Sashe 16
Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kawai sai ta fara kuka ta ce, "amma ka ce min ka daina ko? Ka san bana so. Yaushe ka fara yi min ƙarya? Ina yarda da duk abinda ka ce min saboda na san ƙarya ba ɗabi'arka ba ce, amma gashi ka fara Omar." Ya tausasa murya ya ce, "ai na faɗa miki dalilina Didi, kuma bazan sake ba faga yau nayi miki alƙawari, ki daina kuka." Ajiyar zuciya tayi ta kalle shi bata ce komai ba.
Ɗauke wacce ta faɗi ƙasa tayi ta miƙe ta ce, "Zan shiga na kwanta." Ya miƙe shima yana kallonta ya ce, "ki daina kuka to, bazan sake ba in sha Allah." Ya share mata hawayen da kansa ta kalle shi tace, "na daina Omar." Da hannu yayi mata alamun tayi murmushi sai tayi murmushin shima yayi murmushi ya fita ya barta a wajan. Ajiyar zuciya tayi ta shiga ɗaki bayan ta kashe hasken falon.
Washe gari.
Kasancewar Juma'a ce da wuri ta tashi dan tana yin abincin sadaka duk ranar, nan da nan ta haɗa shinkafa da wake da dafaffan kwai ta zuba a disposable packs kamar yadda take yi in an idar da sallah ta fita da kanta ta rabawa yara. Lokacin da ya shigo ta gama tana zubawa a packs ɗin ya kalle ta ya ƙaraso ya ce, "Didi wai ba za a samu mai taya ki aikin nan ba?" Ya faɗa yana karɓa tare cigaba da yin abinda yake yi.
"To Omar ko wacce mace tsoron shigowa gidan nan yake yi saboda kai, kai kanka in kaga baƙuwa ka dinga faɗa kenan taya zan samu mai ta ya ni aiki?."
"Gabaɗaya mutanen unguwar nan munafukai ne, musamman ma matan." Jin abinda ya ce sai tayi murmushi ta bar masa ya cigaba da abinda yake yi dan tasan bazai barta ta cigaba ba. Sai da ya gama sannan ta kalle shi ta ce, "Amma dai ba da ƙananun kaya zaka je masallaci ba?." Zai yi magana ta ce, "Don Allah ka saka manyan kaya, don Allah na don ni ba." Hannu ya wanke bai ce komai ba ya shiga ɗakinsa.
Sai gab da lokacin sallah sannan ya fito yana fitowa ta fito itama daga falo ta bishi da kallo tana murmushi. Ya yi mata kyau cikin yadi milk colour, abin ka da namiji mai kyau, duk da bai saka hula ba amma yayi kyau sosai. Murmushi tayi ta ƙaraso inda ya ke ya ce, "ƙanina mai kyau ne wallahi, Allah ya sa kayi budurwa yau." Taɓe baki yayi bai ce komai ba kuma bai yi murmushi ba.
Ta kalli gashin kansa ta ce, "ya kamata ka É—an rage gashin nan na kanka, kalli fuskar ka ma, gashin yayi yawa kamar wani buzu."
"Shi ne" Abinda ya ce kenan yana juyawa ya fita ta bishi da kallo tana murmushi.
Hijjabi ta saka ta fita bayan ta rufe ƙofar gidan ko makulli bata saka ba dan ta san babu wata halitta da zata iya shiga gidan da sunan sata. Kai tsaye gidan Hajja ta shiga a lokacin Nayla tana zaune kusa da Hajja sun saka ta a gaba ita da Salma sai wai ta basu labarin lokacin haihuwar Salma.
Sallamar Didi ya saka suka amsa Nayla ta ce, "Didi." Didi ta harare ta ta ce, "daman kin ce min baza ki sake zuwa ba gashi kin tabbatar." Nayla tayi dariya sosai, Didi ta kalli Hajja ta ce, "Hajja ki shaida mun yi faɗa da Nayla." Hajja ta ce, "ko ɗazu sai da tayi zancenki, amma wai baza ta shiga ba saboda Omar. Na ce Omar ya raba Yaya da ƙanwarta."
