Sashe 17
Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Didi sallama ta jiyo daga tsakar gidan hakan ya saka ta kashe gas ta fito tana amsawa. Gabanta sai da ya faÉ—i ganin wanda ya yake tsaye a tsakar gidan ta daure tayi murmushi ta ce, "Kawu kai ne tafe? Sannu da zuwa." Wanda ta kira da Kawu ya yi murmushi ya ce, "Yauwa Aisha, ke kaÉ—ai ce a gidan?."
"Eh ni kaÉ—ai ce Kawu, Omar bai dawo daga masallaci ba. Shigo kawu."
Kawu ya yi ajiyar zuciya dan yana daga cikin masu tsoron Omar ya shiga falon da sallama. Didi ta amsa ya zauna suka gaisa ta ce, "Ya Mutanen gidan?."
"Lafiya lau Aysha. Daga masallaci nake na biyo mu gaisa na kawo miki kafin bikin ƙanwarki" ya faɗa yana miƙa mata katin.
Didi da murmushi ta ce, "bikin wa za a yi Kawu?." Kawu ya ce, "Bikin Ramla." Jin sunan Ramla sai da gabanta ya faÉ—i itama sai tayi murmushi ta ce, "Kai ma sha Allah! Allah ya nuna mana lokacin."
"Amin ya Allah, Amma zaki zo ko?."
"Zuwa kai Kawu, in ban zo ba waye zai zo?." Yayi murmushi ya ce, "gaskiya ne, ku ne yayyen amarya."
Tayi murmushi ya miƙe tsaye ta ce, "Kawu ko ruwa baka sha ba ka miƙe." Kawu ya ce, "sauri nake yi, babu komai ba sai na sha ruwa ba. Na ce Omar bai shirya aure bane?." Ta kalle shi ta ce, "Gaskiya bai shirya ba."
"In ya shirya akwai ƙannensa zai iya zuwa ya nema." Jin abinda Kawu yace sai tayi murmushi tana murna da Omar baya nan da an shiga uku da wannan furuci na Kawu.
"Didi!" Omar ya faÉ—a yana shigo falon. Ganin wanda yake parlon sai ya tsaya cak yana kallonsa kafin ya girgiza kai ya kalli Didi da ita kanta bata so ya shigo ba, Kawu kuwa ya gamq tsurewa saboda tsoro.
Karaf Didi tayi ta ce, "Omar ga Kawu, ya biyo mu gaisa ya kawo katin biki ƙanwarka Ramla." Idanu ya waro waje ya ce, "ni bani da wani Kawu a duniya, kuma bani da ƙanwa, bani da ƙanwa a duniyar nan kar ki sake cewa ƙanwata!."
Kawu yayi tsitt bai ce komai ba zuciyarsa rawa kawai take yi saboda tsoro. Kallon Kawu ya yi ya ce, "Baka san baƙi ba sa zuwar mana gıda ba?." Kawu ya ce, "Omar ni ne fa."
"Kaine wa? Na ce kai ne?" Ya faÉ—a a zabure yana fito da idanunsa waje cikin fusata.
Didi ta kalle shi ta ce, "Omar meye haka?."
"Didi wai meyasa ki ke min haka ne? Su waye waɗannan da ki ke bari suna shigo mana gıda?. Waye shi? waye na mu?" Ya faɗa yana ɗaukar iv da aka kawo ya watsar dasu a tsakiyar falon.
"Omar Kawu ne fa."
"Ke ki ka san wani Kawu ni ban san shi ba, bani da wani Kawu a duniya" ya faÉ—a idanunsa a waje yana karkaÉ—a yatsansa. Kallon Kawu ya yi ya ce, "ka manta abinda na yi maka wancan lokacin ko? Baka ji ba ka sake zuwa gidan nan ko?. Shikenan zan maka tabon da baza ka sake marmarin zuwa ba."
Kawu ya tsorata sosai ya ce, "ka yi haƙuri Oma...."
