← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 54

Sashe 46

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Narma ta katse shi ta ce, "Not at all. Dad...!" Ta faɗa tana jan sunan tare da kallon sa. Ta ce, "promise me you will allow me to marry him at any cost." Dad ya riƙe hannunta ya ce, "I promise you zaki aure shi indai yana sonki, abinda bazan amince ba shine in baya sonki bazan yarda ki aura shi ba." Ta yi murmushi ta ce, "Dad I'm Barr Nass don't forget, i will attract his attention."

Dad ya yi murmushi ya ce, "anything for you my daughter. Kema ki yi min alƙawarin damuwarsa baza ta sake baki damuwa har ki yi ciwo ba." Narma ta girgiza kai ta ce, "in sha Allah." Rarrashinta suka dinga yi suna bata baki har ta ware ana hira da dariya da ita.

Bayan Kwana biyu.

Narma ta tabbatarwa da kanta Omar shine farin cikin ta dole ta san ya zatayi kafin ta rasa ranta, duk da tayi ƙoƙarin ajjiye damuwar ta kamar yadda ta yiwa mahaifinta alƙawari amma soyayyar tana nan a tare da ita. Ta daure bata nemi Omar a kwanakin ba tana so taga zai kira ta ko bazai kira ta ba.

Abin mamakin bai kira ba kuma bai yi mata koda text ba, sai ta tabbatar da gaske bai É—auki maganar ta da mahimmaci ba tunda gashi ya share ta bai kira ya ji ya take ba.

Shi kuwa Omar shi kansa ya san ya damu da lamarin Narma, daurewa kawai yake yi yana nuna bai damu ba amma a zuciyarsa ya damu da ita sosai ma kuwa. Bai san dalilin da ya saka ya damu ɗin ba, shi ba sanin so ya yi ba balle ya ce sonta yake yi. Bai taɓa ƙoƙarin kiranta ba,
dan shi kansa ya san bazai iya neman ta ba ko meye zai faru, dalilin da ya saka ya jure rashin jinta ya share ya bar tunaninta.

Kamar ko yaushe yana zaune cikin ƴan uwan sa ƴan daba ana meeting akan ƴan wata unguwa suna faɗa kuma ana cewa ƴan unguwar su ne. Yana zaune yaji kiran waya amma bai duba ba har suka gama meeting ɗin da bai ce komai ba, hankalin sa baya tare dashi shiyasa bai ce komai ba. Ana gamawa ya tashi ya nufi gida. Yana shiga ɗaki wayarsa sake yin ƙara ya ɗauko tare da zubawa number ido, har lokacin bai yi saving ba dan baya so ba, kawai baya so ya bada wata ƙofa da wani abun zai shiga ransa.

Kamar bazai É—auka ba sai kuma ya É—auka tayi shiru bata ce komai ba shima bai ce komai ba. Nunfashinta kawai yake ji yana sauka a hankali, saukar numfashinta sai ya saukar masa da kasala sosai ya yi shiru bai ce komai ba.
"Da ban kira ka baza ka kira ni ba ko? Ka san damuwar da na shiga a kanka kuwa? Ka san har asibiti na kwanta saboda kai?. Saboda Ina sonka ka ke min haka ko Faruk? Shikenan na gode" ta faÉ—a a sanyaye.

Lumshe ido ya yi zuciyarsa na bugawa sosai, in ya ce bai ji daɗin maganarta ba ƙarya yake yi, in ya ce bai ji maganar ta na shiga zuciyarsa ba ƙarya yake yi, in ya ce bai ji rauni ya mamaye zuciyarsa ba ƙarya yake yi. Buɗe ido ya yi har lokacin bata sake magana ba yana dai jin nunfashin ta kamar ɗazu.

Shiru ya rasta tsakani har mintina biyu sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "shikenan ka gaishe da Didi."
"Ya hanya?" Ya tsinci muryarsa ya faÉ—a ba tare da ya shirya ba. Narma jin maganar sai tayi ajiyar zuciya mai nauyi ta ce, "hanya ba lafiya ba, ni kaina ba lafiya nake ba Faruk."
"Ayya Allah ya bada lafiya" ya faÉ—a a hankali.

Narma ta ce, "Amin,Thank you." Nan ma ya sake yin shiru bai ce komai ba, Narma ta ce, "Okay byee" ta faÉ—a tana yanke wayar da sauri. Shiru yayi yana kallon wayar yana mamakin kansa da ya tambaye ta hanya, to Ina ruwansa?. Numfashi ya sauke, ya saka a ransa tausayinta yake ji shiyasa haka da wannan tunanin ya share wancan.

•••••••

        Mutanen Saudia sun dawo Kaduna, Nayla har lokacin bata dawo daidai ba domin abinda take ji yafi ƙarfin zuciyarta. Nauyi take ji kamar dutse aka ɗora mata a ƙirjinta, wani lokacin numfashi wahala yake mata saboda nauyin da zuciyarta tayi mata. Washe garin da suka dawo Twiny ta juya Kano saboda mijinta ya gama komai na gida. Sai ta sake zama shiru-shiru bata da abokin shawara, gashi tana son zuwa Kano amma tana tsoron Abiy kasancewar bata jima da dawowa ba.

Kamar yadda ta zaɓarwa kanta kullum tana ɗaki a zaune sai ga autan su ya shigo ya ce Abiy yana kiran ta. Sai da ta daidaita nutsuwarta sannan ta fito ta same shi a falon da shi kaɗai yana kallon tv. Da sallama ta shiga ya amsa yana bita da kallo tare da tattara nutsuwar sa gabaɗaua a kanta.

