← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 54

Sashe 52

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama ta bita da kallo ba tare da ta tanka ba. Familyn Garkuwa kawai take maimaitawa a zuciyarta, ta ya zata bar Nayla ta auri É—an Familyn Garkuwa?. Kaf wanda aka lissafa a cikin masu neman aurenta wallahi baza ta bari ta aure su ba, har cousin É—inta Abbas bazata bar auren ya yu ba. In ma ta bari ta aure su taje ta huta kenan taji daÉ—in zaman aure, ai wallahi yadda bata ji daÉ—in zaman aure ba Nayla ma baza ta ji daÉ—in zaman aure ba, duk yadda zata yi zata yi don ganin Nayla ta sha wahala a gidan aure, baza ta bari a kai Nayla inda zata ji daÉ—i ba wallahi. In ta bar hakan ya faru mahaifiyar Nayla ta ci bulus kenan, ita ta wahalar da ita a gidan aurenta kuma sai ta bar Æ´ar cikinta ta ji daÉ—i...? Wannan ai ba abu ne da zai yu ba wallahi. Kai ta girgiza tana cize baki tana tunanin abinda ya kamata ace ta yi.

•••••••
Thursday
10:00am

      Didi kallon Omar take yi ganin ya sha kwallaiya cikin manyan kaya riga da wando da hula, ya yi matuƙar kyau kamar ba Omar ɗinta ba. Omar ya kalle ta ya ce, "Didi mun shirya sai Abuja." Didi jikinta gabaɗaya a sanyaye ya ke ta ce, "to Omar, Allah ya kiyaye hanya."
"Amin. Don Allah ki daina sanyin jikin nan bana so."
"Omar ji nake kamar akwai abinda zai faru wallahi, bana so ka tafi Omar."

Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "Babu abinda zai same ni, kar ki damu." Kai ta girgiza ta ce, "kai da wa zaku je? Kana da abokan da zasu raka ka?."
"Ni ina da abokai ne? Sai dai yara su Bash."
"Dasu Bashir É—in zaku je?" Ta tambaya da mamaki tana kallon sa. Gira kawai ya É—aga mata sai gasu sun shigo kowa ya ci manyan kaya, Bashir da Goje ne, daman sune na hannun damansa, ba kamar Bashir.

Da kallo take bin su sai suka bata dariya ganin yadda suka yi wani iri dasu harda kwalli suka ranbaÉ—a su a lallai za a je gidan sirikai. Ganin Didi na dariya sai suna suka yi dariya dan sun fahimci canjin da suka yi take yiwa dariya.

Didi ta ce, "lallai su Bashir an ci kwalliya. To ina Tukur?
"Babbar Yaya ai baza a barki ke kaÉ—ai ba."
"Shi zai yi gadina kenan. To a mota zaku tafi?." Omar ya ce, "eh a mota zamu je."
"Allah ya kiyaye" ta faÉ—a tana kallon su kafin su fita ita dai gani take wani abun zai faru dasu dukkan su.

*Abuja.*

Ana ta shirye shiryen tarbar in-law, Dad ko fita bai yi ba yana gida saboda tunda ya ga Narma tana matuƙar sonsa ya san ba ƙaramin mutum ta ɗauko ba. Ya gayyato Minister don tarbar sa suna zaune a falo suna hira. Narma ta ci kwalliya sai murmushi take yi, bata kawo matsala a zuciyarta ko kusa, a ganin ta tunda tana son Omar dan yazo gidan sunba abin damuwa bane ba.

Narma ta sakko daga sama Mum ta bita da kallo tana murmushi ta ce, "my daughter, kin yi kyau." Tayi murmushi ta ce, "thank you Mum. Yau rana ce mai mahimmaci a wajena shiyasa nayi kwalliya."  Mum ta ce, "dukkan mu rana ce mai mahimmaci, ko haɗuwarki da Asharaf baki wannan farin cikin da ki ke yi yanzu ba."

