Sashe 37
Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bai sake magana ba ya cigaba da tafiya har suka zo inda take nufi. Shiga suka yi ya ajjiue motar yana jira ta fita. Kallon sa yake ji tana ji a jikinsa shiyasa yaƙi kallonta, bai san meyasa ta canja haka ba. Narma ta ce, “mu je tare.†Kai ya girgiza bai kalle ta ba ta ce, “Don Allah.†Kallon ta yayi ya rasa meyasa ta canja gabaɗaya, ya rasa meyasa take masa irin wannan abubuwan kamar wacce take tare da wani mijinta.
“Bazan je ba†ya faɗa kai tsaye. Narma taji babu daɗi a zuciyarta, ta buɗe ta fita ya bita da kallo dan iya tafiyarta ma abar ɗaukar hankali ce.
Ba jimawa sai gata da wani waiter a bayan ta da ledoji, ta shiga motar sannan ta karÉ“a ta kalle shi ta ce, “mu je.†Fita suka yi ta sake kallon shi ta ce, “Zaka kai ni zoo park? Amma mu shiga tare kaji!†Yadda tayi maganar kaÉ—an ya rage bai saki motar ba, amma kasancewar sa akwai dakiya da basarwa bai nuna ba ya ce, “ni bazan shiga ba.â€
“Don Allah Omar!.†Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba ya ɗauki hanyar Zoo park.
Ba ya cewa komai yana ji tana kallonsa ya rasa meyasa take son kallon sa haka kawai. Narma kuwa tunani take yi, ko shima yana jin irin abinda yake ji akan sa oho. A haka suka Æ™araso bakin zoo park, ta kalle shi ta ce, “mu je don Allah.†Yana kallon gabansa ba tare da ya kalle ta ba ya ce, “babu inda zan je.â€
“Don Allah†ta faɗa tana kallonsa.
“Bazan je ba!.â€
“Ba don ni ba, don Allah, don Annabi.†Numfashi ya sauke ya kalle ta, baya son magiya ko kaɗan, magiya tana daga cikin abinda Didi take masa ta cuce shi ya yi abinda ba ya so. Ba tare da ya kalle ta ba ya buɗe motar ya fito ta biyo bayan sa tana murmushi.
Shi ya biya kuɗin ticket suka shiga ciki. Tafiya suke yi tana gaba yana baya, sam yaƙi yarda su jera su tafi tare, da tazo kusa dashi zai ɗan tsaya har sai ta wuce sannan zai biyo ta. A haka ta suke ta tafiya, suna zuwa waje-waje baya cewa komai dan shi kam ya gaji. Mamaki yake yi ma da ya amince ya biyo ta, mamakin kansa yake yi kamar ba shi ba wani abun yana niyar canja shi. Da aka zo wajan tiger sai Narma ta yi murmushi ta kalle shi sai ta ga ba wajan ma yake kallo ba.
Ta yi murmushi ta ce, “Tiger i like your acting†daga haka tayi gaba. Bai yi tunanin me ta ce ya wuce shima.
Waya ya tsaya yana amsawa hakan ya saka ta tsaya tana kallon sa cikin annushuwa mai yawa, ko tare da Ashraf take bata jin wannan abinda take ji a kansa, shiyasa ta kasa fassara shi har yanzu. Basu jima ba suka fita suka mota tare da ɗaukar hanya. Har lokacin bai ce mata komai ba itace dai take kallon sa kamar ta cinye shi. Lokacin sallah ne yayi hakan ya saka yake gudu har suka ƙarasa gidan ya tsayar motar.
“Na gode.†Kai ya É—aga kawai bai ce komai ba. Ta yi gyaran murya ta ce, “Gobe zan koma Abuja.†Kallon ta ya yi ta É—aga masa kai ta ce, “Daddy ya ce na koma ni kuma ban gaji da Kano ba.†Maimakon ya amsa mata abinda ta ce sai ya ce, “Allah ya kaimu.â€
“Amin ya rabbi. Ƙarfe sha biyu jirgina zai tashi, zaka zo ka kaini airport?.†Yadda take maganar a shaÆ™e ya saka shi ya kalle ta, sai ta marairaice ta ce, “please!.â€
“Allah ya kaimu†ya sake faÉ—a a taÆ™aice. Ta amsa da amin ta ajjiye masa abinda ta siyo ta ce, “ga naka nan, in baka so ka kaiwa Sister. Sai gobe†ta faÉ—a tana buÉ—e motar ta fita. Kafin ta shiga gidan ya fito ya ce, “Makullin.â€
Tsayawa tayi tare da dawowa, ta karɓi key ɗin tana kallon sa bata ce komai ba ta wuce ciki zuciyar tahar zillo take yi daga ƙirjin ta saboda bugawar da take yi. Bai bar gidan ba sai da yayi sallar la’asar sannan ya fita daga gidan ya nufi gidan Didi.
Narma tana kallon sa har ya fita ta jingina da bango idanunta a lumshe ta ce, “Wayyo Allah, ne nake ji haka akan wannan mutumin? Meyesa bana so ya yi nisa dani? Meyasa nake so naji yayi magana? Ina haushinsa da nake ji a baya ya tafi?.†Babu mai bata amsa ta buɗe idanunta a bayyane ta ce, “me hakan yake nufi?.†Gate ɗin gidan take kallo kamar shi take kalla kafin ta ja baya ta ta koma ciki.