Didi tayi dariya suka gaisa da Hajja suma duk suka gaishe ta amsa da murmushi ta ce, "Hajja mutuminki shine yake firgitata, na faÉ—a mata kuma ta daina jin tsorosa babu abinda zai mata amma ta kasa. Kuma da zata zauna a garin nan na wani lokaci suna sabawa shikenan. Wahalar sabo ne dashi kawai." Salma ta ce, "Didi ko iya wannan idanun na sa ma ai ya isa ka ji tsoro balle ya buÉ—e baki."
Didi tayi dariya ta ce, "yanzu saboda shi sai ku daina zuwa wajan Yayarku?." Salma ta ce, "ai Didi lamarin na sa ne akwai ban tsoro." Nayla ta ce, "Ke da bai taɓa tarfa ki kamar yadda ya yi min bama kenan, ina jin in ke ya yiwa abinda ya yi min suma zaki yi." Didi ta ce, "ai na faɗa miki shi zan saka yazo ya ɗauko min ke in baki koma ba, zaki gani kuma."
Hajja ta ce, "wai! ranar sai Hauwa ta suma." Suka yi dariya gabaÉ—aya kafin Didi ta ce, "Hajja dahuwar awara zaki koya min, wacce nake kaiwa ana yi min bata yiwa Omar daÉ—i." Hajja ta ce, "shikenan kin kama Hauwa har wuya. Ja hannunta ki je ta dafa miki, ta iya dafa awara nesa ba kusa ba. Itama irin Omar É—in ce, tsabar son cin ta da take yi sai da ta iya dafawa." Didi ta kalli Nayla ta ce, "Alhamdu lillah, ki ce shiga gida ya kama ki."
Nayla ta wara ido ta ce, "ai gwara ki aiko min da kayan nayi miki a nan sai na aiko miki da ita, kuma ban iya mai yawa ba Æ´ar kaÉ—an na iya dafawa." Didi ta ce, "ai wallahi gida zamu je ki yi min nima na koya, babu wani na aiko miki dashi baki isa ba."
"Allah Didi tsoronsa nake ji, in na ganshi hantar cikina kaÉ—awa take yi." Suka yi dariya gabaÉ—aya Didi ta ce, "Tsoron nake so na cire miki, ki saba dashi shima yayanki ne kamar yadda nake yayar ki."
Hajja ta ce, "ai na faɗa mata in da amana ai ruwa bazai dafa kifi ba, Ita da ya saɓo ta a kafaɗa ko riga babu itace mai faɗar haka a kansa." Nayla ta dafe kai cikin takaicin kalaman Hajja ta ce, "Wai Hajja don Allah meye haka?." Didi ta yi dariya ta ce, "Hajja kina bata kunya."
"Kunyar ƙarya ce, ai ba ƙarya nayi ba a kafaɗar ya ɗauko ta ko? Kuma ai gaskiya ne rigarsa ya saka mata."
Didi ta ce, "Gaskiya Hajja ki daina tuna mana maganar nan kunya mu ke ji." Hajja tayi dariya ganin Nayla sai ɓata rai take yi, ita kuma tana sane take faɗa saboda ta tunzura Nayla ɗin. Didi ta miƙe tana dariya ta ce, "Nayla ina jiranki." Nayla ta ɗaga kai dan babu yadda zata yi ne amma bata son haɗuwa da Omar.
