← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 54

Sashe 33

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗakin gado biyu ne a ciki amma Didi ce kawai a kwance, Narma tana jingine da bango tana kallon Didi da aka gama saka mata ruwa bacci ya ɗauke ta. Hannun Didi ya riƙe wanda aka sakawa ruwan ganin zai faɗi ya ajjiye a gefen ta ya zare mata hijjabin jikinta ya sake taɓa wuyanta. Ƙaramin tsaki ya yi jin har lokacin da zazzaɓin ya ce, "Sai da nace mata kar ta fita amma taƙi ji."

Narma ita dai kallon sa take yi domin mamaki yake bata sosai, gabaɗaya ya sauya mata ya yi sanyi damuwar rashin lafiyar wacce bata san alaƙar su ba ta canja shi. Kana jin yadda yake magana kasan ko wacece wannan ya damu da ita sosai. Kallon gefen ta ya yi yaga tana kallonsa sai a lokacin ma shi ya tuna da ita dan wallahi tunda yaga yadda Didi take ya manta da wata Narma a bayan mota. Sai Narma tayi murmushi ta ce, "Zata samu sauƙi in sha Allah." Kai ya girgiza bai ce komai ba, amma yaji ta burge shi sosai.

Awa ɗaya suka kwashe a asibitin dan shi bazai iya tafiya ya bar Didi ba, ita kuma Narma duk ta gaji sosai. Bai ma lura da yanayin ta ba, abinda ya sani ko babanta ne zai zo bazai bar Didi ya tafi wani waje ba. Ya kalle ta ya ce, "zan kira waya azo a mayar dake gida yanzu." Narma ta ce, "A'a, ka bari ta farka sai mu tafi gabaɗaua, jikinta bai yi worst ɗin da za'a yi addminting nata ba." Shiru kawai ya yi bai sake cewa komai ba. Fita ya yi ya yi sallar magriba ya dawo a lokacin Didi ta buɗe ido. Bayan ya dawo ya ƙaraso inda take ya riƙe hannunta ya zaunar da ita akan gadon ya ce, "ya jikin?."

Didi ta ce, "na ji sauƙi sosai, ciwon kai ya rage sai rashin ƙarfin jiki da babu."
"Shima zaki daina ji in sha Allah." Ba sake magana ba ya fita jim kaɗan ya dawo ya kalle ta ya ce, "zamu tafi gida, ga magani da allurai an bayar, ai kin ce jikar Hajja ta iya allura ko?." Didi ta ɗaga masa kai, ya riƙota ta tashi tsaye ya saka mata hijjabi da kansa ya riƙe hannunta ya ce, "Mu je gida." Kallon Narma tayi ta ce, "Ka bar baƙuwar ta ka."
"Wacce baƙuwa?" Ya furta yana kallon Narma dan wallahi ya sake mantawa da ita.

Narma ta ɗan saki fuska kaɗan ta biyo bayan su. Yanzun ma Didi ya buɗewa gaba ta shiga, Narma ta shiga baya suka sake komawa gidan Didi. Narma tana mamaki kenan itace bazai buɗewa ƙofa ba tunda gashi yana buɗewa wacce bata sani ba. Suna tsayawa Narma ta ce, "Allah ya ƙara sauƙi."
Didi ta kalle ta ta ce, "Amin. na gode Barr Nass." Narma bata yi mamaki yadda ta santa ba tayi mata murmushi ta fita.

Bayan sun shiga Didi ta ce, "ka bar ni kaje ka mayar da ita gida, tayi ƙoƙari sosai wallahi." Ya kalli Didi ya ce, "zan kai ta, so nake na tabbatar kin samu lafiya."
"Na samu lafiya Omar, ka je ka mayar da ita ba kowa ne zai yarda da irin haka ba." Bai ce komai ba ya fita ya shiga motar bai ce mata komai ba har suka je gidan.

Fitowa yayi daga motar bayan ta fito ta kalle shi ta ce, "Allah ya ƙara lafiya, a gaishe ta." Dan kawai kallon sa take yi ne ya saka taga bakin sa ya amsa da amin, amma maganar ko kan harshensa bata zo ba balle laɓɓansa. Ya miƙa mata key ta girgiza kai ta ce, "kaje da motar saboda kana da mara lafiya, kaje da ita kawai." Kai ya girgiza ya ce, "bana buƙata" ya faɗa yana sake miƙa mata key ɗin.

"Ka je dashi." Ya girgiza kai ya ce, "bani da buƙata, na gode."

Murmushi tayi jin yana yi mata godiya ta karɓi key ɗin har ya juya ta ce, "Omar!." Wani iri ya ji a jikinsa, ya waiwayo ya kalle ta ta ce, "Ranar da aka yanke ni a hannu kaine ka biya kuɗin asibiti, na manta ban biya ka ba. Please ka bani account number ɗin ka na tura maka."

Kamar zai yi magana sai ya fasa ya É—aga kai kawai yana juyawa ya fita, ta bishi da kallo tana murmushin da bata san dalili ba. Mai gadi ta kira ta bashi key É—in motar ta ce ya kwaso mata kaya ya shigar mata dasu ita kuma ta shiga ciki.