"Kar ka sake faɗar sunana, haƙuri kuma ban san shi ba!" Ya faɗa da ƙarfi yana kallonsa. Didi ta kalli Kawu ta ce, "Kawu yi haƙuri, ka tafi kawai Kawu." Ganin Omar zai fita ta ce, "Omar kar ka fita daga falon nan, Kawu mu je na rakaka." Omar jikinsa rawa yake saboda ɓacin rai ya fita daga falon. "Omar! Omar ka dawo!" Ta faɗa da ƙarfi amma ina ya fita daga gidan.
Kawu ya ce, "Aisha tsoro nake ji kar ya saka ayi min wani abun, haka kwanaki ya saka aka kusa hallaka ni." Ganin Kawu ya tsorata sosai sai ta ce, "babu abinda zai maka Kawu, tunda nace babu abinda zai yi babu ɗin, Kayi haƙuri."
"Ni zan bada haƙuri da na zo tunda na san baya so, ki yi haƙuri duk laifina ne ni na jawo wannan tsanar da yake mana." Didi ta ce, "Mu je kawu." Har ƙofar gida ta raka shi, ta ka ga su Bash kuwa suna jiran fitowarsa.
Kallon su tayi ta ce, "Kar wanda ya yiwa Kawu komai, in kuma wani abun ya same shi duk sai ranku ya ɓaci, ku faɗawa Damisar na ku ni nace a ƙyale shi. Kawu shiga motarka." Kawu jiki na rawa ya ce, "A'a Aisha."
"Kar ka damu Kawu babu komai." Kawu dai tsoro ne ya saka shi shiga motar ya bar unguwar a guje.
Didi gidan ta shiga cikin ɓacin rai ta shiga falo tana mamakin baƙar zuciya irin ta Omar da baya mantawa. Bai bar dangin uwa ba, haka ma dangin uban bai bar su ba. Har gwara ma na uwa tsanar da ya yi musu bata kai wacce ya yiwa su Kawu ba. A lokacin ya shigo tsakar gidan ya tsaya yana zagaye ransa a matuƙar ɓace zuciyar sawuya, fuskarsa tayi wani irin ga jijiyoyin kansa sun tashi. Abokin karawa kawai yake nema ya wuce a kansa.
"Assalamu alaikum, Didi na da......" Maganar Nayla ta maƙale saboda wanda suka haɗa ido dashi a cikin gidan. "A'uzubillahi minal shaiɗanir rajim!" Nayla ta faɗa a tsorace cikin gigicewa dan bata san ma ta yi ta'awizin ba. Omar ya sake wara ido a kan fuskarta cike da mamaki da fusata ya ce, "Shaiɗan!" Ya faɗa yana kallon Nayla tare da takowa zuwa inda take.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleemaâ¤ï¸
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
Â©ï¸ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
*Book 1*
*P 08.*Â Â Â Â Â Â
Nayla baya take ja yana takowa inda take idanunta a waje ƙirjinta yana up and down saboda tsoro da tashin hankali. Shi kuma yana takawa inda take saboda ɓacin rai da zallar haushi da takaici a zuciyarsa. Sai da ta jingina da bango ya dakata da bin bayanta, jikinta na rawa kar kar kar bakinta na motsawa amma ta kasa magana.
"Ni ki ke yiwa korar shaiÉ—anu? Wacece ke! Waye ya turo ki gidan nan!?."
Tsawar da ya yi ya sake firgita Nayla ta runtse idanunta cikin fargaba da tashin hankalin da bata taɓa shiga irin ta ba. Numfashita ya kusa ɗaukewa ganin ƙaramar wuƙar da ya zaro daga ƙasan takalminsa ya ɗago ya ɗora wuƙar akan wuyanta yana sake wara idanunsa waje ya ce, "Wacece ke!?."
Nayla bata taɓa shiga tashin hankali kamar yadda take a ciki yanzu ba, ƙafafunta sai rawa suke yi saboda tashin hankali, zuciyar tacike da dana sanin abinda ya shigo da ita gidan. "Omar!" Didi ta faɗa da hanzari tana zuwa ta janye Omar daga kusa da Nayla da take zubar da hawaye. Sharaf Nayla ta faɗi a numfashi ta na sama da ƙasa saboda tashin hankali.
