← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 54

Sashe 2

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan take jikinsa ya soma, yana kallom Omar yana karkarwa dan daman an faÉ—a masa Omar indai akan Yayarsa ne babu abinda bazai yi ba. Omar ya kalli cikin idonsa cikin dakakkiyar muryarsa irin ta jarumai mazajen gaske ya ce, "maimaita abinda ka faÉ—a mata naji." Jikin Muktar rawa yake yi sosai, ji yake kamar ya yi fitsari saboda tsoro ya kasa furta komai saboda tashin hankali.

Aisha da take tsaye itama t ce, "Omar meye haka ne? Ka sake shi!?" Ta faÉ—a cikin É—aga murya. A fusace ya kalle ta ya ce, "DIDI ki matsa baya, babu abinda zai hana ban farka bakin wannan mutumin ba. Nan gaba na ga da wanne bakin zai furta irin abinda ya ce yanzu" ya dawo da kallon sa ga Muktar shi ya ce, "Tunda ya tako har cikin gidan mu babu abinda zai hana ban É—auki mataki a kansa ba. Ko na datse masa harshe, ko na farka cikinsa."

"Wayyo Allah na shiga uku!. Aisha don girman Allah ki taimake ni, ki ce ya ƙyale ni, ki taimaka min kar......" maganar da ta maƙale saboda wuƙar da ya kawo kusa da wuyan sa ya ce, "kana cigaba da magana wallahi sai dai uwar ka ta haifo wani."

Ɗif ya yi ya kulle bakinsa da jikinsa yana karkarwa sosai nan da nan hawaye suka fara ambaliyya daga idanunsa saboda tsoro. Didi ta ƙaraso wajan ta riƙe hannunsa ta ce, "Omar ka ƙyale shi ya tafi na ce ko?."

"Bazan ƙyale shi ba. Ba shi yana da zarrar zuwa har gidan nan yake cewa ya fasa aurenki ba?
Inda iya wannn kalmar ya faɗa da sauƙi, amma har magana mara daɗi ya faɗa a kanki. Didi ko duniya ce zata taru yau babu abinda zai hana ban farka cikin mutumin nan ba."

"To ba ni aka faɗawa magnar ba ina ruwan ka...? Malam ka cika shi ya tafi bana son wannan ɗabi'ar" Ta faɗa da ƙarfi tana son cire hannun Omar daga wuyan Muktar amma ta kasa.

Kallon Muktar ɗin ya yi da yake hawaye kamar ƙaramin yaro jikinsa na rawa sosai ya ce, "ka ci albarkacin ta a yau ka sha, amma kar ka sake idanuna ya sake ganin fuskar ka, In kayi wannan gangancin zaka yi dana sanin zuwan ka duniya." Kai yake ɗaga kamar ƙadangare saboda tsoro Omar ya ce, "baka da baki!?." Yadda yayi maganar cikin tsawa ya ake firgita shi ya ce, "na....ji....ka yi....ha...ku....ri."

Omar ya cika masa wuya ya kalle shi ya ce, "durƙusa ka bata haƙuri." Babu ɓata Lokaci ya zube a ƙasa ya ce, "Ki yi haƙuri Aisha, na tuba ki yafe min." A fusace Omar ya ce, "sunan ta ka ke faɗa kai tsaye babu girmamawa? Sa'ar ka ce?." Jiki na karkarwa Muktar ya ce, "ki yi haƙuri Mama, Allah ya wuci zuciyarki."

"Haifar ka tayi da zaka ce mata Mama!?" Ya sake faɗa yana cakumar rigarsa. Muktar ya fashe da kuka mai sauti ya ce, "Ki yi haƙuri Anty, ki yi haƙuri don Allah." Omar ya sake shi ya nuna masa ƙofa ya ce, "bar nan." Ai bai sake magana ba ya fita a guje ko takalman sa bai ɗauka ba saboda tsoro.

Omar ya kalli inda Didi take ganin bata wajan ya san ta shiga gida ya kalli yaransa da suke ƙofar gida ya ce, "duk ranar da ya shigo area nan kar ya fita da lafiya." Dukkan su suka haɗa biki suka ce, "An gama Damisa, a fito Lafiya Magudu uban matsiyata." Ya jiyo idanunsa masu ban tsoro ya kalle su ya ce, "Zaku iya wucewa anjima sai ku zo" yana gama faɗa ya shiga gida yana jin su suna amsawa.

        Yana shiga tsakar gidan Didi ta tare shi ta ce, "Omar me yasa ka ke min haka ne? Omar me yasa ka ke son saka min ciwo ne wai?." Zai yi magana ta ɗaga masa hannu ta ce, "kar ka ce komai sai na baka dama. Ya ka ke so nayi ne? Me ka ke so ka zama ne Omar? Yau gabaɗaya satin ka biyu da fitowa daga prison bayan ka shafe kwana goma a ciki, so ka ke ka kuma komawa ne?."

"Didi...." Ta katse shi ta ce, "ba wani Didi, babu wani Didi kar ka ƙarasa. Omar me ka ke son zama ne don girman Allah? Ɗan ta'adda ka ke so ka zama ko me? A gaban idona ka dinga zancen zaka farkawa wani ciki?."

"Duk abinda ya faɗa miki naji, in ya fasa auren ki ya faɗa cikin magana mai daɗi mana sai ya faɗa da wulaƙanci?. Na rantse da girman Allah ba dan ke ba sai na yiwa bakinsa illa."

"To waye zai aure ni bayan kowa tsoron ka yake ji? Da irin wannan dabi'ar taka ka ke so na yi aure Omar?. Wanne iyaye ne zasu amince ɗansu ya aure ni bayan ina da ƙani irin ka?." Ganin idon Yayar tasa ya fara kuka da hawaye sai ya lumshe idanunsa ya buɗe ya kalle ta ya ce, "Didi don ina so ki yi aure ba haka yana nufin zan juri ko wacce kalma a kanki ba, Wallahi ko waye yayi ƙoƙarin ɓata miki rai shima sai nasa da na danginsa ya ɓaci."

