← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 54

Sashe 24

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da tayi sallar i'sha sannan ta fara shiri, sun yi da ƙawayenta zasu ne yawo hakan ya saka ta shirya cikin doguwar riga wacce jikinta take kamar roba mai tsaga a baya, daga hips ɗin akwai wani maɗauri kamar mayafi daka ɗaure shi aka ɗaura a tsakiyar rigar. Rigar baƙa ce hakan ya saka ta haska jikinta sosai, ta ɗauki hula ta saka sannan ta ɗauko ƙaramin mayafi ta ɗora akan hular. Kallon kanta take yi, dan ta kanta san tayi kyau itama sosai, ta fesa turare masu daɗin gaske sannan ta sauka falon ƙasa a lokacin takwas daidai.

A daidai wannan lokacin Omar ya shigo cikin gidan ya kalli Yahya suka gaisa yana cewa, "yanzu Hajiya yake tambayarka." Omar ya ce, "gani ai, tana ina?."
"Tana ciki bata fito ba." Omar ya kalli agogon wayar sa ya ce, "ƙarfe takwas aka ce min, yanzu kuma takwas da mintina biyu, In takwas da sha biyar tayi wallahi babu inda zan je."

Shi dai Yahya kallon sa yake yi da mamaki, ganin sun haɗa ido sai Yahya ya ce, "ban san ko sunanka ba amma ƙarfin halin ka yana bani mamaki." Omar ya kalle shi ya ce, "Omar sunana."

"Koda na ji, yanayinka da maganarka da ta masu suna Omar ka yi kama, Daman da wahala ka ga masu suna Omar ba irinka ba, ko kaÉ—an ba sa lamuntar raini." ÆŠan murmushi Omar ya yi kawai amma bai ce komai ba.

Narma ce ta fito tana duba waya tana cewa, "wai ina driver nan yake ne? Bana son wulaƙanci da iskanci fa, dan ya raina ni ni ce zan zauna ina jiran sa?."

Inda yake ta kalla ta ga ya kalle ta ya ɗauke kai kafin ya ƙarasa wajan motar ya buɗe mazaunin driver ya shiga ya zauna ita kuma ta ja ta tsaya. Ƙwanƙwasa glass ɗin gaban motar tayi ya sauke glass ɗin ƙasa. Wani irin kallo take masa na raini da ƙasƙanci ta ce, "Malam ka sakko ka buɗe min, ko kana so kace ni zan buɗe?."

"Baki da hannu?" Ya faÉ—a ba tare da ya sake kallon ta ba.
"Ina dashi, kai nake so ka buÉ—e min."
"Ashe baza ki je" ya sake kallon agogo ya ce, "kina da mintina bakwai in lokaci ya cika babu inda zan je."

Kallon sa take yi shi kuma ya kalli glass ɗin gaban motar kamar motar sa, fuskarsa ɗaure matuƙa ga wani kwarjini da fuskar take fitarwa. Duk da tana jin tsoronsa musamman yadda ya ɗaure fuska amma hakan ya saka ta kuma cewa, "ni kuma indai baka buɗe min ba bazan je" ta faɗa tana komawa gefe ta ja ta tsaya tana so ta ƙure shi iskancinsa.

Shi kuwa kallon ta yayi zuciyarsa a sama matuƙa, abu ɗaya kawai ya sani ko zata mutu ta dawo wallahi bazai buɗe mata mota ba sai dai kar ta je. Zama ya cigaba da yi a cikin motar sai kace motar ta Didi ce. Agogo yake kallo yana jira lokacin da ya bata ya cika ya fita ya bar gidan. Su dai ma'aikatan gidan kallon ikon Allah suke yi, mamakin Omar su ke yi ɓangare ɗaya suna jin daɗi an samu daidai da Narma, suna tsaye suna so su ga waye zai ci wasan.

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 11.*

Kowa a wajan kallon ta yake yi ana kuma jira a ga Omar zai fito ya buɗe mata motar ko bazai fito ba. Ga mamakin su Omar bai fito ba yana zaune a cikin motar kamar motarsa, ita kuma tana tsaye har lokacin tana jira ya fito ya buɗe mata. Mamakin sa take yi ganin bai sauko ya buɗe mata ba kenan bazai yi ba? In haka ya faru wacce irin kunya zata ji a gaban ma'aikatan gidan?. Wayarta ce tayi ƙara ta ga ƙawayenta da suke jiran ta zasu fita ne, ta buga uban tsaki ta kashe wayar tana sake kallon sa babu alamun ma zai fito dan ko kallon inda take ma baya yi.

Shi kuwa Omar ƙoƙarin daidaita ɓacin ransa yake yi dan in ya fita a yadda yake jin zuciyarsa tsaf zai sharara mata maruka masu zafi, shi kuma ba haka yake so ba, yana so su rabu lafiya ko dan alƙawarin da ya yiwa Didi, sannan yana so su rabu lafiya ko dan kuɗin mahaifinta da ya karɓa. Shiru na kusan mintina biyar hakan ya yi daidai da saursa minti biyu ya kama gaban sa.

Yahya ne ya ƙaraso wajan motar  a sanyaye ya ƙwanƙwasawa glass ɗin gefen Omar, Omar glass ya sauke yana kallon sa ya ce, "Omar don Allah kazo ka buɗe mata ka huta." Omar ya kalle shi ya ɗauke kai dan babu amfanin ma yi masa magana.