Sai da ta zauna sannan ya ce, "Mamana dawo kusa dani" ya faÉ—a yana nuna amsa kan kujerar da yake. Ba musu ta tashi dawo kusa dashi ya fuskance ta ya ce, "Mamana baki da lafiya ne?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "bana son body language, ki yi min magana."
"Lafiyata lau Abiy." Abiy ya ce, "ƙarya ki ke yi, tun a Saudia kika canja gabaɗaya. A wancan lokacin na karɓi dalilinki ne kawai saboda kar na takura ki, amma ba dan na amince da abinda ki ka ce ba. Me yake damun ki kika koma haka? har rama naga kin yi, me ya faru?."

Nayla tayi shiru bata ce komai ba Abiy ya ce, "ban kai na ji damuwarki ba?." Da sauri ta ce, "A'a Abiy."
"To faÉ—a min."
"Babu ne shiyasa."
"Kar ki yi min ƙarya Mamana, ƙarya ba halin ki bane. Ki faɗa min gaskiya kafin na gano da kaina." Nayla ta ce, "da gaske nake Abiy, babu abinda yake damuna."

Abiy ya yi shiru yana kallon ta cikin nazari, bai yarda da abinda ta ce ba, ya san kawai bazata faɗa bane amma zai san yadda zai yi mata. Ya sauke numfashi ya ce, "shikenan. Ga offer ki" ya faɗa yana miƙa mata takarda.

Nayla murmushi tayi cikin farin ciki ta karɓa Abiy ya ce, "Federal inland revenue service ne. Ranar Monday zaki je ki gama duk abinda ya kamata." Nayla cikin farin ciki ta ce, "Abiy na gode, Allah ya saka da alkhairi ya biya ka da aljanna." Murmushi ya yi ya ce, "Amin Nayla. Sai zancen shagon ku keda Twinyn ki, za a ƙara muku jari ku cigaba da juya kuɗin, Kwana biyu ma ke bakya zuwa."

Nayla farin cikin samun aiki duk ya cika mata zuciyata, burinta a rayuwa kawai ta yi aiki shiyasa Abiy ya samar mata. Ta ce, "Abiy ni na rasa me zance saboda murna." Murmushi ya yi kawai yana kallon ta ya ce, "Nayla kenan. Akwai abinda ki ke so bayan wannan?."

Nayla tana murmushi ta ce, "babu komai Abiy. Kawai Ina so na kaiwa Hajja tsarabarta ne." Murmushi ya yi ya ce, "Nayla sarkin zuwa Kano, Ke dai kina son shiga Kano." Tayi dariya ta ce, "Kano da daÉ—i Abiy."
"Shikenan, in kin shirya sai ki je gobe ki yi kwana biyu ki dawo."

Farin cikin da Nayla taji ko da ya miƙo mata offer bata ji ba, hakan ya bayyana a kan fuskarta sosai da murya ta ce, "Na gode Abiy, Allah ya saka da alkhairi ya jiƙan mahaifa, Allah ya jikan Ummana." Murmushi ya yi ya ce, "Amin. Bani offer ɗin kinje ki shirya." A guje ta miƙe ta shiga ɗaki tana murna.

Cikin murna ta yi ajiyar zuciya ta zabura ta buɗe trolly bag ta fara zuba tsarabar Hajja da ta Salma har da Didi ma. Wata maroccon jallabiya ta maza ta ɗauko kalar baƙa mai kyau da santsi ta kalla ta ce, "zata yi masa kyau sosai." Murmushi take kamar shashasha, tana hango in Omar ya saka rigar ya zai koma. Da haka ta gama zuba kayan a jakar tafiya Kano.

Wayarta taji tana ƙara da ta duba sai ta ga Abiy ne, tana ɗauka ya ce, "Mamana ki bar zuwa Kano gobe a gama settling aikin nan da kika samu, in aka gama kafin ki fara aiki sai ki je ki dawo. Yanzu ake sanar dani gobe ake so ki je." Sai jikinta ya yi sanyi ta ce, "to Abiy" daga haka ya yanke wayar ita kuma ta zauna gabaɗaya murna ta koma ciki.

Nayla Anya kuwa🤔

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 22.*

Kwance tashi babu wahala a wajan Allah, a hankali zuciyar Narma ta fara rinjayar zuciyar Omar, tun tana kira yana ƙin ɗauka har ta kai in bata kira shi bama baya jin daɗi. Gashi da shegiyar izza shi bazai iya kiranta ba, in ta kira kanta ta yiwa, in bata kira ba bazai kira ba.

Tun yana ƙaryata kansa akan yana sonrta har ya amince da gaske yana sonta, kuma shima ya shirya auren ta kamar yadda ta shirya aurensa. Ranar da ya bayyana mata kamar zata yi hauka saboda murna, duk da bai yi wasu dogayen kalamai ba, kawai ya ce mata shima zai iya aurenta daga nan bai ƙara koda kalma ɗaya ba. Narma ta dinga murna tana farin ciki, shi kansa farin ciki yake yi, duk da wani lokacin sai ya ji kamar soyayyarta ta bar zuciyarsa, bayan kwana biyu sai ta dawo.

Duk da basa haÉ—uwa amma babu laifi sun saba a waya, da yake ba aikin yi ne dashi ba in dai zata kira shi zata same shi, shine dai bai cika kiran ta sosai ba.
Chapter 46 · 0% Book details