Jin Mum ta ambaci Ashraf sai ta murmusa kawai tana tuna yadda suka ƙare dashi jiya, yana jajjada mata wallahi sai ya aureta babu wanda ya isa ya aure ta in ba shi ba. Dad ne ya shigo yana kallon Narma ya ce, "Daughter bai zo bane?." Narma ta kalli Dad ta ce, "bai ƙaraso ba Dad."
"Okay zamu yi sallah." Ta amsa Dad ya fita don su yi sallah.

Su Omar basu suka shiga Abuja ba sai ƙarfe uku na rana, duk sun jigata saboda zama mota, kai tsaye hotel suka je suka kama ɗaki a nan suka huta zuwa la'asar suka yi sallah kowa ya sake gyarawa sannan suka nufi gidan su Narma.

Lokacin da su Omar suka je ƙofar gidan Narma ya kira a waya ya ce mata gasu sun zo. Mai gadi ta kira a waya ta bashi umarnin buɗe musu su shigo. Mai gadi ya kalli su Omar bayan sun gama waya da Narma ya ce, "Hajiya ta ce ku shiga." Ya faɗa yana bisu da kallon mamaki.

Yadda ake ta zuzuta su, tun safe aka ce musu za a yi baƙi ya ɗauka zai ga motoci sun cika estate ɗin sai ya gansu taxi. Buɗe musu ya yi suka shiga gate ɗin farko suka shiga na biyu. Narma ya gani a tsaye da alama jiran su ta ke yi,da sassarafa ta ƙaraso inda suke dan takalmin ƙafarta ma silifa ne, tana zuwa ta kalle shi da murmushi ta ce, "Barka da zuwa Faruk."

Su Bash dai sunan tsaye suka yi, basu ɗauka inda Ogan nasu ya kawo kansa ya kai haka ba. Duk da sun san gidan, suna zuwa tare dashi wani lokaci. Kenan a gidan Sanata yake neman aure? Kuma wannan kyakykyawar budurwar ita yake so?. Gaskiya sun jinjina ƙarfin guiwa irin ta Omar, gashi babu damar magana balle su tanka, sun san halinsa. Narma ta ce, "mu je falon." Bayan ta suka bi tana tafiya tana yiwa ma'aikatan gidan faɗa, su kuma sai gaishe su suke yi suna ana bata haƙuri.

A babban falon ta kalli Omar ta ce, "Dad sun je masallaci, tun ɗazu suna jiran zuwan ka baka zo ba, yanzu zasu dawo." Omar ya girgiza kai ya zauna ko ɗar a zuciyarsa baya ji. Yadda ya zauna ya harɗe ƙafa sai ka ɗauka Sen ɗin ne da kansa, su Bashir kallon ikon Allah kawai suke yi, basu ɗauka lamarin ogan nasu ya kai haka ba.

Nan take aka cika gaban su Omar da abin sha da abin motsa baki. Narma ta fita ta koma cikin gida dan ta sanar da Mum zuwan su. Bash ya kasa haƙuri bayan ta fita ya ce, "Sai da kai Tiger, wallahi Madugu ƙwarin guiwar ka yana burge ni sosai. Allah ya bani ikon koyi da kai, Allah ya zamanin Jan wuya na mu." Omar bai ko kalle shi ba kaɗa ƙafa kawai yake yi, babu abinda suka taɓa abinda aka kawo musu. Su Bashir suna son cin koda Apples ɗin da aka ajjiye ne, amma waye ya isa ya taɓa bayan ga Boss a gefe bai taɓa komai ba? Sai dai kallon.

Dariyar Dad suka jiyo suna shigowa falon shi da minister. Turus suka yi ganin su Omar a zaune a kan kujera suna kallon masu shigowa. Kallo ɗaya Sen ya gane Omar ya kalle shi da mamaki ya ce, "A'a Tiger, saukar yaushe? Zuwa babu notice?" Ya faɗa yana ƙarasowa fuskarsa ba yabo babu fallasa.........

