "Shine nace waye haka?."
"Yayan mahaifiyarka." Ya girgiza kai ya ce, "ban san shi ba." Banza tayi masa bata sake magana ba dan in ta biye masa ranta ne zai zo ya ɓaci da irin waɗanan kalaman na sa marasa control. Jin ta yi shiru sai ya girgiza kansa ya ce, "ba dan ba dan ba ko....hmm." Jin abinda ya ce sai ta kalle shi suka haɗa ido ya ce, "bani da dangi a kaf duniyata, ke kaɗai ce dangina a kaf rayuwata."

"Hmmm Omar kenan!." Ta faɗa kawai bata tanka masa ba, in ta biye masa taurin kansa ɓacin rai zai jawo mata, shi kuma ko a jikinsa gaskiyar abinda yake zuciyarsa ya ke faɗa. Tv take tana kallon a lokacin aka hasko fuskar wacce ta kunna tv domin ta a daidai lokacin tana cewa, "Sunana Narma Sagir Sani wacce ku ka fi sani da Barr Nass."

Murmushi Didi tayi ta ce, "haka kawai Allah ya ɗora min soyayyar yarinyar nan a zuciyata. Bana kallon shirin nan amma saboda a shafin ta na instagram na ga ta ce yau za a saka interview ɗin da aka yi da ita ya saka na zauna." Kallon wacce take kallo yayi yana mamakin ko meye abin so a yarinyar nan da Yayarsa take son ta oho. Kallon sa tayi ta ce, "yarinyar nan bata burge ka?. Tana ƙoƙari wajan karɓar cases na ƙananun yara, sannan an ce bata taɓa yin rashin nasara ba a duk case ɗin da zata yi." Kallon tv ya yi ya kalli Didi ya ce, "Tunda ke tayi miki shikenan ai."

Dariya tayi ta dafa kafaɗar sa ta ce, "ɗazu da safe da baka nan Oga Mansur ya sake zuwa gidan nan. Don Allah Omar ka daure ka koma harkar aikin kayan nan, aikin ya karɓe ka kana da nasibi sosai akai meyasa baza ka dogara da kanka ba?."

"Bayan Allah akwai wanda na dogara dashi ne?" Ya tambaya ba tare da ya kalle ta ba. Ta girgiza kai ta ce, "Babu, amma in da sana'ar aikin yin takalman nan ka ke yi sai an fi ganin girmanka da martabarka, saboda kowa ya san harkar sa'anarka ka ke yi babu mai yi maka wata magana ta banza. Aikin ya karɓe ka, ka iya fiye da tunanin mai tunani, meyasa ba zaka riƙe iyawar ka ba?."

"Ni da ba sarki ko gwamna ba martaba da girman me zan nema? Tunda ina girmama kaina hakan ya ishe ni. Kuma ko a yanzu babu wanda ya isa ya yi min maganar banza, ai na wuce a kalli idona a yi min maganar da bata kwanta min ba. Ai ko kura ta rame ta wuce rainin karnuka, kuma duk lalacewar giwa ai tafi ƙarfin suya, balle giwar da lafiyar ta babu abinda ya same ta."  Zata sake magana ya ce, "Didi zaki ɓata bakin ki ne kawai, na wuce zama a ƙarƙashin wani, in zan yi sai dai nawa na kaina."

Ta girgiza kai ta ce, "Tunda kai ba kowa bane zama a ƙasan wani ya zamar maka dole, kuma waɗanda ka ke so ka bawa haushi a rayuwa baza ka taɓa ɓata musu rai da ɗaukar wuƙa ko adda da zaman prison ba. Murna ma zasu yi in suna ganin har yanzu kana cikin wannan ƙasƙantacciyar rayuwar. Amma in ka gyara rayuwarka ka koma makaranta, Allah ya ɗaukaka duk mai son ganin ka wulanƙanta a wannan gaɓar ne zai ji haushi." Kallon idanun ta yayi na wani lokaci sai kuma yayi murmushi wanda fararen haƙoransa da suke a jere reras suka bayyana ya ce, "Didi baza ki gane ba."
Chapter 5 · 0% Book details