← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 54

Sashe 47

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau ta kama ranar juma'a kamar ko wanne sati Didi ta kammala abincin sadaka ta rabawa yara ta koma tana hutawa ya shigo bayan an sakko daga masallaci. Da kallo take binsa ya zauna ta ce, "har an sakko?." Gira kawai ya ɗaga alamun eh kafin ya kalle ta sosai ya ce, "Didi." Ta kalle shi  ba tare da ta amsa ba, ya ce, "ta ya zan iya gane Ina son wata?."

Da kallon rashin fahimta ta bi shi ta ce, "ban gane ba, me ka ke nufi?."
"Ina nufin in na fara son wata ta ya zan fahimci hakan?. A taƙaice ya ake gane soyayya?."

Didi da kallo take bin sa cikin faÉ—uwar gaba, babban tashin hankalin ta bai wuce kar ya ce yana son Narma ba, amma tunda ya tambaya zata faÉ—a masa dan tafi kowa sanin bai san soyayya ba. Didi ta ce, "To nima Omar ba wani sani nayi ba ai."

"Amma baza ki kasa yi min bayani yadda zan gane ba ai ko?" Ya faɗa yana tsare ta da ido. Didi ta ce, "Zuciyarka zata dinga bugawa a yayin da ka ganta, zaka dinga ɓata lokacin ka wajan saurarenta, zaka dinga jin shauƙi sosai koda sautin muryarta ka ji, zaka dinga jin zaka iya yin komai dan ka mallaketa. Sannan....." dakatar da ita ya yi ya ce, "iya wannan da ki ka faɗa ma ya isa."

Kallon fuskar ta yayi, cikin rashin tsoro ya ce, "Hakan yana nufin ina son Narma, daman na tambaye ki ne dan na tabbatar kuma na tabbatar É—in."

Cikin tashin hankali Didi ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Omar ka san abinda ka ke faÉ—a kuwa?. Kana son Narma ka ce fa? Don Allah ka faÉ—a min wasa ka ke yi." Da mamaki ya ke kallon ta jin tayi dogon salati ya ce, "wannan salati haka Didi na meye? Bata cancanci na sota É—in ba ne?."
"Omar kai ne baka cancanci ka sota ba, Omar ita ba ajinka bace, don girman Allah ka rufa min asiri ka bar maganar nan, Ina kai ina soyayya da Æ´ar gidan sanata Omar?."
"Kin zo a makare Didi, domin kuwa wannan asirin naki bazai rufu ba. Ina sonta kuma zan je har gaban sanatan na faÉ—a masa."

Didi numfashi ta ja kawai tayi shiru bata ce komai ba, dan babu amfanin maganr, ta san kuma wallahi sai ya aikata tunda ya faÉ—a. Hawaye yaga tana yi ya tausasa murya ya ce, "don Ina sonta shine ki ke kuka?."

Didi ta ce, "Omar bana so wani abun ya same ka, Ina ji a jikina soyayyarta bazata zama alkhairi a gare ka ba."
"Kin san gaibu ne Didi?." Jin tambayar da ya yi mata ya saka take kallon sa da mamaki, kenan dai da gaske son Narma yake yi tunda gashi yana yi mata wata bahaguwar tambaya.

"Ban san gaibu ba Omar, amma auren ka da ita da kamar wuya." Omar ya murmusa ya jingina da kujera ya ɗora ƙafa kan ɗaya ya ce, "ki taya ni addu'a kawai, amma kin san tunda na ɗauki hanya bazan karkace ba. Zan je har gidan su har gaban sanata na nemi auren ta, kin san bana jin tsoro komai kuma bana tsoron kowa. Ki kwantar da hankali ki daina kuka, babu abinda zai same ni sai alkhairi."

Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "ai shikenan" ta faɗa cikin rashin mafita dan ta san bazai bari ɗin ba kamar yadda yace. Ganin ta a yanayin damuwa sai ya yi ƙoƙarin kawar mata da tunani ya ce, "Ya zancen AbdulHamid? Kwana biyu bana ganinsa." Didi a sanyaye ta ce, "Ta ya zaka ganshi kullum kana ɗaki kana soyayya?."
"Hmm! Saura wata nawa bikin?."
"Ban sani ba" ta bashi amsa a taƙaice tana miƙewa ta shiga ɗaki ta bar masa falon.

Murmushi ya yi dan ya san haushinsa take ji, shi kam tunda ya ɗaura ɗammaara bazai kwance ba. Kiran Narma ne ya shigo wayarsa ya ɗauka ya ji ya ce, "Faruk na shigo Kano, Ina so mu yi magana da gaggawa, kuma zuwa dare zan koma Abuja. Na karo Mum gaisuwar rasuwa ne." Daƙyar ya ce, "maganar meye?."
"Ni dai Ina so mu haÉ—u, zaka zo ko nazo gidan ku?." Numfashi ya sauke kana ya ce, "kina ina?." Narma ta ce, "Ina guest house, amma ba wanda ka sani ba. Ina zaka zo zan baka address É—in, ko kuma naje wancan da ka sani sai mu haÉ—u."

Shiru yayi yana nazari akan zuwan kamar bazai ce komai ba, ta san halinsa akan wannan shirun yanzu sai ya ɓata mata lokaci har lokacin tafiyar su ya yi. Ta ce, "please na faɗa maka da wuri zamu bar Kano."
"Zan zo" ya bata amsa taƙaice kafin ya kashe wayar. Ba jimawa yaji ƙarar messege ya miƙe ya fita daga falon.

