Sashe 45
Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin ya yi shiru bai ce komai ba ta kuma cewa, "Zancen yaushe ta fara sonka duk daga baya ne, zuciya tana fara son wanda mutum bai taɓa gani ba, ana fara soyayya a iya jin murya kawai. Mace na fara son namiji in taji muryarsa a tv ko radio, haka namiji yana fara son mace in yaji muryar ta koda a hanya ne."
Shi Omar mamaki abin yake bashi shiyasa ya kasa magana, ya sake kallon ta ya ce, "wai da gaske yana faruwa a gaske ko sai a film? Ni ban amince da soyayyar ba, ban amince akwai wani abu soyayya a duniya ba. Ina jinta tamkar tatsuniya, ina jin labarin soyayya kamar iska da zata zo ta wuce ba tare da ka ganta ba, ina jin labarinta tamkar tafiyar ruwa. Ban amince akwai soyayya ba Didi, ni ban yarda akwai ta ba balle har na yarda da son da wata take min."
Didi tayi murmushi tana girgiza kai ta ce, "Zaka amince da akwai soyayya Omar, zaka tabbatar da soyayya gaskiya ce a lokacin da ka fara son wacce ka ke so, daga wannan lokacin zaka tabbatar da soyayya ba film bace ko wucewar iska. Yanzu babu abinda ka sani sai ni, soyayyar Yaya da É—an uwanta kaÉ—ai ka sani, baka san ko wanne irin so ba sai ita, baka san son ko wacce mace ba sai ni, baka jin ko wacce mace a zuciyarka sai ni É—in. A yanzu baza ka gane ba, sai zuciyarka ta fara son wata mace sannan zaka tabbatar. Yanzu meye mafita akan Narma?."
"Mafita kamar ya?."
"Ya zaka yi da ita?. Misali ace da gaske tana son naka, ya zaka yi mata?."
"Haƙuri zata yi Didi, me zan yi mata?." Didi ta ce, "Haka nake so naji ka ce, domin Narma ba kalar wacce zaka yi gangancin fara so bace, in ka bari zuciyarka ta yaudare ka ka fara sonta wallahi kaine a ruwa domin kaine zaka sha wahala. Mallakar Narma abu ne mai wahala a wajan namiji irinka, in kuma kaga hakan ya faru to sai dai tsananin rabo."
Omar ya murmusa kaɗan ya ce, "ban san meyasa kike faɗar wannan maganar ba, ni ban cancanci a soni ko a aure ni bane?." Didi ta girgiza kai ta ce, "ka cancanta mana, ka cancanta a wajan wanda ka cancani kaso a soka. A wajan Narma, ko a wajan masu matsayin na ƙasa da ita wallahi baka cancanta ba Omar. Ba maganar hasken fata ake yi ba, ba maganar kyau ko sajen fuska da ƙirar jiki ake ba Omar. Magana ake ta karatu da kuma kuɗi, magana ake ta asali mai kyau, in ma asali na kuɗi ko na sarauta. Omar duka wannan baka dashi, kaga kenan a wajan ta baka cancanta ba, ba ita kaɗai ba har masu biye mata."
Ransa yaji ya É—an sosu akan maganar Didi, ya zuba mata ido yana kallon ta kafin ya ce, "Shi mutumin da bashi da karatu ko bashi da kuÉ—i ba mutum ba ne?." Didi ta ce, "Mutum ne mana Omar, amma a gidan Senator Kano central ba mutum bane wallahi."
Kallon Didi yake yi kawai bai ce komai ba, kamar zai yi magana sai ya fasa bai ce komai ba ya kawar da kai gefe. Didi ta tausasa ta ce, "Ka bata haƙuri Omar, in mahaifinta yaji tana sonka ma wani babban tashin hankalin ne, kar kaga kuna waya dashi ko kana zuwa inda yake yana yi maka dariya. Wallahi dariyar nan ta manufa ce Omar, ba tsakani da Allah yake sonka ba amfani yake yi da kai. Da zarar ya ji ƴarsa na sonka duk wannan zai gushe, saboda ba matsayin ku ɗaya ba."
A fusace Omar ya ce, "Saboda ita muslma ce ni kafiri shiyasa ki ke kiran ba matsayin mu ɗaya ba?." Mamaki ya bawa Didi ganin yaji haushin abinda tace, har ya kasa ɓoyewa ya nuna mata hakan. Didi ta ce, "a wajan su gwara kasancewar ka kafiri akan kaje a yadda ka ke kace kana sonta Omar."
Didi ta ta sake tausasa murya ta ce, "Ni don Allah ka rufa min asiri kar ka bari wannan kalaman nata ya yi tasiri a kanka, yadda na sanka baka bawa kowa ƙofa a rayuwarka itama kar ka bata, ka ɗauka komai ba komai bane ka manta da ita, ka toshe duk hanyar da zata bi wajan neman ka."
Omar ya zuba mata idanunsa yana zagawa dasu a fuskarta ya ce, "Yanzu kika gama faÉ—a min baka sanin lokacin da soyayya take shiga zuciyarka, nima in soyayyarta zata shiga zuciyata zan hana ne?."
