← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 54

Sashe 10

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abinda taji an faɗa kenan cikin kakkausar murya. A hankali ta juyo a firgice suka haɗa ido nan take gabanta ya yanke ya faɗi. Kafin ta tattaro abinda zata ce ya ware murya cikin tsawa ya ce, "Nace Wacece ke!? Me kika yi a zaune a na wajan?." Nayla tsabar tsoro bata san ta miƙe tsaye ba, jikinta na rawa nan da nan ido ya cika da hawaye abin ka da ƴar shagwaɓa.

"Goje!, Tk!, Bash! kuna Ina!" Ya faɗa da ƙarfi yana kallon ƙofa, sai gasu sun shigo falon da hanzari. Nayla ya nuna musu ya ce, "ya akayi wannan ta shigo gidan nan? Wacece ita? Kenan in bana nan barin kowa ku ke yi ya shigo!?." Goje ya kalli Nayla da har lokacin jikinta yake rawa cikin tsawa ya ce, "Ke daga ina ki ke!? Waye ya baki izinin shigowa gidan nan?."

Numfashi take ja daƙyar hawaye na sakkowa daga idonta, ta saka magana balle ta iya cewa wani abun. "Ba magana ake miki!?."
"Cha....ji....na....ka...wo..." a fusace Omar ya ce, "Nan gidan kawo chaji ne? Ku fitar min da yarinyar nan yanzu."

Didi da take banɗaki take jiyo amon maganarsa da hanzari ta fito dan da tasan zai shigo baza ta bar Nayla ita kaɗai ba, ta san sai an yi haka. Tana fitowa falon ta ce, "Kar wanda ya taɓata."

Cak suka tsaya da ƙarasowa inda Nayla take ta jawo hannunta zuwa kusa da ita sai kawai ta fashe da kuka ta kwanta a jikin Didi. Didi ta shafa kanta ta ce, "yi haƙuri Nayla, da na san zai dawo yanzu da ban barki ke kaɗai ba, Zauna" ta faɗa tana zaunar da ita akan kujera.

Omar ta kalla fuska babu walwala ta ce, "kai wai meyasa ka ke haka ne? kenan bazan yi baƙi ba sai wanda ka sani?. Haka kawai daga dawowarka kazo ka fara yiwa ƴar mutane ihu ba tare da ka santa ba? Kenan bazan yi baƙuwa ba lallai sai ka santa? Meye haka ne?."

Kallon Didi yayi amma bai ce komai ba ta kalli su Goje ta ce, "kenan ku ne masu yi masa gadina, sai baƙin da ku ka ga dama sannan zasu zo su ganni ko?." Zasu yi magana ciki tsawa ta ce, "ku fice ku bani waje!." Dole suka cika umarninta suka fita. Didi ta dawo da kallonta gare shi ta ce, "kar ka sake ganin baƙuwata ka sake yi mata ihu, in kai baka buƙatar baƙi ni ina buƙatarsu, wajena tazo ba wajanka ba dan haka babu ruwanka da ita."

Wani irin yake ji a jikinsa da zuciyarsa, ya zubawa Didi ido cikin abubuwan da suka tarar masa a ƙirji. Na farko kukan da Nayla take yi yana daga cikin abinda yake sake harzuƙa shi, a ganinsa dan shagwaɓa shi zata saka a gaba tana yiwa kuka, me aka yi mata?. Na biyu faɗan da Didi take masa a gaban baƙuwa yafi komai ɓata masa rai. Ta fi kowa sanin baya so ayi masa faɗa a gaban mutane balle kuma mace baƙuwa wacce bai santa ba, babban abin haushin ma ko gaisawa bata tsaya sun yi ba ta fara yi masa faɗa akan wata wacce bata da alaqa da ita.

Kallon Nayla ya yi a fusace ya ce, "dalla malama ki yiwa shiru ko na yanka bakin ki!." Wata irin firgita Nayla tayi sai gata ta dawo ƙasa daga kan kujera ta cure waje ɗaya jikinta na tsuma. Babu zato babu tsammani ta ji maganar shiyasa ta gigice.

Didi ta sake fusata ta kalle shi ta ce, "Omar fita ka bar min falo." Ido ya waro waje jin mamakin abinda tace, a daidai lokacin da Nayla ta kalle shi sai ta sake gigicewa ganin idanunsa kamar za a saka hannu a cire saboda girma. Kafin ya yi magana ta sake cewa, "na ce ka fita ko!?." Bai ce komai ba ya juya ya fita a zuciyarsa yana tabbatar da dole ma ya hukunta Nayla duk da bai santa ba.

Didi ta koma kusa da Nayla ta riƙe ta ta ce, "yi haƙuri Nayla, taso ki zauna." Ta faɗa tana taso da ita ta zaunar da ita akan kujera ta kawo mata ruwa mai sanyi ta ce, "sha ruwa." Ba musu ta karɓa tasha tana sauke ajiyar zuciya. Didi ta kalli gaishe ta sai ta bata dariya ganin hawaye shaɓe-shaɓe fuskarta har tayi ja kamar wacce aka yiwa duka.

"Yi haƙuri kin ji, haka nan yake shi in yaga baƙo ko baƙuwa in bai san su ba shikenan sai faɗa. Ki nutsu ai ya tafi ki goge hawayen nan."

Nayla ta goge idanunta tana jan numfashi amma har lokacin a tsorace take. Sai da Didi taga ta nutsu sosai sannan ta sake cewa, "kar ki damu bazai sake yi miki haka ba." Nayla ta ce, "ai bazan sake zuwa ba ma Didi, bara na É—auki waya
ta na tafi."

