Sashe 12
Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Allah yasa ba harkar siyasa ba ce ba." Murmushi yayi kaɗan amma bai ce komai ba. Ta kalle shi ta ce, "ina so ka gane ƴan siyasar nan amfani suke yi da ku wajan lalata rayuwarku su kuma su inganta ta ƴaƴan su, ku ɗauki makami ku je ku yi musu yaƙi su kuma su gina yaran su da ilimi. Kuna nan kuna wahalar banza kuna haƙilo ƴaƴan su suna gida cikin ac da kwanciyar hankali, ku kuma sun mayar da ku ƴan wahala waɗanda ba su san darajar kan su ba. In da gaske yaƙin neman zaɓen su ke yi su fito a yi da ƴayan su mana. Baza su yi ba saboda rayuwar ƴaƴan su ba irin ta ku bace, aikin ku ku salwantar da rayuwarku a kan su, su kuma su gina na su." Kallon Didin yayi ya ce, "Didi kenan."
"Ko nayi ƙarya ne?."
"A'a" ya faɗa yana ɗauko wayar sa ƙirar iphone yana dannawa.
Didi ta kalle shi ta ce, "Ni wai ya aka yi ka ke iya operating É—in waya? Gashi ko labarai ne da turanci sai na ji ka karanta ka faÉ—a min, ya abin ya ke?." Ya kalle ta da mamaki ya ce, "Oh dan bana so ana yi min magana da turanci shiyasa ki ke yi min kallon ban iya ko?." Ta yi Æ´ar dariya ta ce, "A'a ban ce ba. Kawai dai na san ko secondary school baka yi handling ba, duk da ka ce jarabawa ce baka yi ba."
Ya kalle ta ya ce, "Ai kin san jarabawar ce ban yi niya ba, kuma mutum nawa na rubutawa waec ana biyana?. Ko ke da ki ke taƙama da wani NCE ko diploma sai mu zuba, wallahi sai na kai ki ƙasa ko motsi baza ki iya ba. In kina mamaki a feɗe biki biri har wutsiya." Ta yi dariya sosai ta ce, "Wane mutum! Ku ai gifted ne, ku karatu yake bi kuna guduwa. Da ka tsaya ka yi karatu ko Omar, da ba ƙaramin amfana za a yi dakai a ƙasar ka ba."
"Babu niya, tunda sai wanda yake da ilimin boko ne yake zama wani a duniya zan ta zama a yadda ku ke kallona."
Didi ta ce, "Allah ya ke bawa kafirai arzuƙi a duniya balle musulmi mai bauta masa?. Allah yana bada duniya ga wanda yake da wanda baya so, lahira ce sai rabo. Ba sai mai karatun boko ne yake zama wani ba Omar, in dai Allah ya saka maka albarka zaka iya zarce wanda ya kai matakin professor. Ilimin yana da amfani ne saboda goyayya da mutane."
"Mutane haka suke ɗauka, wanda bai yi boko ba babu shi babu arzuƙi a duniya. Turanci ne kaɗai ilimi a nigeria, duk ilimin ka in baka iya shi ba a banza ake kallon ka. Mu baza mu yi karatun ba, kuma baza mu yi turancin ba, in Allah ya ce yes sai na ga ɗan shegiyar da zai ce no. Ko yanzu in niya zan je a bani takardar da ku ke taƙama da ita, kawai babu niya ne."
Didi ta yi dariya cikin tsokana ta ce, "Ni dai ina so naji ya akayi ka ke iya karanta turanci? Ko duk zaman social media É—in ne ya kawo haka?. Yadda ka ke zama ko yaushe cikin danna waya da kuÉ—i ka ke samu da ita da ka ji daÉ—i." Murmushi ya yi kaÉ—an bai ce komai ba.
Ta ce, "tsokanarka nake, ko a shekarun baya kana cikin wanda makaranta take ji da ku." Bai bata amsa ba sai girgiza ƙafa da yake yi, ta kalli ƙafar ta sa ta ce, "wai ni meye benefit ɗin wannan baƙin abun da ka saka a ƙafarka? Gashi dai yana yi maka kyau sosai, amma adon mata ne."
Taɓe baki ya yi bai ce komai ba ta ce, "ko da yake ko mace aka gani da sarƙar ƙafa wata fassara ake mata daban."
"Ni kam yana burge ni."
"Sai matarka ta saka." Bai ce komai ba cikin tsokana ta ce, "Wai kuwa ka san me aure yake nufi?." Wani kallo ya ɗago ido yake mata na kin raina min hankali, Didi ta sheƙe da dariya ta ce, "to kai ba abokai ne da kai ba, ba wani waje ka ke zuwa ba ta ya zaka fahimta daidai?." Murmushi ya yi bai kula ta ba dan bazai kulata ba.
Kira ne ya shigo wayar Didi ganin sabuwar number sai ta ɗauka masu siyan abincin ta ne, ta saka a speaker daga can ɓangaren aka yi sallama jin muryar namiji sai ta amsa a sanyaye kafin ya ce, "don Allah da Aisha nake magana?." Didi ta ce, "eh itace. Wake magana?."
"Sunana Abdulhamid."
"Allah sarki!."
"Aisha ina so ki bani lokaci ina so zan yi magana dake." Didi ta kalli Omar da ya kafa mata idanu ta ce, "Magana da ni? Akan me?."
"Alkhairi. Magana a waya baza ta yu ba ikon ganin ki nake so ki bani." Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "To san sanar da kai."
"Yauwa na gode, don Allah ki saka lokaci mafi kusa in hakan zai samu."
