← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 54

Sashe 50

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba musu ta tashi ta kawo mata haɗi da ruwa ta sha kafin Jidda ta ce, "amma faɗa mana zai iya sakawa ki ji sauƙi a zuciyarki, kin san babu wanda zai ji labarin daga bakin mu." Nayla tayi murmushi ta ce, "qaunar da zaku nuna min shine ku yi min addu'a."

Ganin ta dage taƙi faɗar waye sai suka ƙyaleta suna ta hira har ita, dan ta ɗan sake amma da ta tuna sai hawaye. Sai tara na dare suka baro gidan Twiny zuwa gidan Hajja. A nan Hajja take faɗa mata ga abinci Didi ta kawo mata kaɗam ta iya ci ta ajjiye ta kalli Hajja ta ce, "Hajja gobe zan koma Kano, na kira driver Abiy zai mayar dani gida."

Hajja ta kalle ta tace, "Hauwa'u an fasa kaiwa jibin?." Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Na fasa Hajja. Na tuna akwai abinda zan yi a gidan, kuma ranar ranar litinin Ina da aiki." Hajja ta ce, "To Hauwa'u Allah ya kiyaye hanya ya nuna mana goben, Allah ya yi miki maganin damuwarki." Ta amsa da amin daga nan bata sake cewa komai ba, Salma tana kallon Labarina ita kuma ta miƙe ta shiga cikin ɗaki.

Kamar yadda ta fada washe gari da ƙarfe goma na safe driver ya zo daga Kaduna, sai da ta bari ya huta ya ci abinci a wajan Hajja bayan sallar azahar suka ɗauki hanyar Kaduna.

Ko a can kasancewar babu wanda ya san da dawowata, da yake ta asabar ce Abiy yana gida shi da Yaya Ahmad tayi sallama a falon ta shiga. Yaya ya ce, "A'a, mutanen Kano." Murmushi tayi ta ƙaraso ta zube akan carpet ta ce, "Abiy ina yini."
"Lafiya lau Mamana, ya kika baro Hajja?."
"Lafiya lau, tana gaishe ka. Ga saƙo ta ce a baka." Ya karɓa yana cewa, "Hajja bata gajiya da hidima in dai aka je sai ta bayar? Na kuwa gobe sosai. Zan yi mata waya na yi godiya."

Da Yaya suka gaisa kafin ya ce, "mutanen kano, ba sai gobe zaki dawo ba daman?." Ta yatsine fuska ta ce, "Gajiya nayi kawai na kira Baba Salisu na ce ya zo ya taho dani yau." Ya yi dariya ya ce, "ikon Allah, zaman Kanon ne kuma ya ishe ki?." Tayi dariya kaÉ—an Abiy ya ce, "nima nayi mamaki, bata faÉ—a min ma zata taho ba, sai Salisu ne yake cemin ita zai É—auko tayi amsa waya jiya, na ce to sai ka dawo. Gaskiya zan faÉ—awa Hajja taci tarar ki kin gudo kin barta."

Nayla tayi dariya ta miƙe ta shiga wajan Mama. Itama tayi mamakin ganin ta suka gaisa daga nan ta koma ɗakinta tana sauke ajiyar zuciya. Zaman Kano ai ba nata bane, indai tana son kanta da zaman lafiya dole ta bar shi.

Da daddare Mama ta shiga wajan Nayla ta same ta ta yi shiru ita kaÉ—ai. Zama tayi kusa da ita ta ce, "Nayla." Nayla ta kalle ta ta ce, "Na'am Mama."
"Tunanin me ki ke yi haka?."
"Babu komai Mama."
"Haba Nayla, kowa ya ganki ya san kina cikin damuwa mai yawa. Meyasa baza ki faÉ—a min ba? Ko dan bani na haife ki ba?."

