Sashe 32
Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Salma ta kalle ta tace, "Sai ina?." Ta kalli Salma ta ce, "Zan je gidan Mama Zaliha." Hajja ta kalle ta ce, "Sai kin dawo, amma dai kar ki yi dare." Nayla ta É—aga kai alamun to, Salma ta ce, "Amma da kin faÉ—a min da na raka ki."
"Na ji jiya kina cewa bakya jin daÉ—i shiyasa, ni kuma tun jiya ta kira ni ta ce nazo." Salma ta ce, "Da motar Hajja zaki je?."
Nayla ta ce, "A'a, napep zan hau." Hajja ta ce, "ke bana son shirme, kin san babanki baya son kina hawa abin hawa na haya ko? Meyasa baza ki bari a kira Sayyadi ya kai ki ba?." Nayla ta ce, "Hajja ai ba jima zan yi ba, yanzu zan dawo" ta faÉ—a tana fita da sauri dan kar Hajja ta hanata.
Nayla tana fita daga gidan kallon ƙofar gidan Didi ta ta yi gabanta ya faɗi sosai, a hankali ta fara takawa zuwa ƙofar gidan faɗuwar gabanta na tsannanta, wani irin yanayi baƙo a gare ta yana ratsa ilahirin jikinta. Ƙofar ɗakinsa a buɗe take tayi sallama ta shiga gidan amma shiru babu alamun motsi.
Tana gab da shiga falon ta ji an ce, "wace a nan!?." Da sauri ta jiyo suka haÉ—a ido, Sarai ya gane itace tun wucewarta ya ganta, yana sane ya ce wace a nan dan yarinyar ta soma zuwar masa wuya.
Nayla ta ce, "ni ce, ina yini." Bai amsa ba ya ce, "Haka ake shiga gidan mutane babu sallama?." Nayla ta sunkuyar da kai ta ce, "nayi sallama."
"Mtsww! To me ya kawo ki?."
"Wajan Didi na zo."
"Tattara ƙafafunki ki bar gidan nan Didi bata nan." Jin abinda ya ce sai ta ɗago ta ga shima ita yake kallo fuskarsa a ɗaure sosai. A hankali ta tako ta zo ta wuce shi ya bita da harara ya koma ciki.
Haushin Didin ita kanta yake ji tun safe ta wani fita gidan biki, bikin ma kuma wai gidan Kawu tsabar lalacewa. Ga Nayla da ta ke neman tunzura zuciya sa, ta dame shi da shige da fice a cikin gidan su. A bayyane ya ce, "wannan yarinyar akwai nacin tsiya."
Nayla ba ƙarmain daɗin ganinsa taji ba ta dinga sauke ajiyar zuciya tana tafiya fuskarta da murmushi, ji take kamar an yi mata babbar kyauta mai matuƙar daɗi kasancewar ta ganshi har sun yi magana. A haka ta hau napep ta tafi gidan Mama Zaliha dan kar ta koma Hajja ta fahimci wani abun da baza ta je ba.
Omar shiryawa ya yi cikin manyan kaya na yadi baƙi mai gajeran hannu kansa babu hula, gidan ya kulle da makulli sannan ya tafi wajan Narma da niyar kai ta inda ya ce zasu je.
Narma tun shigarsa tana tsaye a balcony tana kallon sa, wara idanu tayi tana kallon sa cikin shigar manyan kaya dan ya yi mata kyau sosai. Bata taɓa ganin sa da manyan kaya ba, duk da ƙananun kayan suna karɓar sa kamar jarumin india, amma kyaun da yayi a manyan kaya ƙarshe ne.
Gani tayi kamar kwanakin da ɗauka bata ganshi ba ya sake yin kyau ga wani class na musamman da ya ƙaro, duk da fuskarsa babu annuri amma ya yi mata kyau sosai. Gazebo ya shiga ya zauna akan kujerun da suke cikin ta. Yadda ya zauna ya ɗora ɗafa kan ɗaya yafi komai tafiya da ita, bata san tayi murmushi ba a bayyane ta ce, "Tiger!."
Sakkowa tayi daga saman ta fito harabar gidan tana kallon inda yake, samun kanta tayi da nufar wajan da yake cikin salon tafiyar ta ƴan gayu. Har ta isa bai sani ba sai tsayuwarta ya gani da ƙhamshin turarenta. Ɗago ido ya yi ya kalle ta, ta yi kwalliya cikin straight gown, ta kawo mayafi mai kauri amma mara girma ta saka, tayi ɗauri da ta ja shi baya gaban gashin ta ya fito sai hakan ya ƙara mata kyau sosai.
"Ina yini" ta furta tana kallon sa shi kuma tuni ya janye idanunsa dan ya kasa gane abinda yake ji in yana kallon ta musamman in itama kallon sa take yi. Miƙewa ya yi ba tare da ya amsa ba, a shagwaɓe ta ce, "na gaishe ka kayi min shiru, kuma saboda kirkin da ka yi min ya saka na gaishe ka." Lumshe ido ya yi ya buɗe jin yadda maganarta ta tatsa har cikin zuciyarsa, wani irin sanyi yake ji a jikinsa yanayinsa na canjawa.
Sake haɗa ido suka yi ya janye ido bai ce komai ba. Narma ta ce, "baza ka amsa gaisuwar ba?." Ɗan ƙaramin tsaki ya yi ya ce, "lafiya." Daga haka ya yi gaba ta bishi da kallo duk sai taji haushin kanta da ta yi abinda ya dizaga ta.