Senator ya haɗu da In law😂😂🫸🏼

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
wa.me/701 809 8175
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*_Godiya ta musamman ga waÉ—annan mutane masu karamci, kirki, daraja da kuma alkhairi._*

1-Halimahz
2-Oum Nabil
3-Jamila Umar Janafty
4-Oum Mumtaz
5-Maryam Kitty
6-Aisha Muhammad Alto
7-Autar Manya
8-Mai Dambu
9-Maryam Jumare
10-Maryam Hadeja
11-Zainab Kano
12-Aunty Nice
13-Gureenjoh.

_Ina miƙa godiyata a gare ku, Allah ya saka muku da alkhairi, Allah ya bar zumunci ya cikawa kowa burinsa na alkhairi amin._❤️❤️

*Book 1*
*P 25.*

Omar bai tashi tsaye ba kuma bai ce komai ba, su ma su Bashir ganin Boss bai tashi tsaye ba sai suka gyara zama. Sen ya ƙaraso yana bin su da kallo, ransa ya ɓaci ganin su a zaune akan kujera kamar wasu baki masu mahimmaci.

Minister ya kalli Omar ya kalli Sen ya ce, "Ina baƙin da aka ce mana sun zo?." Sen ya ce, "to nima dai ban ga kowa ba, nayi tunanin zan ga Bakuwar mota a car park amma ban gani ba."

Kallon su Omar ya yi ya ce, "ku jira ni daga waje zan gana da baƙi yanzu. Bana son irin wannan zuwan babu notice, ni ban san ma ya akayi aka bar ku kuka shigo ba wallahi. Mtsww..." Sai kuma ya ɗaga murya ya ce, "Auwal!." Da sauri wanda aka kira da Auwal ya shigo, Sen ya kalli su Omar ya ce, "kai su BQ, in na gama ganawa da baƙi sai su zo. A taƙaica waye ya bar su suka shigo? Irin waɗanan baƙin ba ni nake faɗa muku zuwan su ba?. Waye ya shigo da su?."

"Hajiya Narma ce" ya bashi amsa da girmamawa.
"Narma!" Ya maimaita cikin mamaki.
"Itace.." Sen ya tafi tunani, ya kalli Omar ya sake kallon Auwal ya kuma maimaita sunan Narma. Omar da ya ke jinsa yake kuma kallon reaction ɗinsa ya murmusa ya ce, "babu wasu baƙi da zasu zo Sen, mu ɗin nan dai mu ne baƙin." Da sauri Sen ya juya yana kallon Omar ya ce, "ban gane ba."

"Ba kana jiran zuwan sirikan ka bane?" Omar ya faɗa yana kallonsa kamar yadda shima shi yake kallo. Kasa magana Sen ya yi sai kallon Omar da yake yi cikin mamaki. Omar ya ce, "to ai ni ne." Sen ya yi ƙaramin tsaki tare da tamke fuska ya ce, "kai kar ka ga Ina wasa dakai, Ina baka damar zuwa gidan nan ko yaushe ka raini ya shigo tsakaninmu, ka tsaya matsayin da na baka. Ku tashi ku bar min falo!."

Narma ce ta shigo falon ta ce, "Dad!." Kallon ta ya yi cikin fusata ya ce, "Ina baƙin naki suke? Sannan kece kika buɗewa waɗanan falon nan suka shigo?." Narma cikin shagwaɓata ce, "ni ce mana. Kuma Dad ai sune baƙin nawa, Tiger shine Faruk ɗina, your inlaw."
"What!!" Sen ya faɗa da ƙarfin gaske yana kallon Narma da take kallon sa, ya kalli Omar da yake zaune har lokacin kamar falon babansa, ya kuma kalli minister da yake tsaye ya rasa ma abinda zai ce.
Chapter 52 · 0% Book details