Nayla ta girgiza kai ta ce, "A'a Mama ba haka bane, babu damuwar ne shiyasa." Mama ta zo kusa da ita ta riƙe hannunta ta ce, "uwa nake a wajanki, na haife ki na yi jika dake Nayla. In baza ki iya faɗa min damuwar kiba wa zaki faɗawa? In baki furta min abinda yake damunki ba wa zaki fadawa?. Uwa ce fa ni, ko bani da maganin damuwarki in nayi miki addu'a Allah zai amsa." Nayla kalaman Mama suka karya mata zuciya ta fara share hawaye. Mama ta sake nutsuwa ta ce, "faɗa min Ina jinki."

Nayla ta ce, "Mama babu komai, in akwai zan fada miki bazan ɓoye ba." Mama tayi murmushi ta ce, "shikenan Nayla. Allah ya yi albarka, ki fito ki ci abinci" daga haka ta tashi ta fita tana tabbatarwa da kanta ƙarya Nayla tayi mata, amma zata tambayi Jidda dan ta san ita ta san dalilin damuwar Nayla.

••••••••

Washe gari Didi ta shiga gaishe da Hajja ta kuma yiwa Nayla sallama dan fita zata yi kar ta shiga bata nan tarar da Nayla ta tafi, tayi mamaki sosai Hajja ta bata labarin a yadda ta shigo gidan da yadda ta ce ita ta fasa zama. Didi ta ce, "Allah ya sa ba Omar ne ya tsorata ta ba, dan ke baki ji ajiyar zuciyar da tayi da ta ganshi ba. Ni wallahi tsoron nasa da take ji ya fara bani tsoro." Hajja ta dinga dariya tana faÉ—in ba wani tsoro kawai akwai abinda yake damunta ne.

*Abuja*

Kamar ko yaushe suna zaune gabaÉ—aya suna hira Narma ta kalli Dad ta ce, "Dad." Ya kalle ta ya ce, "Narma." Narma ta ce, "mun gama magana da Faruk ya ce zai zo ku gaisa." Sai kuwa Najwa ta ce, "Awwnn! Ki ce shima dai yanzu da gaske yana yi ko Sis?."

Aka yi dariya Dad da fara'a ya ce, "da gaske ki ke?." Ta É—aga kai alamun da gaske kafin ta ce, "yana so ka bashi date da time É—in da zai zo." Dad ya ce, "wow! wannan abin farin ciki ne sosai. Inda zai iya zuwa ranar Monday zan so hakan, zan kira minister mu zauna tare domin mu tarbe shi" sai kuma ya kalle ta ya ce, "Ko kuma ranar Monday da aiki?."

Narma ta ce, "Dad ko yaushe ne zai zo indai a kaina ne. Zan faÉ—a masa in ya amince ranar monday É—in zai zo." Mum da take dariya ta ce, "oh my god! Narma....." Narma tayi dariya ta ce, "Mum I love him so much, my feelings for him are impossible to hide" ta faÉ—a tana murmushin sannan ta ce, "then he loves me too." Nabil yayan ta ya ce, "Ma sha Allah, muna taya ki murnar samun wanda ki ke so." Tayi murmushi ta ce, "thank you bro, let me go and call him" ta faÉ—a tana tashi ta shiga ciki a guje. Dad yayi dariya suna tattauna yadda za'a tarbi siriki in yazo.

Narma na shiga ɗaki Omar ta kira bai ɗauka ba, ta sake kira bai ɗauka ba sai ta ƙyale shi dan baya son tana tara masa kira. Wajan mintina kaɗan da kiran ya kira ta ta ɗauka da sauri ta saka a kunne sai ta ce, "kashe na kira ka."

Daga can ɓangaren Omar ya ji abinda ta ce ya maimaita a zuciyarsa, me take nufi kenan? bashi da kuɗin da zai iya kiran ta kenan sai dai ita ta kira shi?. Kafin tayi magana ya yanke wayar, Narma ta kira sau adadi yaƙi ɗauka.