Didi ta ce, "waye yace maka raina ya ɓaci?Gaskiya ya faɗa Omar kowa a unguwar nan kallon da suke min kenan. Ban taɓa aure ba muna zaune da kai a gida ɗaya gani suke kamar ni da kai wani abun mu ke aikatawa mara kyau shiyasa rashin auren baya damuna. Shekaran jiya matar Alhaji Yusuf ni da ita ta faɗa min ido cikin ido. Kaga na damu...? Ban damu ba saboda ni na san ba haka bane, suna yiwa abun kallon baibai ne, kuma babu wanda ya isa ya ce zamana da kai a gidan nan akwai haramci, sai dai su yi tunanin banza su daina. Aurena kuma lokaci ne kawai bai yi ba."

Bai yi magana ba kallon ta yake yana kuma hakaito kamannin matar da ta ambata a idanunsa yaji ta ce, "kowa tsoron zuwa ya ce zai aure ni yake yi saboda kai Omar, kaf ƙofar nasarawa da kewaye tsoronka suke ji iya kallon idanunka ma tsorota su yake yi balle ka yi musu magana. A haka ka ke cewa burin ka nayi aure?."

Ya sauke numfashi yana kallon ta kafin ya dafa kafaÉ—arta ya ce, "Didi lokaci ne kawai bai yi ba, in yayi zaki yi aure. Kawai bazan yarda ki auri É—an kutmar uba bane, dan ko kina auren nasa ya raina miki hankali ni mai iya ganin bayan sa ne."

Ta cire hannunsa daga kafaÉ—arta ta ce, "Omar ka daina furta wannan kalmar, ka daina cewa zaka ga bayan mutum don Allah ka daina."

Leɓensa ya ciza ya kalle ta ya ce, "Didi kamar uwa ki ke a wajena, in na kira ki da uwata ban yi laifi ba. Ina so ki sani babu wani ƙato ɗan ƙatuwa da ya isa ya ɗaga miki yatsa ban karya shi ba, kuma shi wannan da ya fita na ƙyale shi ne yanzu saboda ke amma ai zamu haɗu ko da sanayya ko da ganganci. Itama matar Yusuf ɗin zamu gauraya" yana faɗa ya juya ya shiga wata ƙofa da take farko  a cikin gidan.

Idanu ta wara waje jin abinda ya ce cikin É—aga murya ta ce, "Omar kar ka yiwa matar nan komai fa, matar aure ce kar ka sake ka yi wannan gangancin!." Bata ji maganar sa ba daman ta san bazai ce komai ba.

Waje ta samu ta zauna tayi tagumi hawaye na sakkowa daga idanunta. Tana matuƙar son ƙaninta Omar, tana matuƙar ji dashi bata so taga wani abun ya same shi. Amma Omar ya wuce tunanin mai tunani, duk yadda ka ke tunanin rashin jin Omar ya wuce haka. Baya ji tun yana yaro, baya bari in aka ɓata masa tun bai kai haka. Yana da zafi sosai, iya kallon idanun Omar zai saka ka firgice balle ka buɗe bakinsa ko ya yi maka barazana.

Kaf unguwar tsoron sa ake ji ko almajiri baya iya shigowa gidan yayi bara saboda dashi. Babu maƙociyar da take shigowa gidan saboda shi, baya ɗaukar raini kuma yason munafurci da gulma. Bashi da ɓoye-ɓoye kuma girman ka baya hana shi magana, shiyasa gidan kullum shiru sai Didi kawai ita kaɗai saboda kowa tsoron sa yake ji ba a iya zuwa. In kaga mutane a gidan to tabbas baƙi ne, shima haka zai ta cin magani yana zare musu idanu dan ya tsani ya ga anyi baƙo ko baƙuwa.

Hawaye taji yana share mata sai ta kalle shi bayan ya canja kaya zuwa ƙananun kaya ya tsuguna a gabanta ya ce, "duk wanda ya zama silar zubar hawayen ki sai na zama silar zubar jini a jikinsa, Didi kin san bana kisa, ban taɓa kashe rai ba. Amma akan hawayenki zan iya farke maƙworagon ko waye" ya faɗa yana wara idanunsa yana kallon ta.

Murmushi kawai tayi ta miƙe tsaye ta ce, "baza ka ci abinci ba?." Shima ya tashi tsaye yayi yana kallon ta ya ce, "Zamu zo anjima dasu goje mu ci, yanzu zan je na dawo."
"Ina zaka je?."
"Wani É—an aiki zan je nayi."
"Wanne aiki ne?." Ya kalli idanunta ya ɗauke kai  dan baya yi mata ƙarya kuma shi baya ɓoye mata komai na sa. Ya ce, "mutanen Yakasai ne suka ƙwacewa wani na mu waya sannan suka kashe shi, Ke kin san sai naje mun zauna dasu."

Ta girgiza kai tace, "don Allah Omar...." Ya dakatar da ita ta hanyar faɗim, "Didi sai na je fa, amma nayi miki alƙawari bazan yi faɗa ba indai ba sune suka so hakan ba. Magana kawai zamu je mu yi domin na ja musu kunne akuyar su ta kiyayi ramata."

Kallon sa take yi bata ce komai ba shima haka kafin ya ja baya ya ɗauke idanunsa daga kanta ya ce, "Zan dawo yanzu Didi." Yana faɗa ya fita cikin takunsa na ƙasaita ya bar ta a tsaye tana kallon sa.
Chapter 2 · 0% Book details