A hankali take takowa dan É—akyar take motsawa saboda yadda ta kamata rigar, daga wajan guiwarta an kama rigar sosai ta tsuke. Baya ta juya tana yiwa mai gadi magana a nan ya hango doguwar tsagar bayan rigar wacce ta bayyana farara digadiginta, har abinda ya rab digaginta da cinyarta a bayyane yake. ÆŠauke kai ya yi daga kanta yaja dogon tsaki ba tare da ya san dalili ba, ta buÉ—e motar ta shiga shi kuma ya ja motar suka fita.
Babu wanda yake magana a cikin su kamar ko yaushe, shi titi yake ita kuma danna waya amma lokaci zuwa lokaci tana É—agowa ta kalle shi sai ta cigaba da abinda take yi. Shopping complex suka shiga kamar yadda ta ce, ya tsaya a harabar store É—in ta buÉ—e ta fita bata ce masa komai ba.
Fitowa ya yi shima ya shiga dan akwai abinda yake so ya siya. Bata san ya shigo ba sai ganin sa tayi a ɓangaren turare ya ɗauki ɗaya na maza sannan ya ɗauki ɗaya na mata. Ƙarasowa wajan tayi ta kalle shi shima ya kalle ta amma bai ce mata komai kafin kuma tayi magana ya wuce. Wajan kayan shayi ya je ya ɗauki coffee sannnan ya ɗaukarwa Didi milo dan ya san ta akwai son Milo, haka kawai ma sha take yi.
Kafin Narma ta gama shi ya biya kuɗi ya koma mota ya zauna yana duba turaren da ya siya. Ba jimawa sai gata nan ta fito bayan ta da mai riƙe da ledar da ta yi siyayya. Yana daga zaune buɗe baya aka saka mata sannan ta shiga motar suka tafi. Jira yake yaji ta ce ga inda zasu je yaji tayi shiru shi kuma bazai tambaya ba.
Ta wani ƙaramin cafe suka zo wucewa Narma ta ce, "ɗan tsaya a nan zan siyi donut." Faka motar yayi ta shiga ciki bata jima sosai ba ta dawo ta shiga motar. Wani almajiri ne yazo wucewa yana bara Omar ya sauke glass ya miƙa masa kuɗi shi kuma yana addu'a, Omar ya ɗaga glass ɗin bai ko kalle ya ba. Donut ɗin ta buɗe sai ta kalle shi ta ce, "Ga donut" ta faɗa tana miƙa masa ledar. Kai ya girgiza mata kawai ya ja motar suka tafi.
Wayarsa ce tayi ƙara ya kalla yaga Goje ne yake masa waya sai ya ɗauka ya saka a kunne Goje ya ce, "Damisa babbar Yaya ce babu lafiya, yanzu ta dawo daga unguwa."
"Subahanallah! Me ya same ta?" Ya tambaya a gigice. Goje ya ce, "Bamu sani ba, kawai mun ga saukarta daga napep tana jiri kamar zata faÉ—i."
"Gani nan" ya faɗq yana yanke wayar tare da ƙara speed ɗin motar.
Kallon sa Narma take tana mamakin Wacece babu lafiya haka ya damu?. Sannan mamakin kanta take yi wai ita Narma itace driver yake amsa mata waya a mota bata É—auki mataki ba, ita kanta ta san ta canja.
Gani tayi sun wuce hanyar su ta kalle shi ta ce, "gida fa zan je." Ai ko kula ta ma bai yi ba sai da ya ganshi a ƙofar gidan su ya fita a gigice ya shiga gidan. A kwance ya samu Didi kana ganin ta ka san bata da lafiya, ya tallafo ta jikinsa ya ce, "Sannu Didi, tashi mu je asibiti." Ta kalle shi ta ce, "A'a Omar, ba sai naje ba."
"Wallahi sai kin je, ki tashi mu je ko na ɗauke ki wallahi." Jin abinda ya ce sai tayi murmushi ta miƙe ya riƙe hannunta suka fito, gidan ma a buɗe ya barshi saboda su Bash suna nan.
Motar da taga ya buɗe mata gaba ne ya bata mamaki, duk da tana cikin ciwo bayan ya shigo sai sa ta ce, "Omar motar waye wannan?." Narma da take baya ta maimaita Omar a zuciyarta tana cewa, _Dama sunan sa Omar? Suna mai daɗi. Shiyasa yake da fushi mana da yawa masu suna Omar haka suke._ bai bata Didi amsa ba ya ja motar ta ce, "wai yaushe ma ka iya mota Omar?."
Kallon ta ya yi ya ce, "Don Allah ki yi shiru baki da lafiya" ya faɗa yana taɓa goshinta yaji zafi sosai. Narma da take baya ta ce, "Sannu, ya jiki?."
Didi kanta ciwo yake É—akyarta iya waiwayowa bata ma iya gane wacece sosai ba, ta É—aga kai kawai daga nan tayi shiru. Narma dai mamaki take yi ko wacece wannan? Ya ruÉ—e tunda aka ce bata da lafiya, gata kuma har yana haÉ—a ta da Allah akan tayi shiru cikin rarrashi, lallai ko wacece tana da mahimmaci a gare shi.
Asibitin da suka je aka yiwa Narma dressing nan suka je ya fito da kansa ya riƙe Didi suka shiga asibitin. Narma ganin yadda jikin Didi yake rawa sai ta bata tausayi sosai daman ita akwai tausayin mara lafiya hakan ya saka ta fito itama ta bi bayan su. Kwantar da Didi aka yi akan gado aka yi mata allura kafin a ɗauki jininta a gwada a dawo a fara yi mata treatment ɗin malaria.