← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 54

Sashe 31

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Narma ta kalle su ta ce, "shine Tiger fa, na san kin san sunan na sa ko?."
"Ni kuwa na san sunan, ban dai san fuskarsa ba amma na san sunansa ko É—azu media akan maganarsa ta yamutse."
"Yes shine. Ai na baku labarin abinda ya faru jiya, shiyasa Dad yake so ya dinga kai ni duk inda nake so."

Safna ta kalle shi ta ce, "amma kin cuce shi, a ina ya yi kama da bouncers don Allah? Ki ga mutum É—an daidai dashi ki haÉ—a shi da waÉ—anan jibga-jibgan halittar?." Suka yi dariya gabaÉ—aya Nasreen ta ce, "Gaskiya dai ta cuce shi, wannan ai ko rabin bouncers bai kai ba, yanayin jikinsa ma sha Allah."

Safna ta ce, "kuma gashi bai yi kama da yadda ake faÉ—arsa ba. Kalle shi fa fari kyakykawa mai zubin buzaye." Nass ta ce, "ni kaina mamaki nake yi anya kuwa É—an daba ne kamar yadda ake faÉ—a?. Amma jiya na gani da idona." Narma ta sake cewa, "mu je mu tafi, É—an rainin hankali ne yanzu sai na neme shi na rasa." ÆŠaya daga cikin su tace, "Dan ya raina miki hankali?." Nasreen ta ce, "baki yi maganinsa bane." A haka suka fito harabar gidan ko wacce ta sha makeup kuma duk sun yi kyau.

Dukkan su da mota suka zo, ko wacce ta shiga motarta suka fita ita kuma ta shiga bayan motar. Bai ce komai ba ya buɗe mazaunin gaba ya shiga ƙhamshin turarenta ya sake kai amsa ziyara a hancinsa. Kamar zatayi masa magana sai ta kasa shi kuma yana so yaji inda zasu je.

Narma da ta fahimta sai ta faÉ—i sunan event center É—in da location É—in, bai ce mata komai ba ya kunna motar suka fita. Kallon gefen fuskarsa ta samu kanta da yi yana kallon gabansa hankali kwance fuskar sa babu fara'a ko kaÉ—an.
"Na gode" taji bakinta ya furta ba tare data sani ba. Kamar bai ji ta ba haka ya yi, ya cigaba da tafiya har suka zo inda ta ce kafin a buÉ—a masa gate ya shiga ta fito daga motar.

Har zata wuce taji ya ce, "zaki gama yaushe?." Kallonsa tayi suka haɗa ido ta ga fuskarsa babu alamun wasa ta ce, "nan da two hours." Bai sake cewa komai ba ta tsaya tana kallonsa ganin hakan sai ya kalle ta sai ta wuce shi ta shiga ciki. Samun kansa ya yi da kallon ta tana tafiya, ya yi saurin janye idanunsa jin baƙon yanayi ya na kawo masa ziyara.

Bai zauna a wajan ba fita ya yi ya koma gida a yadda ya lissafa ƙarfe goma kenan zasu gama. Ƙarfe goma da wani abun kuwa ya dawo ya samu ƴan mata suna ta fitowa ƴaƴan manya kai da ka ga yaran ka san yaran masu kuɗi ne manya ba ƙananu ba. Hango ta ya yi tana tahowa tana dariya gefen ta Ashraf ne shima dariyar yake yi.

Dauke kai ya yi ya kawar da fuska daga kallon ta ya lumshe ido, ido ya sake buɗewa a lokacin ta zo wajan, kallon motar tayi ta gane ta sai ta ce,  "Ka je kawai zamu tafi da Beb." Kallon baki da hankali Omar ya yi mata ya kalli Ashraf da shima shi yake kallo yana mamakin daman wannan ne tiger ɗin.

Narma ta sake cewa, "ka je kawai." Wani irin kallo yake mata alamun bazai ma yi magana ba ganin hakan Ashraf ya ce, "kai ba Drivern ta bane? To ta ce kaje zan kaita ka tafi mana." Kallon Ashraf ya yi bai ce komai ba dan bashi da lokacin sa. Narma ta ce, "ƙyale shi Beb, mu je ka kai ni na gaji....." bata ƙarasa ba maganar ta maƙale jin ya ce, "Ko ki zo ki shiga ko na ɗauko ki."

Mamaki suka juya suma kallon sa ganin kamar ba shi ya yi maganar ba, ya ɗago ido yana kallonta ta ƙasan ido ya ce, "bana son ɓata lokaci, ki zo ki shiga ina da abinda zan yi. Ni ba ɗan aikin ki bane da zaki ajjiye ni ina yi miki magana kina yin banza ba!." Yadda ya yi maganar a kausashe ya saka Narma ta ɗan ji tsoro amma ganin Ashraf na wajan sai ta danne ta ce, "ba fa zan shiga ba, a motar mijin da zan aura zan tafi."

Ashraf ya ce, "malam ka tafi daman ai aikin ka kenan ko? To Narma tace bata so ba sai ka ƙyale ta ba?." Kallon Narma ya yi yana cize baki ya sake kallon Ashraf ya ce, "in na sake magana ka saka min baki sai kayi dana sani. Wallahi sai na saka ka haɗɗiye haƙorinka."
"Me zaka yi?." Omar bai bashi amsa ba dan yadda yake jin zuciyarsa zai iya karya shi wallahi.