Omar da ya koma ya bawa Didi kayan gabaɗaya, Didi ta karɓa tana godiya dan shi kam ta san ba ci zai yi ba. Didi tana ta yabon Narma shi dai bai ce komai ba ya yi shiru yana kallon wani waje daban yana mamakin yanayin da yake ji a kanta da abubuwan da take yi masa ita kanta Narma. Bai bari tunanin ya yi tasiri a kansa ba ya tashi ya fita daga gidan domin samu ya manta da maganar.
Washe gari.
_Tiger don’t forget my flight is at 12pm._ abinda ya gani kenan a wayar É—sa, ya sake maimaitawa karantawa ya fahimci abinda take nufi. Sake karantawa ya yi a karo na uku sai ya ja tsaki ya cillar da waya ya ce, “iyayi, baza a yi magana da hausa ba sai da turanci, sai ka ce an faÉ—a mata na iya oho.â€
Wanka ya yi ya saka manyan kaya daman ya sanar da Didi zai mayar da ita bai shiga wajan ta ba kai tsaye ya tafi. Ta sama ta hango zuwan sa ta ƙare masa kallo tun kafin ya shigo tana murmushi. A haka ta sakko ta same shi, ta ƙarasa tana sallama da masu aikin a yatsine kamar bata so. Mai gadi ya saka mata jakar ta booth ta shiga motar. Kamar jira yake yi ya shiga shima suka tafi.
Bai ce mata komai ba daman ta san bazai ce ba ita kuma hakan da yake yi ba ƙaramin burge ta yake yi ba. Murmushi tayi bai kalle ta ba abinda yake gabansa kawai yake yi.
Wayarta ce tayi ƙara ta duba taga sunan Dad ta ɗauka ta saka a kunne kafin ya ji ta ce, “Yes Dad, gani nan zuwa.†Shiru yaji ta sake yi kafin ya ce, “shine.†Daga nan bai sake ji ta ce komai ba ta yanke wayar. Shigar su Airpot ba jimawa ya ƙarasa ɓangaren domestic kamar yadda suka ɗauko ta a wancan lokacin.
Tsayar da motar ya yi ta zuba masa ido tana kallo. Kamar bai san kallonsa take yi ba ya share yana kallon glass É—in gaban motar. Ganin kallon ya yi yawa ya juyo fuska a É—aure ya ce, “Kina bina bashi ne? Kin ishe ni da kallo.â€
Murmushi ta yi bata ce komai ba kuma bata daina kallo sa ba. Ƙaramin tsaki ya yi jin hakan sai ta ce, “Faruq!.†Wani irin bugawa zuciyarsa tayi ya kalle ta da manyan idanunsa da suke da haske a wannan lokacin. Itace mutum na farko da ta taɓa kiransa da wannan suna, kowa ya san Faruk sunan sa ne amma babu wanda ya ke faɗa masa sai dai Omar ko sunayen da aka san shi da shi.
Ganin yana kallon ta sai ta ce, “Zan tafi, amma na kasa gane yanayina haka kawai bana so na tafi.†Bai amsa mata ba ta sake cewa, “Amma zan dawo, naji daÉ—in kwanakin da nayi a Kano tare da kai. Da farko nayi maka wata fahimta daban please ka yafe ni, abinda nayi maka ya wuce.â€
Shi wallahi mamaki take bashi yana tunanin anya ba Æ™waya ta fara sha ba, to in ba aikin Æ™waya ba ina ita ina bashi haÆ™uri? Laifin me tayi masa da take bashi haÆ™uri? A matsayin sa nawa da zata bashi haÆ™uri?. Daga yin kwana takwas tare dashi har tayi masa laifin da zata bashi haÆ™uri?. Katse shirun ta yi ta ce, “Faruk say something..â€
Kallon ta ya yi ya ce, “zaki rasa jirgi.†Ta kalli agogo ta ga saura mintina ashirin jirgi ya tashi ta kalle shi ta ce, “in na rasa zan iya neman wani.†Ganin bazai magana ba sai ta buÉ—e motar ta fito, ga mamakinsa da kanta ta É—auko jakarta a bayan mota ta riÆ™e handbag É—inta ta dawo kusa dashi ta ce, “thank you for being always by my side, thank you for your helpful.â€
Ya fahimci abinda take nufi rass, ya gane abinda ta ce kawai shi sam baya so ayi masa turanci ne. Inda ace zasu cigaba da zama a Kano tare sai ya karta mata warning akan yi masa turanci, baya ra’ayi ya fi son ayi magana da yaren da ya iya.
Kallon ta ya yi ya ga abaya ta saka, a karo na farko da ya ganta da abaya amma duk da haka an yi shaping abayar ta zauna daidai da jikinta ko wanne lungu na jikin ta ya shiga cikin abayar ya zauna dasss kamar a jikinta aka É—inka.
“Allah ya kiyaye hanya.†Narma ta ce, “Amin. Can you do me a favor please?.†Kallon ta ya yi da mamaki da kuma takaici, shi ba ya son turanci amma ita ya ga alama in bata yi ba bata jin daɗi gabaɗaya. Narma ta ce, “Smile please.†Ko kallon ta ma bai yi ba balle ya yi murmushi, sai ma sake haɗe gira da ya yi ya ɗauke kai.
Murmushin ita take yi dan iya wannan ɗauke kan ya biya ta ta ce, “I like your acting Faruk. Anyway, na tafi ka bawa Yahya key ɗin motar sai na sake dawowa a karo na biyu.†Kai ya ɗaga mata ta fara tura jakarta gaba tana tafiya ya samu kansa da binta da kallo.