Sashe 30
Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A cikin sakan biyar ta ƙare masa kallo har lokacin kallon ta yake yi duk da tana jin tsoro amma ta daure ta ce, "ina kwana." Bai amsa ba bai kuma daina kallon ta ba yana mamakin wannan yarinya da shegen naci take, bata jin magana duk da ya yi mata warning bata daina zuwa gidan ba.
Janye idanunsa ya yi bai ce komai ba, jin bai amsa ba sai ta ce, "Didi tana nan?." Nan ma yayi mata banza sai jikinta ya ɗan yi sanyi, daman gashi a tsorace take dashi gashi yayi mata banza. Kallon inda take ya yi yaga tana tsaye ya ce, "in zaki shiga ki shiga, in fita zaki yi ki bani waje!" Ya faɗa da ƙarfi bata san ta wuce shi a guje ba sai sautin tsakinsa taji tayi ajiyar zuciya.
Bata tarar da Didi a falo ba sai ta zauna kamar munafuka ta kasa sakewa, motsin shara taji ana yi sai ta miƙe ta kalli window ga mamakin ta shine yake share gidan a nutse, sai ta tsaya tana kallon sa tana murmushi wanda bata san tana yi ba. Didi da ta fito ta ga Nayla na kallon window sai ta yi murmushi tana daga bayanta ta ce, "Nayla." Firgigit tayi ta kalli Didi ta ce, "Didi yaushe ki ka fito?."
"Ta ya zaki san lokacin da na fito kina kallon mutumin ki yana shara? Ya baki mamaki ko?" Ta faɗa suna zama a kan kujera. Nayla sai taji nauyi kallon sa da ta tsaya yi amma bata nuna ba ta ce, "Sosai ma kuwa, kawai ji na yi ana shara sai na leƙa ashe shine, kawai sai na tsaya ina kallonsa."
Didi tayi dariya ta ce, "ai dole ki tsaya, In ya so ya ga dama shi yake yin komai a gidan nan hatta girki, har inda na kwanta shine zai gyara kuma baza ki ce namiji ne ya yi ba. Amma in bai ga dama ba abinda ya ci abincin ma ni zan É—auke." Nayla tayi murmushi tana kallon Didi ta ce, "shi dai sai ka rasa ka gane wanne iri ne, in ya yi gabas sai ya karkace."
Didi ta ce, "shiyasa nake faɗa miki yana da kirki fiye da tunaninki, yana da hira sosai. Kawai bashi da saurin sabo ne kuma baya son baƙi kwata-kwata."
Nayla daɗi take ji a zuciyarta ana hirar Omar hakan ya saka ta sake gyara zama ta ce, "ina fa kirki a nan Didi, har gaishe shi nayi yayi min banza." Didi ta ce, "bazai amsa ba ai, in kinga ya amsa to tabbas kun sana dashi matuƙa. Naga alama dai tsoron na sa ya ɗan ragu a zuciyarki."
Nayla ta ce, "hmm ina fa, wallahi akwai daurewa nayi nazo na gaishe ki, kwana biyu kin yi rashin lafiya." Didi tayi dariya ta ce, "ai kuwa na gode sosai Nayla, Naji daɗi matuƙa Allah ya bar zumunci." Nayla ta amsa da amin amma a zuciyarta kawai so take a cigaba da zancen Omar. Ƴar hira Didi take janta da ita akan labarin mutanen Kaduna da Hajja tana amsa mata da lafiya kowa yake.
Shigowarsa suka gani ya canja kaya zuwa jeans blue da farar riga mai layi-layi a jikinta, riga ta mai dogon hannu ce, sai ya tattare hannun rigar zuwa guiwarsa hannun, farin hannunsa da gashin da yake a kwance a hannun ya bayyana sosai, hakan da yayi sai ya ƙara masa kyau sosai. Nayla kallon sa take yi kawai cikin burgewa, daga sama yana da faɗi duk da ba faɗi sosai ba, amma daga ƙasa ɗan ƙarami dashi kuma a tsuke kana ganin sa kaga halittar cikakken namiji jarumi.
"Ina zuwa haka Alhaji Omar?." Didi ta tamabaya tana kallon sa da murmushi. Ya kalle ta bayan ya ɗage gira ya ce, "Yaushe ki ka fara sanin inda zan je?." Tayi dariya ta ce, "abin ne da mamaki, naga ƙarfe sha biyu ma bata yi ba ka shirya. Ko wajan yarinyar nan zaka je?." Agogo ya kalla ya ce, "A'a sai anjima."
"To ina zuwa ko abinci baka ci ba?."
"Bana son cin komai, zan je wani waje wataƙila bazan dawo ba sai dare." Didi ta girgiza kai ta ce, "Allah ya kiyaye Alhaji Omar Faruk." Murmushi ya yi yace, "Amin."
Murmushin da ya yi shine ya saka narkar da Nayla a kogin kallonsa har bata san ta tallafi haɓar ta tana kallonsa ba, ya gama tafiya da ita daga shigarsa, da maganarsa, uwa uba murmushin da yake sakawar Didi.
Sai da ya fita sannan ya kalli Didi taga tana neman wayarta sannan ta miƙe ta ce, "Didi bara na koma." Didi ta ce, "da wuri haka? Na ɗauka sai anjima." Nayla ta ce, "zan dawo anjima in sha Allah, ai yanzu na rage tsoronsa." Didi tayi dariya ta sake yi mata godiya ta raka ta har waje sannan ta dawo.