Gaban Didi ya faÉ—i jin kalamansa, tsoron ta É—aya kar taje ya fara son Narma ta shiga uku. Didi ta ce, "Addu'a zaka yi Allah kar ya baka ikon fara sonta." Baice komai ba ya fita yana mamakin wannan kalamai na Didi masu kama da rainin hankali.Â
Didi da kallo ta bishi a bayyane ta ce, "Wai Narma ke son Omar...Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ya Allah ka kiyaye min ƙanina daga faɗawa tarkon soyayyarta, gwara ce itace take sonsa da ce shine yake sonta, gangancin fara son Narma kamar ganganci da rayuwarsa ne. Ya Allah kar ka bashi ikon fara son wannan yarinya" ta faɗa kamar zata yi kuka.
••••••
    Narma da zazzaɓi mai zafi ta sauka a Abuja, ta kira Najwa ta ce tazo ta ɗauke ta, ba jimawa sai gata ganin yanayin da take ciki sai ya bata tsoro ganin da gaske bata da lafiya kawai ta wuce asibiti. Sai bayan sun je asibitin an bata taimakon gaggawa sannan ta kira Mum ta sanar da ita.
Awa biyu tayi a asibitin suka koma gida an samu zazzaɓin ya sauka. Bacci tayi sosai bayan sun koma dan har da maganin bacci aka bata, ta jima sosai tana bacci har dare sannan ta farka, da yake ta san ba sallah zata yi bata yi ƙoƙarin yin sallah ba tana kwance tana tuna kalaman Omar masu kama da sukar mashi a zuciyarta.
Tashi tayi ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta, wai itace take son namiji kamar Omar, ɗan daba wanda bashi da komai bai san komai ba sai riƙe wuƙa. Ita Barr Narma, manager director ta kamfanin mahaifinta, ita Narma da take juya kuɗin mahaifinta da suka haura billions wai itace take son wani da bashi da komai har yake mata wulaƙanci. Turarukan da suka kan madubin ta watsar, ta jawo madubin ya faɗi kasa ya tartwase a wajan, ta faɗa kan gado tana fashewa da kuka.
A guje Mum, Dad, Najwa da Nabil suka shigo daƙin. Dawowar Dad kenan sun rako shi sama wajan ta suka ji sautin fashe-fashe daga ɗakin. Ganin yanayin da take ciki ya saka su ƙarasowa da gudu kowa yana tambayarta abinda yake faruwa. Bata iya magana ba sai kuka da take yi a jikin mahaifinta mai tsuma zuciya. Duk sun yi shiru suna surarem kukan da take yi, sai da tayi mai yawa sannan ta tsagaita sai ajiyar zuciya da take yi.
Najwa ta kawo mata ruwa Dad ya bata tasha yana kallon ta a nutse. Sai da yaga ta nutsu sosai sannan ya ce, "Me yake damun ki Daughter? Me ya faru kika shiga wannan yanayin?."
Narma murya a shaƙe ta ce, "I'm in love Dad." Dad ya kallo Mum ya sake kallon Narma ya ce, "kina nufin ki ce duk wannan damuwar da kike ciki saboda soyayya ne? You're in love, that's why you looks like this?." Bata yi magana ba sai lumshe ido ta tayi a jikin Dad bata ce komai ba.
Dad ya yi shiru bai ce komai ba Mum ta kalle ta tace, "Narma taso mu je ki ci abinci." Bata samu damar magana ba ta miƙar da ita tsaye suka fito falo ta zaunar da ita. Tea ta zuba mata ta miƙa mata ta ce,"Oya take it." Narma a sanyaye ta ce, "I want to brush my teeth first."
"Okay, Najwa kai ta bathroom." Najwa ta riƙeta ta miƙe tsaye, Dad ya ce, "take her to my bathroom, sai an gyara ɗakin ta, ki buɗe drawer akwai sabon brush." Da to ta amsa suka wuce zuwa ɗakin Dad.
Basu jima ba suka dawo, Narma ta zauna tana shan tea É—in kaÉ—an-kaÉ—anan tana tunanin yadda suka yi da Omar. Sai da shanye tea É—in tass suna ta yi mata sannu. Sai da ta gama ta nutsu sannan Dad ya ce, "akwai abinda ki ke so?."
Ta girgiza kai alamun babu ya ce, "okay, tell me your problems. Who is the guy you are in love with?." Ta yi shiru bata amsa ba, Mum ta ce, "Narma Dr ya tabbatar mana da kina cikin damuwa shine ya haifar miki da zazzaɓi ɗazu, yanayin muka same ki a ɗaki ya tabbatar min da maganar Dr gaskiya ne. Waye wanda ki ke so haka?."
Shiru tayi bata ce komai ba, Nabil yayanta ya ce, "Narma feel free ki faɗi abinda yake ranki, kar ki damu zamu yi supporting ɗinki hudrend percent." Narma tayi ajiyar zuciya ta ce, "Dad ku taya ni da addu'a saboda kamar bazai karɓi ni ba." Mum ta ce, "what! Kina nufin daman ke kike sonsa ba shi yake sonki ba?." Narma ta ɗaga kai alamun eh. Mum cikin wani yanayi ta ce, "damn it! Ta ya hakan ya faru Narma?."
"I don't know" ta faÉ—a kamar zatayi kuka.
Dad cikin rarrashi ya ce, "ɗan waye? Ɗan sarkin Dubai ne?" Ya faɗa yana kallon ta, dan a ganinsa duk wanda Narma zata so har haka kuma bai san tana yi ba, bai ma karɓeta ba, a ganinsa sai dai ɗan sarkin Dubai. In ba haka ba to waye zata iya wannan son da ya saka mata zazzaɓim damuwa? A ganinsa ko ɗan president albarka.