Didi tayi dariya ta ce, "Wallahi babu inda zaki je, kuma in baki shigo gidan nan ba shi zan saka ya ɗauko min ke a wajan Hajja." Nayla tayi gum bata ce komai ba amma zuciyarta cike take da tsoron sa, bata taɓa ganin halitta ta mutane wacce take tsoro kamar sa ba.

Ganin ta yi shiru sai Didi ta tashi ta shiga kitchen ta É—auko abincin da ta dawo kusa da Nayla ta ce, "ko zaki kai masa abincin?." Yadda Nayla tayi da idanu cikin firgici ya bawa Didi dariya ta ce, "wasa nake kwantar da hankalinki" ta faÉ—a tana fita tana dariya dan wallahi yadda ta tsorata dariya ta bata.

Setroom ɗin da yake gidan wanda ya kasance ɗakinsa ta nufa, kafin ta ƙarasa ya fito har yayi wanka ya canja kaya zuwa na shan isa, dan rigar jikinsa ko hannu bata dashi sai wando wanda ya wuce guiwa da kaɗan. Kallon sa tayi ta ce, "sai mu koma ka ci abinci." Bai kula ta ba sai ma sake tamke fuska da yayi yana kallon ƙofar ɗakin da alama tana ciki tunda ga takalmin ta nan.

Didi ta ce, "Magana nake maka Omar." Nan ma ya share ta dan tsakani da Allah in ba dan ita bace da yanzu ba wannan labarin ake yi ba, ta bashi haushi sosai. Itama sai ta É—aure fuska ta ce, "ina yi maka magana kayi min banza."
"Me zan ce miki? Kin nuna waccan abar ta fi ni" ya faÉ—a cike da jin haushi.
"To haka kawai daga ganin yarinya sai ka fara yi mata ihu baka san ta ba baka san daga inda take ba? kai baza a yi baƙi a gidan nan ba kenan?."

Ya kalle ta ya ce, "duk wanda zai zo gidan nan munafuki ne, yana zuwa yaga ya muke rayuwa ni dake." Didi ta ce, "in ma hakan ne babu ruwan ka, kar wata baƙuwata ta sake zuwa kayi mata abinda ka yi yanzu, Wajena suka zo ba wajanka ba." Ya kalle ta ya taɓe baki ya nuna kansa da yatsa ya ce, "ni ki ka yiwa faɗa a gaban wata yarinya, ni kika yiwa tsawa har ki ka ce na bar miki falo kuma duk a gabanta. Ni ko Didi?."

Didi ta kalle shi dama ta san zai ji haushi ta ce, "kaine ka jawo, lokacin da ka shigo da kun gaisa ka shiga ɗaki inda nake ai da hakan bai faru ba." Ya girgiza kai cikin ƙunar rai, baƙin ciki yake ji zuciyarsa, kamar shi tiger Didi ta yi masa faɗa akan wata banzar yarinya wacce bai ma santa ba. Ya kalli Didin da take kallon sa cike da ɓacin rai ya ce, "ni wai kika kora a gaban wata, ni Omar hmm....." ta kalle shi ta ce, "meye hmmm? Kar ka cutar da ƴar mutane, kar ka saka a zubar mata da jini."

        "In ki ka ce kar ayi ɓata bakinki ke yi, zata san ta shigo gidan mu ta saka chaji har an yi min faɗa a gabanta. Nan gaba aka ce ta shigo baza ta yi wannan marmarin ba."

Ganin yadda yake cize baki yana maganar ya saka Didi ta ajjiye abincin da ta taho masa dashi ta riƙe hannunsa ta ce, "Omar kar ka saka ka cutar da ita, na faɗa maka kar ka yi mata komai." A fusace ya cire hannunsa daga nata ya ce, "to meyasa zaki yi min faɗa a gabanta? Meyasa?. daga wani gari na dawo ko tsayawa baki yi mun gaisa ba ki ka fara yi min faɗa." Didi ta ce, "shikenan nayi kuskure, amma kar ka yi mata komai na sake faɗa maka."

Kai ya girgiza dan maganar bata wani shige shi ba ganin haka Didi ta ce, "wai baka gane ta ba ma?." Kallon ta yayi alamun na san ta ne daman, ta ɗaga kai dan tana fahimtar saƙon ido in ya yi mata tunda ya saba ta ce, "ka san ta mana, Nayla ce fa jikar Hajja. Yarinyar da aka taɓa ƙoƙarin yi mata fyaɗe ka cece ta ka dawo da ita wajan Hajja?. Ka tuna har ka dinga yiwa Hajja faɗa akan ne aka barta ta fita ita kaɗai bayan a san baƙuwa ce bata san gari ba, ka tuna?."

Kallon Didi yayi jin abinda take cewa dan ya tuna abinda ta ce É—in tsaf a ransa, har hango lokacin yake yi a idanunsa da yadda komai ya faru. Amma bazai gane ta ba, dan a yanzu ma ba ganin fuskarta ya yi sosai ba, gwara ma a da É—in ya san fuskarta saboda suna haÉ—uwa bayan abin ya faru tana yawan zuwa wajan Didi kafin ta bar garin. Bazai manta da ita ba dan ta silar ta ya fara yankewa wani É—an yatsa a duniya, tabbas a kanta ya fara zubar da jini saboda ceto. Batu ake na shekara tara zuwa goma baya ta ya zai gane ta banda abin Didi?.

"Ni ban san ta ba, ina kallonta a matsayin wacce ki ka yi min faɗa a gabanta" Abinda ya ce kenan ya wuce ya barta a wajan tayi dariya tana jinjina son girma, da son mulki, da zafin kai irin na ƙanin nata, abincin ta shigar masa dashi ɗakim sannan ta koma wajan Nayla.
Chapter 10 · 0% Book details