Nayla sai da ta tsaya a gate ɗin gidan Hajja ta dinga sauke ajiyar zuciya. Namiji mai murɗaɗɗen jiki irin na sa sam basa burgeta, hasalima itace mai kushe duk wani namiji mai irin wannan jikin, bata ƙaunar su tafi son namiji mai normal jiki ba wannan murɗewar ba. Wannan halitta tana daga cikin dalilin da ya saka bata so ace Abbas yana sonta, dan ta san baza ta so shi ba saboda jikinsa dan shi ya fi Omar murɗewa. Amma yau Omar ya burgeta, ya tafi da imaninta fiye da tunanin ta har mamaki abin yake bata. Har hango kanta take yi ta kwanta a ƙirjinsa tana hasahen wanne irin yanayi zata ji a wannan lokacin.
Da ta rufe ido murmushinsa take gani, sau biyu kenan taga yana murmushi, hakan ya shiga cikin tarihin ta dan tun daga murmushin farko da ta gani ya yi komai ya canja, faÉ—uwar gaban da take ji akansa ta canja salo zuwa harbawar zuciya a duk sanda tayi araba dashi. A haka ta shiga gidan zuciyarta na bugawa sossi.
Shi kuwa Omar yazo zai fita sai kiran Sen ya shigo wayarsa ya ɗauka yana shiga ɗakin sayana amsawa. Gaisawa suka yi Sen ya ce, "Tiger Narma ta faɗa min duk abinda ya faru jiya, gaskiya i'm so proud of you, naji daɗin taimakon da ka yiwa Narma sosai." Omar ya ce, "babu komai. Amma ka ja mata kunne Kano ba Abuja bane, akwai masu ƙwace sosai wanda za su yi mata illa ma kafin su ƙwace ɗin. Ta kula in zata fita ta daina kaiwa dare, in ta kai dare ma kar ta sake ta tsaya a ko ina. Allah ne ya taimaka da har motar zasu ƙwace musamman in suka lura da bata san gari ba."
Sen ya ce, "ai ganganci ne irin nata, na faɗa mata duk inda zata je ta kira ka amma bata ji." Omar ya ce, "tafiyar mu baza ta zama ɗaya ba, ni bana son ɓata lokaci ko kaɗan, kuma dai yanayinta bai yi daidai da nawa ba." Sen ya ce, "kar ka damu yanzu ta fahimci abinda nake nufi." Omar ya ce, "babu komai."
"Yau zata je biki zata kira ka."
"Allah ya kaimu."
"Amin. Akwai saƙonka na kyautatawar da ka yi mata jiya, naji daɗi sosai."
"Na gode" ya bashi amsa a taƙaice kafin Sen ya kashe wayar.
Æangaren Narma a daren sai da tayi mafarkin Omar, da ta farka sai kawai ta É—auka taimakon ta da ya yi ne ya saka haka. A haka ta tashi ta shirya dan a ranar zasu fara bikin Samra. Ƙawayenta guda uku ne suka zo gidan, ganin hannunta a É—aure suka dinga yi mata sannu kafin ta sake a fara hira.
Da wuri mai kwalliya tazo aka fara yi musu kwalliya, sai da aka yiwa duk ƙawayenta sannan aka yi mata a lokacin an idar da magriba. Narma tayi kyau cikin ankon kamu dukkan su dogayen riguma suka yi marasa kama jiki, amma Narma fitted gown tayi wacce ta kama ta matuƙa, sannan saman rigar gabaɗaya net ne a jiki ana ganin jikinta.
Ganin yadda tayi kyau duk suka ruÉ—e suna zugata ita kuma tana jin daÉ—i tana fari da idanu. A lokacin Ashraf ya zo gidan haÉ—a ido da ya yi da Narma ji ya yi kasala ta saukar masa lokaci É—aya, ya haÉ—É—iye yawu ya bita da kallo ya ce, "Beb ke ce?." Gira ta É—aga masa ya ce, "you look so magnificent." Mursmushi tayi ya matso aka fara yi musu hotuna masu kyau.
Ashraf ya ce, "Amma dai ni zan kai ki ko?." Narma ta ce, "Dad ya ce Tiger ne zai kai ni."
"Tiger again?."
"Yes, sai dai mu haÉ—u a can." Ya girgiza kai ya ce, "Okay normal, sai mun haÉ—i din." Daga nan suka yi sallama ya fita su kuma suka fara sallar i'sha. Narma dai sai da ta cire rigar gabaÉ—aya sannan ta iya sallah bayan ta idar ta mayar.
A cikin ƙawayen ta wacce suke kira da Safna itace babbar ƙawar Narma, ta kalle ta taɓe baki ta ce, "Narma ya kamata ki daina wannan ɗinkin fa, yanzu an daina wannan matsewar musamman ke da kike da halitta irin wannan."
Narma ta ce, "kina da matsala Safna, to in ban nuna halittar da Allah ya yi min ba meye amfanin ta?."
"Ki adana sai ki yi kwalliya a gidan mijinki."
"Ke baki ga yadda Ashraf É—in ya ruÉ—e da ya ganni haka ba? Da iya surata nake sake kama zuciyarsa. Kuma in bai ga abinda nake dashi ba ta ya ya zai yi mararin aurena?."
Safna ta ce, "amma hakan ba daidai bane, wannan shigar zata iya jawo miki abinda ba kiyi tunani ba Narma. Ina yawan faÉ—a miki wannan maganar amma bakya ji, su Nasreen su daina zugaki, wallahi cutar ki suke yi. Da wannan shigarta ki babu lallai ki samu wanda zai aure ki saboda Allah."
Gabaɗaya suka yiwa Safna can akan abinda ce ita dai tayi musu banza suka ƙaraci surutun su. Ɗaya daga cikin su da ta fita ta shigo yana cewa, "Nass yanzu da bouncers ki ka dawo yawo?." Narma ta ce, "a ina?."
"Gashi nan" ta faÉ—a tana nuna musu Omar ta window wanda ya ke tsaye yana amsa waya.