Yahya ya juya ga Narma ya ce, "Hajiya bismillah" ya faɗa yana buɗe mata amma sai ta bishi da banzan kallo na wulaƙanci ta ce, "Wallahi shi zai buɗe min, in kuma bai buɗe min ba daga yau ya bar aiki a gidan nan, sai naga waye ubansa a Kano da yake min wannan wulaƙanci. Shashasha dashi ƙazami."

BuÉ—e kofar taga an yi sai tayi murmushi ta É—auka zai buÉ—e mata ne, ga mamakin ta kai tsaye inda take ya nufa fuskarsa a É—aure, yana zuwa ya kalle ta ya ce, "in kika sake furta abinda kika furta É—azu sai kin yi dana sanin haÉ—a ido dani a rayuwarki, in kuma kina ganin wasa nake yi ki maimaita abinda ki ka ce yanzu" ya faÉ—a ciki tsawa yana tsare ta da idanunsa masu ban tsoro da kwarjini.

ÆŠiff Narma tayi tana kallon idanun sakamar yadda ita yake kallo, da sauri ta É—auke kai daga kansa, ganin ta yi shiru ya cize baki yana karkatar da baki irin yadda Æ´an daba suke yi ya nuna ta da taysa ya ce, "ki san irin maganar da zaki dinga faÉ—a min in kina so kan ki da zaman lafiya, In kuma kina so na huda cikin ki sai ki cigaba."

Yahya ya kalla ya cilla masa key É—in motar shi kuma ya chafe, Omar bai ce komai ba ya juya ya fita daga gidan.

Wata uwar ƙara Narma tayi ta shiga cikin gidan a guje ta faɗa kan kujera ta fashe da kuka mai ƙunar rai. Wai ita Narma wani banzan ɗan daba, ɗan shaye-shaye ya yiwa wannan wulaƙacin a gaban ma'aikata, kawai saboda Dad ya bashi damar haɗa ido da ita shine yake zaƙewa. Ita Narma mai capacity wani ɗan tasha ya wulaƙanta a gaban masu aiki a ƙarƙashin ta.

Hannu na rawa take kiran Dad, yana ɗauka kawai ta fashe masa da kuka. Dad ya ruɗe sosai ya ce, "Oh Narma, what wrong? Why are you crying like this?." Kuka take yi sosai cikin baƙin cikin da take ji a zuciyarta. Sai da tayi kukan ta gaji murya na rawa ta ce, "Dad i was really disrespected by that guy in front of the maids, Dad ƙawayena suna can suna jira na amma yayi tafiyarsa. Dad gaskiya ni bana son aiki dashi, ka barni da wanda muke tare dasu a nan."

Dad ya ce, "stop crying and talk to me, what happened?." Narma ta bashi labarin abinda ya yi mata sannan ta ce, "Dad wai waye shi da yake min haka ne?."

Dad ya ce, "ba kowa bane fa ce ɗan daba kuma ɗan tasha, ba kowa bane fa ce ƴan bangar siyasa wanda mu ke amfani dasu wajan cikar burin mu. Bana son yin wasa da Tiger shiyasa kika ga ina biye masa duk abinda ya ce, zaɓen gaba nake ji ke kin san kujerar da nake nema, irin su Tiger makami ne sosai a tafiyar mu shiyasa ki ka ina biye masa. In ba dan haka ba shi waye? Ko inda motarki take bai isa yazo ba, lafiyarsa nake so ya bani wajan kare ta ki shiyasa nake jure duk abinda yake miki. Sorry my daughter kar ki damu da wannan, abu ne ƙarami da mun ci zaɓe shikenan bazai sake ganin koda fuskarki ba. So wipe your tears my dear, i know what i'm going to do."

Narma ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "But Dad if he doesn't stop bothring me and upset me, i will have him arrested wallahi." Dad ya ce, "kar ki damu, ni zan san abinda zan yi. Yanzu kin zuwa dinner É—in?."
"Na fasa."
"Gobe ƙarfe nawa zaki je arewa 24 ɗin?."
"Zuwa 11am."
"Okay ki kwantar da hankalinki ki huta kin ji? Babu abinda zai sake faruwa." Amsa tayi kawai ta kashe wayar zuciyarta na aiyana mata irin abubuwan da ya kamata ta yi masa wanda zata huce.

       Shi kuwa Omar yana fita ya tarar da Bash a machine ya ɗauke shi suka bar wajan zuciyarsa na faɗa masa gwara ya bi shawarar Didi ya ajjiye aikin nan in ba haka ba wallahi zai yiwa ƴar mutane illa. A haka suka je unguwar yana sauka akan machine wayarsa tana yin ƙara, ko bai duba ba ya san Senator ne hakan ya saka kawai ya danna ya kara a kunne.

Kafin Sen ya yi magana ya ce, "batun aikin nan na ajjiye shi bazan yi ba, matuƙar zata dinga ɗaga min murya tana faɗa min magana mara daɗi bazan jure ba, gwara na ajjiye shi a huta kawai. In ban ajjiye ba zaka tarar da abinda bazai maka daɗi ba, ba a ɗaga min murya na ƙyale, ba a yi min ihu a kai, ba a yi min maganar banza. Dan tana ƴarka baza ta yi min abinda bana so na ƙyale ba."
Chapter 24 · 0% Book details