← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 54

Sashe 51

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 24.*

A zaune ya samu Didi tana waya ya zauna a kujerar da ya saba zama ya harɗe ƙafa yana kallon ta tana cewa, "Ya jikin na ki?." Shiru tayi ana bata amsa sannan ta ce, "Allah ya ƙara lafiya Nayla, a gaishe da su Mama." Ta Amsa daga nan ta yanke wayar. Ambatar Nayla da tayi ya saka shi ya tuna fuskar ta a lokacin da take hawaye, sai ya samu kansa da jin wani iri a zuciyarsa ba tare da ya san dalilin haka. "Omar ya aka yi?." Maganarta ta katse shi ya kalle ta ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ranar alhamis zan je Abuja wajan mahaifin Narma."

Didi ta kalle shi ta kasa cewa komai sai kallo, ta zuba masa ido bayan ta tallafi haɓarta da hannayenta. Ta ce, "Omar!." Jin yadda ta kira shi ya saka ya kalle ta sai ta ce, "Ka shirya aure ne? Yanzu in aka ce an baka aurenta kana da abinda zaka aure ta?."

Ajiyar zuciya ya yi ya sauke ƙafasa daga kan ɗaya, ya sarƙe hannayensa waje guda ya kalle ta ya ce, "ni ai na faɗa mata ban shirya aure ba, tana so iyayenta su san da ni ne kawai." Zuba masa ido tayi tana kallonsa, a tausashe ta ce, "Omar anya baka yi ganganci da rayuwarka ba? Anya baka saka zuciyarka a tsaka mai wuya ba?. Sai nake ji kamar akwai wani shiri da yarinyar ta shirya maka Omar."

"Didi babu wani shiri sannan babu abinda zai faru, Ina sonta kuma zan je wajan iyayenta matsayin mai sonta."
"Omar kenan, ta ya iyayenta zasu karɓe ka a matsayin mai son ƴar su?. Tausayi ka ke bani wallahi, domin wanna hasashe naka ba mai yuwa bane Omar." Kallon ta ya yi ya ce, "Didi bana so kina ce min haka, wai ita wacece da zaki dinga cewa tausayi nake baki a kanta?."

"Ita ba tsarar ka bace ba Omar, ita ba daidai da kai ba ce ba Omar." Kallon Didin ya ke yi na wani lokacin kafin ya ce, "Didi!."
"Omar."
"Bakya son abinda nake so ne?."
"Omar Ina so mana."
"Meyasa ki ke faÉ—ar abinda ki ke faÉ—a indai haka ne."
"Hmmm!" Didi ta faɗa a taƙaice bata ce komai ba. Omar ya ce, "kawai ki ta ya ni da addu'a." Didi ta ce, "Omar addu'a ko yaushe Ina yi maka ita ai, Allah ya baka abinda ka ke so in alkhairi ce."

Shiru ya yi Disi ta ce, "kuma kaima ka dinga addu'a, kana da ƙoƙarin ibada na sani, amma ka ƙara daga yadda ka ke Omar. Ka cigaba da yaƙi da shaiɗan kana tashi cikin dare, wani lokacin shaiɗan yana galaba a kanka. Ni shiyasa nake son ka samu mace nutsatstsiya mai ilimi wacce zata cigaba da taimaka maka wajan bunƙasa ibadar ka."

Kallon Didi ya ke yi har ta gama magana kafin ya ce, "oh kina nufin dai ban cikin masu ibada? Kina so ki ce mace ce zata saka na yi ko ta hana?."
"Ni ban ce baka yi, in na ce baka ibada ai ƙarya nake yi. Ko a unguwar nan an shaida sallah bata wuce ka a masallaci, sannan ni shaida ce, tunda ni nake rayuwa da kai. Ko a gaban Allah zanyi shaidar kana da ibada daidai gwargwado. Ina so ka ƙara ne kawai Omar, amma batun mace zata saka ka yi ko ka bari wannan zai faru." Taɓe baki ya yi bai ce komai ba ya yi shiru, ya lura adawa take yi da Narma shiyasa bai tanka ba.

Didi ta ce, "To a yadda ka ke ɗin nan Omar in ba dan kana ibadar ba ai da ban san ya zaka zama, Allah sai ya dubi maraicina ya taimake ni ya saka maka son ibadar a zuciyar. Malam Salahudden kuma shine sila, shi ya ɗora ka a kan hanya gashi yanzu baya duniya ka ɗore akan abinda ya ɗora ka a kai. Inda ace ibadar ma bata dame ka ba ai da yanzu ka kashe ni da raina." Ƙala bai ce ba, ya share ta yana kallon wani waje daban kamar ba da shi take maganar ba.

•••••••

Nayla lokacin da Didi ta yanke wayar taji sallamar Omar hakan ya saka ta yin shiru tana sauke numfashi a hankali. Dawowar ta daga office kenan ta samu kiran wayar Didi. Tashi ta yi ta shiga banÉ—aki tayi wanka lokacin har anyi magrib, ta fito ta yi sallah sannan ta fito falo. Tana fitowa Auta ya tare ta ya ce, "Anty Nayla ki zo in ji Mama."

Da to ta amsa tabi bayan sa zuwa ɗakin Mama ta shiga da sallama. Amsawa tayi tana kallon ta har ta shiga kafin ta ce, "Abiy ya ce a sanar dake kina da baƙo in anyi sallar i'sha." Nayla ta ce, "To" ta faɗa a sanyaye tana juyawa zata fita, Mama ta ce, "Nayla bakya son faɗa min damuwarki ko?." Nayla ta kulle ido ta buɗe ta juyo a hankali ta ce, "Mama ki yi haƙuri, ba na ƙi faɗa miki bane, kawai babu damuwar ne shiyasa."  Mama ta ce, "Shikenan jeki."