        Da kayan jikinsa ya tafi tunda Didi ta laqaba masa saka mayan kaya ranar juma'a. Bashir ne ya kai shi a machine ya kuma saka shi ya tsaya ya jira shi ya fito su tafi. Kafin ya zo Narma ta sanar da zuwan da hakan ya saka kai tsaye aka masa iso zuwa harabar gidan. Kiran ta ya yi a waya ya ce, "ki fito." Narma a sanyaye ta ce, "don soyayyar ka da annabi Muhammad S.A.W ka shigo, ba don halina ba" ta faɗa dan ta san zai ce bazai ce bazai shiga ba.

Jin magiya da tayi masa sai ya kashe wayar bashi da zaɓin da ya wuce shiga inda nuna masa matsayin nan ne hanya. Tafkeken falo ne mai kyau da tsari, babu haukan ado a cikin sa amma ya tsaru irin sa ake kira da luxury parlour. Tana tsaye a falon cikin riga da siket na atamfa ta yi mata matuƙar kyau. Kasancewar atamfar baƙa ce sai ta haska farar fatarta sosai.

Ta ɗame kamar ko yaushe, daƙyar take iya motsawa a cikin siket din. Rigar kuwa tsabar kamata da tayi gabaɗaya ana ganin saman ƙirjinta, gashi bata da tsaho in ta ɗaga hannu ana hango cibiyarta. Kallon farko in kayi mata zaka ga shigar ta ƙara mata kyau, amma in ka nutsu zaka fahimci fidda tsaraici ƙarara a tare da ita.

Bai san yana kallon ta sai da yaji ta a jikinsa ta rungume shi da sunan welcome hug. Shiru yayi kamar ruwa ya cinye shi, shi bai yi hugging nata ba kuma bai ƙoƙarin cire ta a jikinsa ba. "Nayi kewar ka" ta faɗa tana kwance a jikisa tana jin farin ciki da nutsuwa na shiga jikin ta. Maganar da ta faɗa ne ya saka shi janye ta daga jikinsa yana binta da shegiyar harara. Da yatsa ya nuna ta ya ce, "gargaɗi na karshe zan miki, kar ki sake aikata haka, kar ki sake cewa zaki riƙe ni, kar hakan ya sake faruwa in ba haka baza ki sake ganina a inda ki ke ba!."

Narma ta shagwaɓe ta ce, "I'm sorry, I just missed you ne shiyasa." Ƙaramin tsaki ya ja sai ta ce, "i'm apologize fa, smile please." Sake bashi haushi tayi dan shi baya son magana da turanci, duk abinda ta ce yaji amma baya ra'ayin ayi masa magana yaren. Murmushi tayi ganin ya sake tamke fuska, ita hakan ma yana matuƙar burge ta wallahi, sake ƙara mata ƙaunarsa yanayin sa yake yi a zuciyarta.

"Have a seat" ta faɗa tana nuna masa wajan zama. Kallon ta yayi da birkitattun idanunsa, yana ayyana dole ya taka mata burki akan turancin nan kafin hakan ya saka ya tsane ta. Bai musu ba ya zauna ta zauna nesa dashi kaɗan ta ce, "kayi kyau Faruk! Sai naga kamar ana ƙara maka kyau ne sosai." Kallon ta ya yi jin wata magana mai kama da zagi dan ya wuce zolaya, shi bai ce tayi kyau ba sai ita zata faɗa? Ina kyaun a wajansa.

Daman ta gama shirya center table ta kalle shi bata damu da rashin bashi amsa ba ta ce, "bismillah." Kallon abinda ta nuna ya yi ya kalle ta ya ce, "ki faɗa min dalilin ki na kira nan." Ta langwaɓar da kai ta ce, "Amma ka sha ko ruwa ne ko? Ni wallahi kamar baka yi kewata ba sai ɗaure fuska ka ke, don Allah kayi murmushi."

Kallon ta ya yi suka faɗa ido ya ce, "zuwan da nayi bai nuna miki abinda kike tunani ba?." Sai ta yi murmushi cikin zallar shagwaɓar da take sake canja masa yanayi ta ce, "haka ne my Faruk. Da kace zaka zo naji matuƙar farin ciki, domin kuwa na san tabbas na babban samu matsayi a wajan ka."

"To Ina jinki." Narma ta gyara zama ta ce, "Yaushe za ka zo Abuja ku haÉ—u da Dad É—ina? Ba a matsayin Tiger ba, a matsayin Faruk inlwa É—insa. Yaushe zaka zo?." Bata ji ya amsa ba hakan ya saka ta ce, "Ina so kaje don ya san da zaman soyayyar mu Faruk, bana son yin aure da wuri, amma tunda na fara sonka nake ji a zuciyata ina son yin aure da gaggawa."

Omar ya kalle ta yana wani tunani, ya rasa meyasa in ta yi zancen aure wani lokacin zuciyarsa bata karɓa, sai ya dinga ji kamar shi bazai aureta ba, sai ya dinga ji shi kamar ba aurenta yake son yi ba akwai abinda yake zuciyarsa ba aure ba. Ya kawar da tunanin ya ce, "na faɗa miki na shirya yin aure ne yanzu? Kuma shi ne ya ce nazo?."

"A'a, ni nake so kazo saboda ya san da kai ayi maganar aure a wuce wajan kawai." Kai ya girgiza ya ce, "baza ki samu matsala ba?."
"Babu wata matsala."
"To zan duba na gani, in na samu lokaci zan sanar dake sai ki faÉ—a masa." Narma tayi murmushin jin daÉ—i ta ce, "thank you my Husband to be. I can't wait to be your wife, I feel like na jawo lokacin da zaka kasance miji a gare ni. Ranar da aka ce na zama matar ka bazan iya bacci ba."
Chapter 47 · 0% Book details