        Omar kuwa haka ya koma gida sunansa da ta kira yake ji har cikin zuciyarsa bai san lokacin ba, ya yi murmushi Didi ta kalle shi ta ce, "murmushin me ka ke yi?." Ya ƙarasa shiga yana kallon ta ya ce, "ya jikin naki? Na ɗauka ma kin yi bacci kin huta."
"Ban yi bacci ba."
"Abinci fa?."
"Na ɗan ci, Hajja ce ta ta aiko min da abinci yanzu." Ya girgiza kai yana kallon ta ya ce, "To yanzu ki ki kwanta ki huta. Sai da nace miki kar ki je gidan bikin nan kika ƙi ji, wataƙila wani abun suka yi miki dan ki yi rashin lafiya daman ba son ki suke yi ba."

Tayi ƴar dariya ta ce, "naji, ko ma meye dai ƴan uwana ne." Ya taɓe baki bai yi magana ba. Tana  so tayi masa maganar Narma da inda ya koyi mota amma bata jin ƙarfin jiki hakan ya saka ta tashi taje ta kwanta shi ma ya fita zuciyarsa cike da tunani kala-kala.

Washe gari bai fita ba har yamma sannan ya je gidan dan yaga kiran Narma bai É—auka bane. Lokacin da ya je gidan shiru babu komai duk bai ga masu aikin ba bai damu ba ya yi zamansa a inda ya saba zama. Ihu ya dinga ji daga cikin gida, da farko ya É—auka kunnensa ne amma sai yaji abun ya yi yawa ihu ake sosai ana neman taimako.

Kamar kar ya shiga sai kuma ya miƙe ya shiga falon gidan dan bai san abinda ya faru a ciki ba, a daidai lokacin Narma ta sakko a guje daga ita sai towel ƙarami wanda ko cinyar ta bai gama ɓoyewa ba, kanta babu ɗankwali tana ihu kamar wacce aka biyo.

Ganinsa a tsaye sai kawai ta yo inda yake ya yi saurin yin baya dan yaga ƙoƙarin rungume shi take yi.

"Geckos a toilet É—ina, ka taimaka min ka kashe shi tsoronsa nake ji." Takaicin da Omar ya ji ji yayi kamar ya tsinke ta da mari ya tsaya kawai yana kallon ta cike da takaici. Wai tsaka take yiwa wannan ihum, da farko ya É—auka wasu ne suka shigo gidan da niyar cutarwa take kukan neman ceto.

"Ka taimake ni ka je ka kashe ta don Allah" Ta faÉ—a tana niyar yin kuka. Kallon inda ta sakko ya yi dan shi kam dai bazai hau saman ba. Mai aikin ta mace ce ta shigo tana cewa, "Hajiya lafiya?."
"Geckos zaki kashe, maza jeki toilet É—ina." Da sauri ta hau saman shi kuma ya fita bai sake kallon ta ba.

Zama ya yi yana amma gabaɗaya ita yake gani a idanun sa ɗaure da towel ta nufo shi a guje, runtse ido ya yi ya buɗe ya tashi zaune sosai ya tuna lokacin da ta riƙe shi da aka ƙwace mata waya, ya sauke numfashi yana jin sabon yanayi a tare dashi mai wahalar fasaarawa.

Bai jima sosai sai ga mai aikin ta ta ƙaraso ta ce, "Wai kazo." Ya kalle ta ya ce, "na zo?."
"Eh, haka Hajiya Narma ta ce." Kai ya ɗaga  mata kawai ta tafi shi kuma ya sake gyara zama dan bazai shiga ba. Bata isa ta aiko a kira shi ba kuma ya je, dan ta ga yana sake mata bata isa ta raina shi ba.

Ga mamakinsa sai gata ta fito cikin riga roba mai bin jiki ko ina na jikinta yana rawa. "Wannan yarinya bata da hankali!" Ya furta yana yana rufe idonsa. Ƙarasowa tayi ta ce, "Tiger daman tambayarka zan yi ya jikin mara lafiya shiyasa na kira ka ɗazu, da baka ɗauka ba shiyasa kayi tunanin akwai inda zan je." Omar ya miƙe tsaye jin tana tambayar lafiyar rabin ransa ya ce, "ta ji sauƙi."
"Allah ya ƙara lafiya, ka gaishe ta."
"Zata ji."
"Baka tura min account details É—in ba." Ya kalle ta suka haÉ—a ido ya ce, "zan tura."

Miƙa masa ledar jiya tayi ta ce, "ka barta a mota jiya, da na ce kwaso min kaya sai aka haɗa min har ita. Nace wannan ai saƙon Tiger ne ba nawa ba." Kallon ledar ya yi dan shi wallahi ya manta da ita gabaɗaya, karɓa yayi bai yi magana ba. Narma ta ce, "Zaka iya tafiya babu inda zan je."

Nan ma bai yi mata magana ba yana mamaki a ransa lallai ma ta samu sake, har zaka iya tafiya take ce masa wato ga yaronta. Ƙwafa ya yi kaɗan zai wuce ta ce, "Meyasa baka son yi min magana? Jiya naji kana ta magana amma ni baka yi min." Bai jiyo ba balle ya tanka ba ya wuce, a nan ya ga Ashraf a tsaye yana kallon su da alama ya jima da zuwa gidan. Bai ko kula shi ba ya fita daga gidan.

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

             ©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

Masu nema daga farko ga WhatsApp link nan.
https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t

*Book 1*
*P 16.*

Narma wajan Ashraf ta ƙaraso da yake kallon ta har tazo inda yake ya kalli Omar da ya fita ya kalle ta ya ce, "me ki ke yi a wajansa?." Narma ta ce, "mu je ciki" ta faɗa tana wucewa shima ya bi bayan ta.
Chapter 33 · 0% Book details