Bayan Didi ta fita Nayla ta kalli Hajja ta ce, "Haba Hajja! Meyasa zaki ce mata na iya don Allah? Kin san tsoronsa nake ji." Hajja ta ce, "ke ni fa saboda kyautatawarsa akan ki ne ce ki je, sannan Didi jikata ce kamar ki, tana sona tana son ku gabaÉ—aya." Nayla ta kalli Salma ta ce, "Salma zamu je?." Salma ta wara ido ta ce, "ai na rantse da Allah baza ni ba, Ke dai ki je." Nayla ta zauna kamar zata yi kuka zuciyarta cike da fargaba.
Didi na rabon abinci a ƙofar gida ta hango Nayla tana tahowa a nutse sai tayi murmushi tana kallonta, ita dai Nayla na matuƙar burge ta sosai, bata sani ba ko dan tana kyau ne ya saka haka oho. Babban abinda yake burge ta game da Nayla shine shigarta, bata taɓa yin shigar banza. Kayanta ta basa wuce doguwar riga, riga doguwa har guiwa da siket, butterfly da sauran kayan mutunci na zamani. Wannan dalili ya saka take sonta sosai, gata kirki.
Tare suka ƙarasa rabon abincin da Nayla suka shiga cikin gidan Nayla sai ɗari-ɗari take yi. Didi ta kalle ta tace, "kwantar da hankalinki baya nan, ya kai yamma bai dawo ba."
Ajiyar zuciya tayi Didi tayi dariya suka fara haɗa awara kamar yadda ta ce. Didi tana gefe tana kallon ta har suka markaɗa a blender aka tace aka fara dafawa. Didi ta ce, "bara na gyara kayan miyar nan mai sauce nake so nayi." Nayla ta ce, "ashe kina son awara, nifa saboda son da nake mata ne ya da na iya dafawa, dan tunda na taɓa ganin gashin kai a cikin wacce ake yi min a gida na daina bari masu aiki su yi min." Didi ta ce, "ni bata dame ni sosai ba, mutuminki ne masoyin awara, bai damu da nama ba kamar yadda ya damu da awara. Zai iya ci miki awara da safe da rana da daddare, Sam shi nama bai dame shi ba, da rayuwar nama da babu duk ɗaya, har gwara kifi ma."
_Shiyasa yake gabjeje mana ashe soya beans yake afakawa cikinsa_ Nayla ta faɗa a zuciyarta. Didi ta ce, "kuma kar ki ɗauka da yawa yake ci, kin san ɗan iyayi ne, ƴar kaɗan in ya ci zata ishe shi kawai sonta yake yi. Da ita da jollof rice mai kifi, da noodles, da pasta and stew. Inda safe ne kuma doya da ƙwai in ta huce ya ci ta da ketcup ko yaji, har mamakin inda ya iya cin ketcup yake yi. Noodles ma sai ya ci ta tun safe har dare kamar yaro. Wani lokacin kuma baya cin ahinci sai dai ya shafa coffee ko ya yini yana cin apple da kankana." Nayla ta yi murmushi kawai tana mamakin ko ita ina ruwanta da abinda yake so.
Didi ta ce, "yau so nake yaci har ya barta, bara na haÉ—a sauce É—in." Nayla ta ce, "bar shi nayi miki kafin awarar tayi, tunda kin gyara kayan miyar bara ayi blending, ni gyara su ne bana so." Didi ta ce, "yau Omar zai ci abincin ki kenan." Tayi dariya kawai ta fara haÉ—a sauce É—in tana yi suna hira.
Nan da nan suka gama Nayla ta tace awarar ta kalli Didi ta ce, "Zamu bar ta haÉ—a jikinta sai mu soya. Ita kuma sauce É—in in kina da mayonnaise ki zuba mata, ko in kin zo serving ki zuba ni dai tana min daÉ—i." Didi ta ce, "ai kam na gode sosai Nayla, Kin ga nima na koya saboda gaba, ashe ma babu wahala." Tayi murmushi ta ce, "bara naje gidan Hajja."
"To ki dawo mu ƙarasa don Allah."
"Zan dawo yanzu Didi" ta faÉ—a tana fita da sauri.