Sashe 38
Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Juyowa tayi ta kalle shi ganin yana kallon ta sai ta yi murmushi ta ɗaga masa hannu alamun bye, bai ko motsa ba sai ma buɗe motar da ya yi ya shiga ya tafi ita kuma ta girgiza kai tana tafiya. Wannan ɗabi’ar ta sa ta ko in kula tana matuƙar burgeta. A haka ta ƙarasa ciki ta tana jin wani abu mai kama da kewa na shiga jikinta.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleemaâ¤ï¸
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
Â Â Â Â Â Â Â Â©ï¸ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
*Book 1*
*P 18.*
Omar tuƙi yake yana tuna murmushin Narma tayi da ta juyo tana ɗaga masa hannu, bai san ya yi murmushi ba sai da ya kalli inda ta zauna har lokacin ƙhamshin turarenta bai daina tashi daga motar ba. Haka yake tafiya har ya koma gidan ya tarar Yahya yana nan ya bashi key ɗin motar ya fito zuwa gida. Da ya koma bai shiga wajan Didi ba ɗakinsa ya shiga ya kira Sen a waya domin ya sanar dashi aikin da ya saka shi ya kammala lafiya.
Sen kamar gaske ya yaba sosai kafin su yi sallama ya kashe wayar yana jin wani abu mai nauyi a zuciyarsa. Gajiya yayi da zaman kasancewar rana ta yi ga yunwa da yake ji dan bai karya ba. Yana fitowa daga É—akin Nayla tana shigowa gidan, kai tsaye idanunsa ya faÉ—a cikin nata da mamaki. Saurin janye ido tayi saboda abinda taji yana sukar zuciyarta, bata iya jure kallonsa ko ya ya yake.
"Ina yini" ta furta cikin sanyi tana niyar gifta shi. Ga mamakin ta sai ta ji ya amsa hakan ya saka ta juyo tana kallon sa shi kuma yana kallon waya, ji ya yi ana kallon sa hakan ya saka ya kalle ta sai ya ga tayi murmushi ta É—auke ido ta shiga wajan Didi.
Didi ganin ta ya saka ta murna suka zauna suna hira kafin Nayla ta ce, "Didi gobe zan koma Kaduna in Allah ya kaimu, sallama na shigo nayi miki." Didi tayi sak cikin rashin jin daɗi ta ce, "da wuri haka?." Nayla ta ce, "wallahi, naso Abiy ya barni na ƙara kwanaki amma ya ce a'a na dawo."
"Wallahi na ɗauka zaki kai gab da ramadan a garin nan tunda naga azumi ya kusa. Allah ban ji daɗin tafiyar nan da zaki yi ba Nayla." Nayla ta ce, "ni kaina ban taɓa jin bana son tafiyar ba kamar wannan lokacin, sosai nake jin bana so na bar Kano."
Didi ta ce, "in kin tafi sai yaushe?." Nayla ta ce, "Wallahi ban sani ba Didi." Didi ta ce, "Allah ya kiyaye hanya ya kai ki lafiya." Ta amsa da amin Didi ta tashi ta shiga ɗaki sai gata da turaren da Omar ya siyo mata ta kawo mata ta ce, "Na rasa me zan baki Nayla, ga turare sabo ne mutuminki ne ya siyo min shi shekaran jiya." Nayla ta karɓa ta ce, "na gode sosai Didi."
"Haba tsakanin mu babu godiya Nayla. Wallahi duk ji nake yi bana so ki tafi."
Nayla kam murmushi take yi ko babu komai ta samu abinda ya fito daga hannun Omar. Shigowa falon ya yi fuskar nan a tamke matuƙa kamar zai yiwa Didi magana sai ya fasa ya juya zai koma. Didi ta ce, "Omar Nayla ce zata tafi gida gobe." Tsayawa ya yi ya kalli Didi bayan ya ɗora yatsunsa a goshi ya ɗan murza kaɗan ya ce, "Wace haka?." Wani irin yarr Nayla taji a jikinta, haka nan idanunta suka taru da hawaye, kenan yana nufi bai ma san sunan ta ba.
Didi ta nuna Nayla ta ce, "gata a zaune." Omar ya tsaya kawai yana kallon Didi cike da takaici. To ina ruwan sa da tafiyar da zata yi banda abin Didi da take son saka shi a sabgar yarinyar, shi kuma tunda tayi masa faÉ—a a gabanta wallahi yake jin haushinta, ya tabbatar ba zai daina jin haushin ta ba har abada.
Bai ce komai ba ya fita Didi ta kalli Nayla ganin tayi shiru ta sunkuyar da kai sai ta ce, "Yi haƙuri Nayla, Omar ne sai addu'a. Ta bakin Hajja ta ce carbin ƙwai ne, jan sa sai mai nutsuwa." Murmushin yaƙe tayi kaɗan tayi mata sallama ta fito zuwa ƙofar gidan. Yana zaune a ƙofar gidan da yaran sa suna magana, Nayla ta wuce da sauri sai da taje gate ɗin gidan Hajja sannan ta tsaya tana sake kallon sa.
Wayar ta ta É—auko ta yi zooming É—insa sosai tayi masa hoto ba tare da ta san dalilin aikata hakan da tayi ba. Wajan Hajja ta shiga ta nuna mata turaren da Didi ta bata kafin su shirya tafiya gidan su Salma dan tayi musu sallama.
Har suka je suka dawo Nayla bata da walwala, Salma tayi-tayi ta faɗa mata abinda yake damunta tace babu komai. A haka suka dawo wajan Hajja Salma tana ta ciwon bakin taƙi faɗa mata damuwarta, Hajja tace bata son komawa Kaduna ne ta ƙyale ta kawai.