Fitowa ya yi daga motar ya matso kusa dasu ya ce, "ka sake yin maganar zaka ga abinda zan yi. Ke kuma kafin na irga uku ki shiga mota in ba haka ba wallahi sai na mare ki!" ya faÉ—a yana nuna ta da yatsa idanunsa a waje. Tsoro ya bayyana a tare da ita bata san ta buÉ—e motar ta shiga ba ya bar Ashraf a wajan ya shiga motar suka fita.

"Wai kai meye haka ne? Ina ruwanka da ni, bani nace ka bari ya kai ni ba?. Biyan ka ake yi, ina da ikon da zan ce bana son abu kuma dole ka yi min. Haba duk kabi takura min, ni wallahi na gaji." Tsayawa ya yi ya jiyo yana kallon ta kafin ya duƙa ƙasa ya ɗauko wata wuƙa mai madaidaicin girma, ya buɗe motar ya fito ya buɗe bayan motar inda take ya saka mata wuƙar a wuya kamar yadda ya yiwa Nayla ya ce, "in kika sake yi min magana wallahi sai na yi miki illa. Ni zaki dinga yiwa ihu? Sa'an ki ne ni?."

Ɗiff Narma tayi tana tuna yankan jiya ma taji azaba balle ya yanke ta a wuya. Kallon idonsa take yi yana kallon nata ya sake cewa, "in kika sake magana wallahi da ƙafa zaki koma, In na yi rantsuwa bana karyawa, ki kiyaye ni duk lokacin da na ce wallahi!."

Shiru tayi bata ce komai ba yaja tsaki ya ce, "stupid girl" ya faɗa yana barin wajan ya sake komawa motar ya ja motar suka tafi. Har suka je gıda Narma bata ce komai ba a tsorace take dashi ko motsin kirki ta kasa, ya buɗe motar ya fita ya barta a cikin motar bai sake kallon inda take ba ya fita daga gidan.

Narma haka ta koma gidan jikinta duk a sanyaye a daren ta kira Dad ta faɗa masa abinda ya yiwa Ashraf sannan ta kwanta amma zuciyarta cike yake da tunaninsa, wai wanne irin ƙarfin guiwa yake da ita haka?. Da wannan tunanin bacci ya ɗauke ta.

Shi kuwa Omar yana komawa text ya rubutawa Sen dan wallahi ya cigaba da zama inda Narma take bai dan adadin abinda zai aikata mata ba, gwara kawai su nemi wani shi kam ya gaji.

Sen yana ganin text ɗin sa ya kira shi ya faɗa maaa abinda ya faru shi kuma ya nuna jin daɗin sa akan hakan, dama amfanin kula da ita ɗin kenan, kuma shi Omar bai san Ashraf ba dole a samu damuwa in ya gansu tare. Daga nan suka yi sallama ya kashe wayar ya kwanta yana tunani, fuskar Narman yake gani a idonsa ya ja tsaki mai tsaho ya kulle ido da ƙarfin gaske.

Kwana biyu bai je ba saboda Sen ya ce ya bari Ashraf É—in ya dinga kai ta dan haka kwana biyu babu inda yake sai dai ya fita ya dawo kawai. Ita kuwa Narma biki suke sha Ashraf yana kai ta duk inda take so amma ta kasa daina tunanin Omar ko kaÉ—am, da ta rufe ido shi take gani musamman lokacin da yake kallon idanunta.

Ranar asabar Ashraf ya koma Omar bai sani ba yana zaune a ɗaki ya ga baƙuwar number tana kiran sa, ɗauka ya yi ya saka a kunne bai yi magana ba Narma ta ce, "Hello Tiger, Narma ce." Jin hakan sai ya gane ta ya ce, "ina ji."
"Ashraf baya anjima zan je biki."
"Okay" ya furta mata kafin ta sake magana ya yanke wayar.

Saurin katse da wayar ya yi jin zuciyarsa na wani irin harbawa lokacin da Narma ta fara yi masa magana, magana take cikin yanga da iyayi hakan ya saka yaji wani iri har bai san ya yi hanzarin kashewa ba. Shin wai me yake Shirin faruwa dashi ne?. Meyasa ya kasa daina tunanin ta? Meyasa yake jin wani iri da ta kira shi yanzu? Lallai dole ya san dalilin hakan kafin abun ya yi nisa.

Ɓangaren Narma murmushi ta samu kanta da yi bayan ya kashe wayar a bayyane ta ce, "muryarsa mai daɗi, zan so naga yana murmushi." Sai kuma tayi tsaki ta ce, "Ko Ina ruwana ma oho, da ya yi murmushi da kar ya yi shi ya sani. Ni so nake na manta dashi amma na kasa, ko meyasa na kasa mantawa dashi oho min" ta faɗa a bayyane tana tashi ta shiga ɗaki har lokacin muryarsa take ji a kunnen ta.

Tofa, Omar da Narma, ga kuma Nayla a gefe.

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

https://www.tiktok.com/@nanahaleemawriter?_t=ZS-8zaZqblsrGp&_r=1

*Book 1*
*P 15.*       

Nayla kuwa yanayin da take ji akan Omar ya fara damunta domin ko yaushe a cikin tunaninsa take, ko yaushe a cikin ganin murmushinsa take da zarar ta kulle. Ga faɗuwar gaba da take addaba mata, ko ya taji an kira wani mai irin sunansa sai ƙirjinta ya buga. Ɗakyar ta jure kwanaki uku bata ganshi ba, a safiyar ranar bayan tayi wanka ta shirya cikin riga da siket, rigar har guiwa ta saka mayafi ƙarami a kanta ta fito falon.
Chapter 31 · 0% Book details