"Shikenan, zan maka text."
"Na gode sosai, ki kwana lafiya" Didi ta amsa shi kuma ya kashe wayar.
"A ina ya samu number ki?" Omar ya tambaya yana kallonta.
"Omar ta ya zan sani? Ni dai kawai ya kira ni ne."
"Me ya ke nema?."
"Omar ta ya zan sani? A gaban ka fa ya kira ni."
Omar ya ce, "wanne lokaci zaki ba shi?."
"Bana ce ba." Ya kalli Didi cikin bada umarni ya ce, "ki faɗa masa yazo jibi, jibi juma'a kenan, ina gida nan zan so na zauna a tatauna dani. In da tsiya ya zo gidan ya tarar, in arzuƙi ne ya kawo shi ana yi masa maraba." Tayi murmushi ta ce, "to babban Yaya." Jin abinda tace sai yayi murmushi amma bai ce komai ba.
"Kai yaushe zaka yi auren ne?." Ya É—an juya idanunsa ya ce, "kwana biyu meyasa ki ke yi min zancen aure ne?." Tana murmushi ta ce, "ai ka kai ka yi É—in ne Omar, santalelen saurayi kamar ka ga kyau ga kwarjini ai dole ayi maka zancen aure."
"Ni wallahi bana kawo zancen aure a raina ko kaÉ—an."
"Ko me yasa?."
"Sai na fara aurar da ke" ya faɗa yana miƙewa tsaye.
Ƴar dariya tayi ta ce, "Ko kuma ni na fara aurar da kai ba." Bai yi magana ba ta miƙe tsaye tana kallon sa duk da ya kere mata a tsayi sosai ta ce, "burina naga kayi aure ka haifa mana mai sunan Mama Omar, duk macen da ta same ka zata yi sa'a, a haka ne ake kallon ka a baibai amma ni da na san ka, na san sa a tana tare da wacce zaka aura, musamman in ka ɗauki nasihar da nake yi maka a kullum."
Fuska sake yake kallon ta ya ce, "Yanzu in aka aure ni ba a yi sa a ba kenan?."
"Eh to, kusan hakan zan ce." Yayi murmushi mai sauti ya kalle ta ya ce, "ina zuwa." Fita yayi daga gidan gabaɗaya. Kasancewar unguwar akwai duhu da ya fito ƙofar gidan daga wajan gidan su ne kawai mai haske sauran wajan babu haske.
A hankali yake takawa yana jiyo magana na tashi ana daga inda yake nufa, muryar maza ya ji suna cewa, "hmm to Omar da Aisha meye basa aikatawa, kai a banza ta kai yanzu bata yi aure ba?. Wannan ingarmar namijin da take kwana dashi waje É—aya ta tashi ba dole mugun abu ya faru ba."
Ɗaya daga cikin su ya ce, "wai don Allah da gaske ku ke?." Na ukun ya ce, "to kai gani ka ke wasa ne? Baka ganin yaron ko kula mutane baya yi saboda ya san iskancin da yake yi?. In da ma ace iya dabancin ya tsaya da sauƙi, to har da lalata da ƴar uwarsa. Ai ba a banza ta kai wannan shekaru babu aure ba, tana samun duk abinda ƴa mace take samu a gidan mijinta a wajansa. Kai baka ganin da an zo neman aurenta sai a gudu ba? Wannan mugun abun da suka binne ake tonowa."
"Kuma fa ashe gado ya yi, ubansu tantirin É—an iska ne tsohon É—an giya. Ai barewa baza tayi gudu É—anta ya yi rarrafe ba, nan gaba zaman unguwar nan sai Omar ya hana mu."
Omar yana jinsu ya runtse idanu cikin ɓacin rai da ƙunar zuciya, ya koma da baya ya hangi yaransa a gefe yayi musu alamun da su yi shiru kar su yi magana su zo inda yake. Nuni ya yi musu da kowa ya kama mutum ɗaya a cikin ƴan majalisar da suke gulmarsu. Cikin sanɗa suka ƙarasa inda suke sai caraf ko wanne ya riƙe mutum ɗaya.
Omar ya tako ya bayyana a gabansu ransa a ɓace sosai duk suka kalle shi cikin firgici da tsoro. Alama yayi musu da su sake su, dukkan su suka sake su ya bisu da kallo dan dukkan su manya ne a haife zasu haife shi. Babu wanda yayi ƙoƙarin miƙewa a cikin su saboda duk sun tsorata matuƙa suna kallon Omar. Abin ka da wanda yake gulmar wani kuma ya kama shi, wanin ma kuma irin Omar."
Tsakiyar su ya shiga ya zauna tare da ɗauko ƙaramar wuƙa a ƙasan takalmin yana shafa ta a hankali ba tare da ya kalle su ba. Duk sun ruɗe, jikinsu ya fara ƙyarma cikin tsoro. Zaman da ya yi a cikin su yafi komai tsorata su, ga wuƙa kuma a hannunsa. Ajiyar zuciya Omar ya yi, ya daidaita kansa kana ya ce, "Ku maimaita hirar da naji kuma yi yanzu." Tsit suka yi kowa ya kasa cewa komai, Omar ya kalli ɗaya daga cikin su sai kawai ya zube a ƙasa saboda tsoro jikinsa na rawa sosai.
"Ku maimaita na ce" ya sake faÉ—a a kausashe yana kallon su. Nan ma suka yi shiru ya girgiza kai ya ce, "kenan kun san ba daidai ku ke faÉ—a ba ko? Shikenan, tunda baza ku yi magana ba bara na saka a saka ku magana."