"Baka da hankali ne Omar? Kashe ta zaka yi?." A fusace ya kalle ta ya ce, "Wacece ita? Ban ce kar na sake ganinta a gidan nan ba?."
"Gidanka ne da sai wanda ka ke so ne zai shigo? Na ce gidanka ne!?."
"Ba gidana ba ne, amma ina da ikon hana duk wanda bana so shigowa cikinsa. Ban son sake ganin wannan yarinyar a gidan nan, bana son sake ganin ta!" Ya faɗa da ƙarfi yana nuna Nayla da take zaune a baya kamar sumammiya.
Didi ta fusata sosai ta ce, "baka isa ba, baka isa ka hana baƙina shigowa gidan nan Omar. Wai kai Meya ke damunka? Meye a cikin kanka? Meyasa baka aiki da hankali ne kai?." Idanu ya sake warawa waje yana kallon Didi jin kalamanta musamman na ƙarshe ta ce, "eh na faɗa, Meyasa baka aiki da hankali? Meyasa ko yaushe zuciya ce take sarrafa tunaninka ba ƙwaƙwalwarka ba?." Kai yake girgizawa Didi ta sake cewa, "wacce irin zuciya ka ke da ita ne kai? Meyasa baka mantuwa baka yafiya?."
"Eh bana yafiya, kuma bazan yafe ba. Iya yau kin cece shi ya sha, amma wata rana zamu haÉ—u a lokacin da babu ke ko?."
"Ƙanin mahaifinka ne, ko ka ƙi ko ka so dole ka kira shi da Kawu." Ƙasa ya yi da muryar da yana girgiza kai cikin ƙunar rai ya ce, "Har abada bani da dangin mahaifi, bani da dangin mahaifiya, kamar yadda na rasa iyayena suma ki ɗauka sun mutu. Ke kaɗai na sani dangina, bayan ke babu wata halitta a duniyar nan da ta rage da zan kalle ta matsayin dangi!" Ya ƙarashe maganar da ƙarfin gaske.
"Ƙarya ka ke Omar, ƙarya ka ke. Kawu ƙanin mahaifinka ne duk da abinda ya aikata maka ba a canjawa tuwo suna. Baba Adamu Yayan mahaifiyarka ne, duk da abinda ya yi maka ba a canjawa tuwo suna. In dai har ka manta da dangin iyayenka to zaka manta da wanda suka haife ka Omar!."
Hannu ya saka ya daki kansa ya juya ya sake juyowa ya kalle ta ya ce, "iyayena sun rasu dan haka bani da wani a duniyar nan in ba ke ba."
"Nima ɗin baka ɗauke ni komai ba Omar, tunda baka yin abinda nake so." Sake kallon ta ya yi ya ce, "na rantse da Allah Didi, in na sake ganin ƙafar wani dangin Baba a gidan nan ranar bazai kwana lafiya ba. Zan iya ɗagawa dangin Mama ƙafa, amma bazan taɓa ɗagawa dangin mahaifina ƙafa ba. Ke kin san waye ni, kin kuma san abinda zan yi da wanda bazan yi ba."
Didi sai ta kasa magana dan baza ta iya da taurin kansa ba, tayi murmushin takaici kawai ta kalli Nayla da take zaune a wajan har lokacin kamar bata numfashi.
Da sauri ta ƙarasa inda take ta ɗago ta jikinta ta ce, "Nayla! Nayla buɗe idon ki don Allah." A hankali Nayla ta buɗe ido tana kallon Didi sai jikinta ya cigaba da rawa ta ƙanƙame Didi tana kuka sosai.
"Yi haƙuri Nayla, ki daina kuka don Allah ki yi haƙuri" ta faɗa tana shafa bayanta a hankali cikin tausayinta da mugun takaicin halin Omar.