Nayla ta fito zuwa falo ta zuba abinci tana ta jagalgala shi amma ta kasa ci. Daƙyar ta iya cin kaɗan kafin ta tashi ta shiga ɗaki ta zauna kawai babu abinda take yi. Cikin wannan tunani har aka yi sallar i'sha ta tashi tayi sallah bayan ta idar hijjabi ta saka kawai akan kayan jikin ta dan na shan iska ne ba canja kaya zata yi ba.

Sallama akayi a ɗakin nata ta juyo taga Yaya da kansa ya kalle ta ya ce, "Nayla ga baƙon ki can a babban falo, ki yi sauri yana jiran ki."

Kai ta ɗaga kawai bata ce komai ba. Ya kalle ta sosai ya ce, "Nayla wai me yake damunki ne?." Murmushin ta ƙaƙalo ta ce, "Yaya na gaji ne kawai, zaman office ko wahala." Dariya ya yi ya ce, "Yanzu kika fara aiki ai Nayla, maza ki zo yana jiran ki." A hankali take takowa zuwa babban falon gaban ta yana faɗuwa sosai.

Da sallama ta shiga kanta ta na ƙasa ya amsa har ta ƙaraso ciki ta zauna. Kanta yana ƙasa ƙafarsa kawai ta iya gani ta haka ta fahimci a inda yake zaune. Nayla ta ce, "ina yini." Murmushi ya yi ya ce, "kin yini lafiya Nayla?."
"Lafiya lau" ta amsa a taƙaice.
"Ya aiki?."
"Alhamdu lillah" ta sake bashi amsa tana wasa da hannun ta. "Ma sha Allah. Sunana Omar ...." Bata bari ya ƙarasa ba ta ɗago da sauri suka haɗa ido dashi. Saurin ɗagowar da tayi ne ya saka shi ya dakata daga maganar da yake yi yana kallon ta. Ajiyar zuciya tayi ta sauke ido ƙasa ganin ba wancan Omar ɗin bane suna ne yazo ɗaya.

Murmushi ya yi ya ce, "me ya baki mamaki?." Kai ya girgiza alamun babu komai ya ce, "Sunana Omar Mansur Garkuwa, ni É—an garin Kaduna ne iyaye da kowa nawa yana cikin garin nan. Amma Ina aiki da NCC a Abuja a can make da zama." Nayla jin sa take ba fahimta take yi ba, shi kam yana ta magana yana gabatar mata da kansa amma ba ji take yi ba saboda hankalin ta baya tare da ita.

"Nayla!." Jin ya kira sunanta ta É—ago suka haÉ—a ido ya ce, "Ina sonki, auren ki nake da burin yi shiyasa na samu mahaifin ki da maganar ya ce nazo na same ki yau. Ina fata zaki amince dani."

Ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Allah ya zaɓa mana abinda yafi alkhairi." Murmushi ya yi ya amsa da amin ya ce, "ki saka min number wayarki" ya faɗa yana miƙa mata wayar. Karɓa tayi ta saka number ta miƙa masa wayar. Ya ƙarba ya ce, "na gode sosai Nayla, na gode da damar da kika bani." Murmushi tayi kaɗan kafin ya bata kuɗi ta ƙi karɓa tace ta gode. Babu yadda bai yi ba amma ta ce bazai karɓa ba dole ya haƙura ya ƙyaleta suka yi sallama ta koma cikin gida.

A falon cikin gida ta tarar da Abiy ana zaune kamar ko yaushe shida Yaya da Yaya Jawad da Auta da kuma Jalila da Mama. Abiy ya kalle ta ya ce, "baƙon naki ya tafi?."
"Eh Abiy, ya tafi." Abiy ya kalli Yaya ya ce, "A NCC yake aiki kuma bazai wuce sa'an ka ba, na san mahaifinsa a nan Kaduna suke gabaÉ—ayan su. Familyn Mansur Garkuwa ne. Yaron babu laifi gaskiya, yana da hankali ana ta yabonsa sosai."

Yaya yace, "Family Garkuwa Abiy? Lallai manyan mutane."
"Sosai kam. Amma ni yadda ake yabon kirkin yaron ne ya burge ni ba familyn sa ba."
"Ita samarin ma har sun yi mata yawa Abiy. Wannan shine na huÉ—u kenan fa, ga cousin É—inta Abbas."

Abiy ya murmusa ya ce, "bari kawai Babana, ka san bana son wannan yazo wannan ya tafi. Abinda ya jawowa Jidda aure ba tare da Nayla ba kenan" ya kalli Nayla ya ce, "Nayla bana son tara samari, bana son wannan saurayi yazo wannan saurayi ya tafi kema kin sani, kamar yadda na bawa wannan Omar ɗin dama zan bawa sauran dama a ciki ki zaɓi wanda ki ke so ki yi auren ki. In kuma Yayanki Abbas ki ke so shikenan."

Nayla ido ya ciko da hawaye ta turo baki ta ce, "To Abiy." Yaya J ya ce, "ke dallah meye na wani hawaye?." Ta goge ido tana kallon sa, Abiy yana dariya ya ce, "Nayla ce fa. Tunda kin fara aiki Nayla aure zaki yi, in Abuja kika tafi sai a nemi transfer ki koma can, in Kano ne sai ki koma can, in a nan ne dai duk ɗaya." Kanta na ƙasa sai ajiyar zuciya da tayi, ta miƙe Jalila na ta tsokanarta, Nayla ta harare ta ta miƙe ta shiga ɗaki.
Chapter 51 · 0% Book details