Sashe 22
Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Omar ya girgiza kai ya ce, "wai abinda ka ke yi mata nima shi zan yi?."
"Fiye da haka ma."
"Ba a haifi yarinyar da zan yiwa wannan abun ba." Yahya yayi dariya ya ce, "Tunda har ka karɓi aiki da Hajiya Narma sai kayi haƙuri kawai, duk abinda ka ke faɗa yanzu a baki ne, amma zaka tabbatar da magana ta gaskiya ce." Kallon idon Yahya ya yi ya ce, "nayi maka kama da wanda yake wasa?."
Kwarjini ya yiwa Yahya sosai sai ya girgiza kai ya ce, "A'a, amma ina baka shawara." Omar ya É—auke kai suka yi sallama da Yahya ya tafi.
Fanfo ya gani daga can gefen compound ɗin kuma yana fa buƙatar yin sallah, ya ƙarasa yayi alwala, ya juya yana kallon gidan a nan ya ga wani ƙaramin masallaci da mai gadin da ya buɗe musu ƙofa a ciki, Omar ya nufi wajan kai tsaye da niyar yin sallah. Narma ce ta fito ta canja shiga zuwa riga mai jikin roba ta kama, sannan daga sama wuyan a buɗe yake ana iya hango saman ƙirjinta. Narma ta ce, "kai!." Bai ko kalle ta ba balle ya saka ran dashi ta ke, ta sake cewa, "da kai nake."
Nan ma Omar bai kalle ta ba sai ma cigaba da tafiya da yayi, mai gadin da yake zaune a cikin masallacin ya taso da sauri ya tari Omar ya ce, "Abokina magana Hajiya take maka." Omar ya kalle shi ya ce, "magana?."
"Eh, gata can tana magana."
"Ba da ni take ba." Muryar Narma ya ji a bayansa ta cewa, "Waye kai ina yi maka magana baza ka amsa ba?." Nan ma bai motsa ba balle ya kalle ta.
Shan gabansa tayi tana kallonsa daga sama har ƙasa ta ce, "ba kai ne Tiger ba? Kana ji ina yi maka magana zaka yi min banza waye kai?." Ganin yayi shiru bai amsa ba ya dai zuba mata ido har hakan ya saka ta janye idanunta ta ce, "charger zaka je ka siyo min yanzun nan, ka bar shiga masallacin ka je ka siyo min."
_Tashin hankali, haka za a yi da yarinyar nan?, ni zata tsayarta ce zata aika? Ni take yiwa tsawa? Lallai kafin na gama aiki da ita sai dai a kai gawar ta Abuja._ Abinda yake aiyanawa kenan yana ƙare mata kallo cikin ɓacin da ya baya bayyana akan fuskarsa.
Ta buÉ—e baki zata yi magana ya ce, "in kika sake yi min magana sai na yi ball dake a wajan nan, sa'anki ne ni ko yaron ki ne..? bani waje!?" Ya faÉ—a da tsawa idanunsa na waje yana kallon ta.
Narma bata san ta daka tsalle ta koma gefe ba sai sautin tsakinsa ta ji ya shiga masallaci yana ayyana dole ma ya kira baban yarinyar nan bazai juri wannan shirmen nata ba, ko ya ajjiye aikin da ya karɓa ko a wayi gari yayi mata illa.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleemaâ¤ï¸
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
Â©ï¸ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
*Book 1*
*P 10.*
Narma suman tsaye tayi ta bishi da kallo cikin faɗuwar gaba, ba a taɓa yi mata tsawa ba sai yau, tsawar ta ratsata sosai shiyasa bata san ta koma gefe ba. Sai da ta dawo hankalinta ta kalli ma'aikatan gidan ta ga kowa kallon ta yake yi rai a ɓace ta wuce cikin gidan a guje. Tana shiga babban falon gidan ta ɗauki waya hannu na rawa ta kira mahaifinta.
Yana É—auka kafin ya yi magana ta ce, "Dad waye wannan ka haÉ—a ni dashi? Dad tsawa fa yake yi min ina yi masa magana yayi min banza. Kuma tun airport ko sannu da zuwa bai yi min ba, kamar ma bai san ya É—auko ni a mota ba. Gaskiya Dad bazan jure zama da wannan mutumin ba na gaji."
Senator da yake sauraren ta sai da ta gama ya ce, "Æ™yale ni dashi zan kira shi yanzu a waya, kin sauka lafiya?." Da shagwaÉ“e ta ce, "lafiya lau Dad. Charger na ce ya siyo min na bar tawa a gida kaga yadda ya yi min tsawa kamar ni ce nake aiki a Æ™asansa? Babban abin É“acin ran a gaban maids É—in gidan nan. Gaskiya Dad i can't toleret this kind of nonsense." Dad ya ce, "don't worry my dear, zan kira shi yanzu."Â
"And let him come and say sorry to me Dad." Senator ya yi murmushi ya ce, "hold on, i'm coming." Kashe wayar tayi ta nemi waje zauna tana lissafa kalar wulaƙancin da zata yi masa.