ÆŠakin da Nayla take kwana Salma ta shiga ta É—auki wayar Nayla da take gefe ta ce, "bara na tura hotuna." Nayla bata ce komai ba Salma ta fara duba wayar. ÆŠagowa ta yi ta kalli Nayla kafin ta ce, "Wannan ba hoton Tiger ba ne?." Jin hakan sai gaban Nayla ya faÉ—i, ta kalli Salma dan bata da mafita ta riga ta gani. Cikin borin kunya Nayla ta ce, "Hotonsa kuma?."
Salma ta haska mata fuskar wayar ta ce, "gashi nan." Nayla ta ce, "oho ban ma san na É—auka ba." Salma ta bita da kallon rashin yarda ta ce, "gashi har zooming É—insa akayi ki ce baki san kin É—auka ba?." Nayla tayi shiru bata ce komai ba.
Salma ta ce, "me ki ke nufi da É—aukar hotonsa Nayla?." Tayi shiru bata ce komai ba Salma zata sake magana ta ce, "Don Allah Salma ki yi shiru, ki bar ni naji da abinda yake damuna don Allah. Na ce miki ban sani ba ai, ga wayar nan a hannunki ki goge mana." Salma ta ce, "ai ko baki ce ba sai na goge" ta faÉ—a tana goge hoton ta ajjiye mata wayar ta fita bata sake magana ba.
Washe gari ƙarfe sha ɗaya na safe Abiy ya iko da driver. Nayla na shan tea taga kiran drivern gidan su sai da gabanta ya faɗi, ta ɗauka nan yake sanar da ita yana waje ta kashe wayar. Kallon Hajja ta yi da salma ta ce, "Hajja ya zo zamu tafi" ta faɗa a sanyaye tana ajjiye kofin shayin hannunta.
Hajja ta bita da kallo ta ce, "Zo Hauwa'u." Ba musu ta ƙarasa kusa da ita ta zauna, Hajja ta riƙe hannunta tace, "faɗa min damuwarki." Sai kawai ta rungume Hajja ta ce, "bana son tafiya Hajja, bana son tafiyar nan, wani iri nake ji a zuciyata Hajja. Bana so na tafi wallahi."
Hajja ita kanta zuciyarta sai tayi rauni, tana matuƙar ƙaunar Nayla saboda kasancewar ta marainiya, kuma a cikin ƴaƴanta mahaifiyar Nayla ce kawai ta rasu, tana kallon Nayla kamar ƴarta da ta rasa. Hajja cikin shigar rarrashi ta ce, "ki yi haƙuri, ki daina kuka, kin ga bakya koma gida masa kina yi masa kuka ba, bazai ji daɗi ba. Ki yi haƙuri ai zaki sake dawowa nan gaba in sha Allah." Nayla ta ce, "Bazai bar ni na kusa ba Hajja, Abiy baya so nayi nisa dashi" ta faɗa tana kuka sosai wanda ya bawa Salma mamaki kawai ta zuba mata ido.
Hajj ta ce, "kewar mahaifiyarki yake yi shiyasa baya so ki yi nisa dashi, gani yake kamar zai rasa ki kamar yadda ya rasa ta. Ki daina ku ka kin ji?." Ta goge ido ta ce, "To hajja." Hajja ta ce, "Akwai saƙo a kitchen ki kaiwa Abban naki, sannan akwai wani ma a bokiti ki bawa Maman taki kin ji?." Nayla ta ɗaga kai tana tashi ta ɗauko ta ajjiye a kusa da ita. Ta ƙarasa jikin socket ta zare chargerta, ta shiga ɗaki ta ɗauko trolly bag ɗinta da handbag ta fito bayan ta saka mayafi.
Salma tana tsaye tana kallon ta tace, "Nayla wallahi mamaki ki ke bani, kamar yau kika taɓa zuwa wajan Hajja zaki koma ki ke wannan kuka?." Hajja ta kalli Salma ta ce, "Ki kaiwa Salisun abin kari ya karya kafin su wuce." Salma ta wuce zuwa kitchen ta haɗa masa ta fita ta kai masa.
Nayla bata ce komai ba amma ta san ita kanta wannan kukan ba wai na rabuwa da Hajja bane kawai, tabbas akwai manufarsa a ƙasan zuciyarta, amma ta kasa gane meye shi. Sai da aka bashi lokaci ya gama, ya shigo da kayan da kansa ya gaisa da Hajja sannan ya fita.
Hajja har bakin gate ta rako Nayla, Salma ta É—aukar mata jaka suka fita ta saka a cikin booth É—in motar, Nayla ta kalli Hajja ta É—aga mata hannu kafin Hajja ta koma.
Kallon gidan Didi tayi sai ta hango Didin na ƙarasowa inda take, murmushi Nayla tayi tana kallon ta Didi cike da tsokana ta ce, "Kukan tafiya daga Kano ki ke yi Nayla? Ko da yake ai dole, ɗan ƙauyen Kaduna ai dole ya yi kuka in zai bar birni." Dariya Salma da Nayla suka yi Didi ta ce, "na ɗauka zaki sake shigowa mu yi sallama." Nayla ta ce, "kar na tsayar dashi ne shiyasa."
"Allah ya kiyaye hanya Nayla, ko Kano zata yi kewarki balle mu da muke cikin ta." Murmushi tayi ta amsa da amin tana ji ina ma tana da zarrar tambayar Omar da ta ce ina yake.