Narma ta tayar da hankalinta ganin yaƙi ɗauka, ta je WhatsApp ta tara masa message tayi masa text message shima ba reply. Tun tana kiran sa har ta gaji ta kuma kasa gane laifin da tayi wanda ya saka ya yanke mata waya ya kuma ƙi ɗauka.

Shi kuwa Omar yayi haka ne dan ya koya mata hankali nan gaba bazata sake cewa ya kashe ta kira shi ba. Yana ganin message É—inta da kiran yayi banza ko kallo bai yi ba dan ya yi alqawari bazai É—auka ba, kuma bazai kira ta ba, zata san waye Tiger.

Sunday ta wuce, Monday ta wuce Omar baya ɗaukar wayarta kuma baya kiranta. Narma hankalinta ya tashi sosai sai ƙarya ta yiwa Dad ta ce ya ce ranar Monday baya nan. Sai ranar talata da yamma ya ga kiran na zuwa bai ɗauka ba sai da ta katse sai ya kira ta da hanzari ta ɗauka, tana sakawa a kunne ta ce, "laifin me nayi maka haka? Me nayi ka ke hukunta ni da wannan hukuncin Faruk?."

"Gobe in na kira ki sai ki sake cewa na kashe ki kira ni. Banda kin raina ni saboda kinga ina surarenki har ke zaki ce min wai na kashe ki kira ni? Nuna min ki ke yi bani da kuɗin da zan kira ki?." Jin yadda yake maganar da tsawa sai Narma ta ce, "I'm sorry...." Cikin tsawa ya katse ta ya ce, "kin manta gargaɗin da nayi miki ko?." Narma ta ce, "yi haƙuri, na saba da yin English ne ko yaushe shiyasa, Amma zan dinga kiyayewa. Kayi haƙuri don Allah."

"Mtsw! FaÉ—i matsalarki" ya faÉ—a kai tsaye yana sauraren ta.
"Ka yi haƙuri, nayi kewarka, kuma Ina sonka, Ina ƙaunarka." Sai ya ɗan sassauta murya bayan ya ja tsaki ya ce, "Ina jin ki."

"Daman tun ranar asabar na faÉ—awa Dad maganar zuwan ka ya ce in kana dama kazo Monday...au litinin, shine na kira na sanar dakai a lokacin."
"Yanzu sai me?."
"In zaka iya zuwa gobe yana jiran zuwan ka."
Omar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "bazan zo gobe ba, amma zan zo ranar alhamis hakan ya yi?." Narma tayi murmushi ta ce, "Ya yi Faruk É—ina, na gode Allah ya barmu tare na haifa maka yara masu kama da kai." Samun kansa ya yi da murmushi mai sauti har taji murmushin nasa. Omar ya ce, "na faÉ—a miki ban shirya aure ba ko? Ban ma san yaushe zan yi ba."

Narma ta ce, "ai fata nayi mana ko?" Ta faɗa cikin shagwaɓa tana narkar da murya. Shagwaɓar da take yi yana ƙara masa karkasashi da yanayin da ya saba ji in suna waya. Jin ya yi shiru sai Narma ta ce, "baka ce amin ba, baka so na haifa maka yaran ne?." Murmushi ya sake yi har Narma tayi mamakinsa, dan ta san sai a gama waya dashi bai yi maganar kirki ba balle murmushi. Ya ce, "Ki jira lokaci."

"Alhamdu lillah! Faruk yana son ya auri Narma har ya haɗa jini da ita. Wannan abin farin ciki ne." Nan ma murmushi ya sake yi amma bai ce mata komai ba, tana ta yi masa zance shi kam baya tanka mata sai ya ga dama, sai da ya gaji ya ce, "Zamu yi magana anjima" daga haka ya yanke wayar yana shafa gajin fuskarsa yana murmushi. Ajiyar zuciya ya yi ya miƙe ya shiga wajan Didi da niyar faɗa mata zai je gidan sirikai.
Chapter 50 · 0% Book details