     Omar kuwa tun yana sallah yake jin kiran waya na shigowa wayarsa, bai katse sallar ba sai da ya idar sannan ya duba wayar ganin mai kiran sai yayi ƙaramin tsaki ya taso ya fito daga masallacin. Car park ya ƙarasa, daga gefe akwai madaidaiciyar gazebo ta shan iska da kujeru a ciki nan ya shiga ya zauna, yana zama wayarsa ta ɗauki ƙara ya ɗauka ya saka a kunne.
    Daga can ɓangaren Sen ya ce, "Tiger." Omar ya amsa suka gaisa kafin ya ce, "Tiger Narma ta kira ni ta ce kayi mata tsawa dan ta ce a siyo mata charger." Omar ya ce, "ba ɗan aiken ta bane ba ni, haka zalika ni ba yaron ta bane. Saboda kai na karɓi aikin nan, kai ta wajan da take so shine abinda ka ce zan yi, amma ba wai dan ta saka ni a gaba tana yi min ihu ba. In a haka za a tafi gaskiya zan ajjiye aikin nan sai a samo wani, ni bazan jure ba."
Senator ya ce, "bata san waye kai bane shiyasa, Amma zan mata magana za a samu mai yi mata aike da siyo mata abinda take so, kai dai kai nake so ka dinga kai ta inda zata je." Omar ya ce, "bazan dinga zama a nan ba gaskiya, zan dinga tafiya in zata fita sai ta sanar dani nazo na kaita." Senator ya ce, "Daman ni abinda nake so shine ka kaita ka kula da lamarinta a duk inda take." Omar ya yi shiru Sen ya ce, "ina zuwa" ya faÉ—a yana yanke wayar.
Omar yana nan zaune bai san me ya faru ba sai yaga Yahya wanda suka rabu ya dawo ya shiga gidan ba jimawa ya dawo ya hau mota ya fita. Taɓe baki yayi dan a kaf duniya bai ga macen da zata aike shi ba in dai ba Didi ba. Tsabar raini shi zata dinga yiwa tsawa ta ɗauka shi yaron ta ne?. Bai jima sosai a zaune a wajan ba kawai ya tashi bayan ya bawa Yahya key ɗin motar da ya bashi ya fita daga gidan.
A can Abuja kuwa Dad yana yanke wayar Mum ta kalle shi a fusace ta ce, "ni fa tun asali ban so ka haɗa riƙaƙƙen ɗan daba da ƴata ba, ta ya ya za a ce kaf jami'an tsaron da suke Kano ka rasa da wanda zaka haɗa ta sai da ɗan daba?. Waye shi da zai mata tsawa har yake ganin yafi ƙarfin ta aike shi? Ba a ƙarƙashin ka yake ba?."
Nabil da yake zaune shima rai a ɓace ya ce, "abinda zan ce kenan Mum. Ta ya zai mata tsawa har kuma Dad ka biye masa ka ce wai in zata yi aike ta aiki Yahya? Kenan shi ya fi ƙarfin ta aike shi ko me?. Gaskiya Dad wannan ba wanda za a zauna dashi bane, ina bayan Mum ka salleme shi kawai a tura mata wani ya dinga kaita duk inda yake so. Wani ƙazami dashi har yana da bakin da zai ce wai baza ta aike shi ba? Waye shi?."
Mum ta kuma ɗora da cewa, "ba kowa bane face ɗan iska gari na banza da wofi, matsayin numfashi su ma ba ɗaya bane amma Dear ya saka tana shaƙar gurɓataccen numfashinsa a mota ɗaya. Tsakanin ta dashi shine mahaifinta ya biya shi ya ne ya tayar da hayaniya a wajan zaɓe da sauran su, amma matsayin ya haɗa mota ɗaya da Narma sam-sam bai tashi ba."
Dad yayi murmushi yana kallon su ya ce, "na fi ku tsanar kusancin da ya samu da Narma saboda bashi da wannan matsayin kuma bazai taɓa samun sa ba har abada. Tsakanin Narma dashi kamar tazarar sama da ƙasa, turaren da Narma take sakawa sai ya siyi danginsa kaf balle kuma agogon da take ɗaurawa a hannunta. Ban haɗa shi da Narma dan ya yiwa Narma wani abun ba, na haɗa ta dashi ne na ɗan lokaci saboda lafiyar ta da zaman ta lafiya a Kano. Ke kin san wancan lokacin abinda ya faru da ita, tare musu hanya aka yi ana ƙoƙarin saceta in ba dan Allah ya tsare ba da yanzu wataƙila bata gidan nan. Shi kuwa kaf kano a san shi, in baka san shi ba ka san sunan shi, ana faɗar sunansa shikenan duk iskancin da ka ke ki dashi ka ajjiye. Saboda haka kawai na bashi Narma ya dinga kai ta duk inda zata je, in ba dan haka ba haɗa ido ma bai kai matsayin da Narma zata yi dashi ba."
Nabil ya ce, "Amma Dad akwai police a Kano da zaka ɗauka a haɗa ta dasu ta je duk inda take so, suna da bindiga shi kuwa bashi da ita, sun san aikin su shi kuwa me ya sani ban da wasa da wuƙa?. Gaskiya Dad ban ji daɗi ba, wani ƙazamin bagidaje dashi har yana da zarrar da kana yi masa magana yana cewa wai zai ajjiye aikin saboda baya son raini? Just Imagine, wani banza shashasha talaka ne yake faɗawa ƴar senator haka."